Ya mik'e da little a hannunsa ya fice. Ta San haushi ya ji don haka ba b'ata lokaci ta janyo mayafinta Hd Veils mai tsadar gaske ta fesheshi da turarenta banda k'amshin gabbasse da yake yi ta fice da sauri bayan ta 'dau jakar Little. Zata ga yau da wani ido Family za su ganta idan sun ganta da baby, tunda har a lokacin Hisham bai sanar da kowa haihuwar ba.

Har suka je asibitin bai kulata ba yana tuk'insa cikin nutsuwa yana sauraran cool music.

Yana tafe tana binsa a baya suka k'arasa 'dakin da aka kwantar da Daddyn. Ya tura k'ofar inda mutanen wajen suka 'd'ago gaba d'aya idanunsu a kansu musamman Sauda musamman yarda suka ga ta yi kyau sai shek'i take ga shi ta cika taf ta ko ina sai zuba k'amshi take kana ganinta dai ka San Naira ta zauna.

Inna Falmata da ta kasa shiru bayan Sauda ta gaishesu ta watso mata tambaya "Kin yi aure Har kin haihu ne ba labari?"  

"D'ana ne." Hisham ya yi furucin da yasa kowa 'dagowa yana kallonsa musamman Mommynsa da ta ji maganar kamar dirar aradu. Fuskarsa a gintse Ya ce "Dama ban rabu da matata ba muna tare, yau kwananta uku da haihuwa." Ya fa'dawa yana mik'awa Umma Falmata Babyn "Little Sa'ad kenan, ga shi ki saka masa albarka." Hannu biyu ta saka ta amshi 'dan don bata da k'warin gwiwar furta ko da kalmar 'A'  haka ya dinga zagaye da 'd'an Sauda tana zaune tana mamakin yarda suke ta wage baki suna furta "Ma sha Allah, ai lamarin Ubangiji ya wuce nan Allah ya yi albarka." Hatta da. Daddynsa sai da Hisham ya kai masa yaron  ya 'daga hannunsa da k'yar ya shafa kan yaron.


********

Ranar Suna, duk da ba su sanar da taron sunan ba Sun ce ba suna Amma haka gidan ya cika da jama'a y'an zuwa ganin k'waf. Duk inda aka ga Umma sai ki ga Har 'dan rusunawa ake ana gaisheta. Dole Hisham Ya bada orderr abinci aka kawo gidan aka ci aka sha kowa ya watse ana fa'dar son barka da girmama lamarin ubangiji tabbas Hukumullahu la ajabun. Umma ta dinga mamakin jama'a ganin yarda ake dandazon zuwa gidan da Dane ko taron take bai zama lallai ta ga wani ba. Amma wannan karan Har gudumawa suka dinga bata sai dai juyin duniya Umma ta k'i amsar ku'din an don sun san ba don Allah suka ba su ba, me yasa ba su ba su a lokacin da ba su da shi ba?

Har gida Abba Mustafa da Khalil da Sa'eed suka je suka taho da Baffan wudil don ya zo ya ga gida ya saka albarka.

Tun daga harabar gidan Baffan wudil yake jaddada hukumullahu la ajabun. Mustafa ka ga lamarin Ubangiji ko? Ka ga abinda Rabbi ya maka ko? Shi yasa ake son kullum bawa ya zama mai zuciya mai kyau wacce bata nufar kowa da sharri sai ka ga Allah yana ta 'daga darajarsa. Zuciyarka mai kyau ce Mustafa don haka ba zaka tab'e ba."

Aka cika masa gabansa da abinci iriiri da abubuwan sha na gargajiya da Umman Sauda ta zauna ta ha'da masa. Sai da ya gama ci Ya nutsu sannan ya musu addu'a suka Shafa aka kuma cigaba da hira.

Bayan Fareeda ta gama idda aka ha'da aurenta da Mahmud Babu Wanda Ya san dalili daga iyayenta sai na Hisham 'din sun bar shi sirri a tsakaninsu. Alhaji Hamza bai zafafa ba don yanzu ya saduda da duniya duniya tsoro take ba shi musamman ganin yarda Allah ya mayar da shi a zaune b'arin jiki baya aiki don ma Sule Hakimi ya yi alk'awarin tallafa masa zai kuma mayar masa da wasu kadarorin da ya rasa.

___________

Bayan Shekara Goma.

Ta fito tsaf da ita cikin rigar likitoci shirinta na fita aikin asibitinta burinta ya cika na zama cikakkiyar likitar mata Saudat kenan, kana ganinta kaga wacce hutu ya zaunawa. Ta zama matashiya y'ar shekara talatin cif

Hisham zaune da y'ay'an sa sun baibayeshi su biyar cif Little, sai Maryam da ake kira Afeefa, da Mustafa Da ake kira Afeef sai Hamza Daddy da Amani mai sunan Mommy Laraba. Ta zauna daf da shi ha'de da fa'din "Wash Daddee wallahi aikin nan is not easy banda ina son taimakon jama'a da na ajiyeshi."

Ya tab'e baki, "Wa ya saka ki? Tun 'd'azu ma ke muke jira zuwa Family Meeting Abba Mustafa ma Ya yi kiranki baki dawo ba." Da sauri ta mik'e ta shige ciki da sauri don ta watsa ruwa shaf ta manta yau ne meeting 'din da suka Saba duk k'arshen wata.

A k'ofar gidan suka tarar da jama'a da yawa masu neman taimako yawanci y'an uwa ne da suke cikin matsala shi kuma Abba Mustafan sai ya saka su taimaka musu da abinda ya sawwak'a.

Hakanan duk azimi sai ya saka sun raba kayan abinci da ku'din zakka ga mabuk'ata da danginsu tabbas arzikinsu na kowa da kowa ne ba za k'yashin taimako ko ka'dan Sun horu da koyarwar Babansu shi yasa a koda yaushe danginsu suke alfahari da su. Har Alhaji Hamza ba su bar shi ba duk wata sai an kai kayan abinci gidansa sannan yana yawan zuwa masa hira akai akai don ya 'd'auke masa kewar rashin tafiya da baya yi.

Arziki kam kullum k'ara hab'aka yake ya zama duk gari babu wanda idan ka ce Alhaji Mustafa Maishadda zai ce bai San shi ba, saboda taimakonsa Har gidauniyar tallafawa marayu y'a Gina mai suna Maishadda foundation. Tabbas Baffan Wudil bai yi k'arya ba da Ya ce Hukumullahi La ajabun.

Allah yasa mu dace Ya bamu ikon aikata komai don Allah ba don a mayar mana ba ko don riya. Allah ka rabamu da aikta zumuncin zamani zumuncin ban gishiri in baka manda.

Ku yi amfani da alherin da yake cikin littafin sharrin kuma ku watsar da shi.

Nagode sosai masoyana Wa ana Uhibbikum Billah.

Mu ha'du a sabon littafina Takaicin Uba... akan Naira 'dari biyar kacal kada ku bari a baku labari Takaicin Uba.... Yazo da sabon salo mai saka takaici da tsayawa a rai... ku biyoni mu tafi garin su Ayra Gaya.

(Amfani da wannan littafin ba tare da sanin marubuciyar ba ta kowanne fanni laifi ne!)

Jikar Nashe ce!

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now