Da sallamar sa cikin natsuwa yadda ya saba babu tashin hankali a tattare da shi sai zallan wahala da yasha, kai tsaye randar ruwan gidan ya nufa ya buɗe ya kurɓa bayan ya kuskure bakin sa sannan kuma ya sha har sai da yayi rabin kofin ya ajiye yana mai kallon Mahiafiyar tasa cikin tausayi da jajircewa amatsayin ta na uwa...kai tsaye ya nufi in da take ya durkusa har kasa ya gai da ta.

"Umma sannu da aiki"

"Yawwa *Aiman* ya ya dai an dace kuwa??

Uhhmmmm Aiman ya ja dogon ajiyar zuciyaa a dai dai lokacin da yake faman kwashe robobin da Umman nasa ta zuba tuwo, gefe ɗaga kuma yana gaishe da kakar tasa ta wajan uba....sai da ta harare sa sannan ta ce,"Mai irin halin uwar sa, ka ci sa a ka zo amatsayin jika na wallahi da sai na maka rashin mutunci"

Dariya Aiman yayi, a ranshi ya ce Ita dai Inna ko da yaushe an mata laifi bata rabo da faɗa, ko duk tsufan ne yake neman susuta ta, ya washe baki alamar kalmar daya faɗa a cikin zuciya ta bashi dariya, ya dawo wajan Umma ya ce,"Inaaa Umma wallahi ba'a dace ba, amma ga wasu ƴan kuɗi nan nayi ƴar buga buga na samo mana dubu biyu.....ya tura hannu cikin tsohon jeans ɗin sa ya ciro ɗari biyar biyar guda huɗu yana mai mika mata, babu zato babu tsammani Inna tayi wuff ta warce ɗayi biyar tana niyan kwace saurin yayi saurin ɓoyewa yana cewa,"Kutttt granny yoo ai na manta kina kusa na ciro zunzurutun kuɗi, wallahi wannan babu kason ki a ciki to amma tun da kin kwace ɗaya to kije na baki"

Ta galla masa harara, tayi gaba tana cewa,"Halin ku ɗaya, sai kuyi ta kus kus kuna munafurci, ni dai gobe ayi mana abin karin ƴan gayu eheeeee"

Aiman yayi dariya ya mikawa Umma sauran kuɗin yana cewa, "To Umma gare ki, fatan kinji sakon ƴad tsohuwa ni dai babu ruwa na" ya karasa da karfi yana shigewa ɗakin sa ya rufe kofa ruf don ya san, Inna tsaf zata iya biyo shi suyi tayi babu ruwan ta.

Inna irin jarababbun nan ne wanda ko baka tsokane su ba sai sun zazzaga maka buhun masifa, tana da faɗa, tana da mita, amma kuma tana da daɗin zama idan ka fahimci halayen ta ka kuma iya zama da ita to zakaci ribar rayuwa.

TURKIYYA
Istiklal
8pm

Misalin karfe tara na dare Ammi ta kwanta, mai aikin mu ma ta kwanta, yayin da nima ina ɗaki na waje yayi tsit tamkar babu halitta mai rai a wannan faɗin gidan, kunsan rayuwar ƙasar waje basu da tsoro ko wani abu, Ina kwance a saman benen dake ɗaki na, waje ne da aka kawata shi da furanni masu ban sha'awa da ɗaukar hankali, an gina wajan ne ta ɗaki na wato ainahin filin shakwatawa, ina kwance saman wani lallausan kujerar lilo mai taushi da daɗi, ina kallon sararin samaniya na kura ma tauraro da wata idanu abin yana bani sha'awa ......na kan jini a wata duniyar ta daban. So da dama ina tambayar kai na da Ammi, "Ammi baki taɓa zuwa Nigeria ba, kuma bakya matsawa Daɗɗy akan zaki je?

Sai Ammi tayi kayataccaen murmushi ta bani amsar da kullin ita ce amsar da take bani sai ta ce,

"Idan da rai wata rana zamu je In Sha Allah"

Murmushi kawai nayi ina daɗa kwaɗaituwa da ganin na taka ƙasar mahaifi na....to amma menene abin farin ciki, ko in ce mene ne abin zakwaɗi, ko ince what so special about going to *NIGERIAN*, ina yawan browsing ɗin country ɗin yanayin su da kabilunsu yana burge ni, uwa uba AL'ADA, babu abin da yafi burge ni da su sai al'adun su suna da yare daban daban wanda daga ciki nafi binchiken yaren HAUSA, Saboda shine yare na, dole kuma da shi zan yi tunkaho.

Ina wannan tunanin har bacci barawo ya sace ni.

The next day

Karar alarm shi ya tashe ni daga nannauyen baccin da na keyi karfe biyar da rabi 5:30am na tashi nayi mika kafin nayi brush al'ada tace yon brush kafin komai da safe, sannan na gabatar da sallah, na zauna na buɗe alkur'ani na karanta suratul ali-imran na rufe na tashi na sauya kayan jiki na izuwa gym wears/ kayan motsa jiki na fita zuwa gym/ɗakin motsa jiki dake gefe cikin apartment ɗin ɗaki na, babban ɗakin motsa jiki ne mai ɗauke da machines daban daban duk wanda rai na yake so hawa na keyi nayi duk abin da na ke so saboda mallaki na ne, Abhi ya siyo min.

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now