Ta waro ido cikin kishi tana kallonsa kafin ta ja hannunsa ta kai masa cizo ta sake da sauri tana nufar bed room sai dai kafin ka ce Me? Ya cim
Mata Ya 'dagata cak ita da cikin da ke jikinta suka shige 'daki. Sauda kin jawowa kan ki....

________________

Ranar kwana tara su Abba Mustafa tsaf suka shirya kayansu don komawa sabon gidan. Gidan da ya zama mallakinsu ba na haya ba kamar yarda suka 'dau tsawon shekaru suna yawon haya. Hakan yasa suka dinga murna da farin ciki sai dai zuciyarsu fal take da alhinin rashin Sa'ad da bai 'dand'ana wannan da'din ba Amma suna fata Ya samu gidan kerewa sa'a a aljannar firdausi.

Sun gayawa y'an uwansu na kusa da suka San za su taya su murna dangin Umma na kusa da y'an uwa da abokan arziki.

"Masha Allah!" Haka zaka ji duk Wanda ya shiga gidan yana furtawa. Gidan da girmansa don daga a waje akwai filin da Umma har ta fara tunanin fara Kiwon kaji. Babban falo sai manyan 'dakuna guda biyu dag
Cikin falon da kitchen da toilet a kowane 'daki sai k'arami a falon. Daga harabar waje kuwa akwai 'dakuna madaidaita guda biyu.

"Maryama haihuwa ta yi rana, tabbas mahak'urci mawadaci." D'aya daga cikin yayyenta ta fa'da tana ranga'da gu'da. Haka kowa ta dinga tofa albarkacin bakinsa. Aka yi addu'oi aka yi saukar al'kur'ani sannan aka ci tuwon shinkafa da wainar da Umma ta yi mai miyar taushe sai tantak'washi da lemon zob'o.
Haka mutane suka watse suna ta mata son barka dafatan alheri."Allah ya tsone idon mak'iya Maryama, kin ga nan ya isheki ki kafa babban keji ki dasa kiwon kajinki wallahi." K'anwar Babarta ta fa'da yayin da Maryama ta raka su. Tana murmushi ta ce "Wallahi abinda yazo raina kenan Inna In sha Allah haka za'a yi." "To Masha Allah, ubangiji Ya dafa ai akwai albarka a cikin kiwo sosai kuwa in dai ya karb'i mutum."

Bayan tafiyarsu Umma ta fito cikin farin ciki ta sake gyare gidan tas ta yi mopping ta baza turaren wuta. Ta bu'de k'aramin 'dakin da yake cikin kitchen abin mamaki cike yake taf da kayan abinci ga kitchen 'dauke da gas da 'd'an fridge madaidaici kowane 'daki kuma da gadonsu gida dai sai son barka ko amarya sai haka. Umma bata San sanda ta saki hawayen farin ciki ba fa'di take "Alhamdulillah Allah mun gode maka, ya wajaba a kaina na yi kwanan Sallah yau na nuna godiya ta a gareka, wa zai maka wannan banda sarkin sarakuna?" Ta fa'da tana 'dauke k'wallar da ta cika kwarmin idanunta "Tabbas Mahak'urci Mawadaci.."

Girki ta 'dora musu a gas 'din tana mamakin yau itace da kunna gas don ma ta Saba da shi a sanda Abban Sauda yake da arziki da bata San yarda zata kunnna shi ba. Shikkenan yau ta huta da wutar itace da gawayi.

Shinkafa ta yi musu da soyayyiyar miyar kaji, yaushe rabonsu da soyayyiyar miya kullum Mara mai sosai suke yi. Ta yanka kabeji ta ha'da musu cole slow tana wannan shine abincin da Sa'adunta Ya fi so ga da'din yazo ga Sa'adu baya raye sai dai fatan Allah yasa y'a ci mafiyinsa a aljanna.

______________

Sanye da doguwar riga ja da aka mata adon ba'ki. Ta yi rolling da mayafin rigar, ta k'ara haske sosai kyanta ya sake bayyana tamkar ba'indiya. Fareeda ce ta zubawa Mahmud ido fuskarta a caku'de kamar za ta yi kuka, lamarin ya gigita tunaninta abinda ba ta tab'a zata ba ba ta yi tsammani ba, duk da tana son Mahmud a wannan tana jin kamar tana dana sanin mu'amalantar sa, tur da halinta tur da son zuciya irin nata ina zata kai wannan abin kunyar? Da wani ido zata kalli jama'a tana 'dauke da cikin k'anin mijinta? Wace fassara jama'a za su yi mata? Fasik'a ma ci amana!

Tuni hawaye y'a gauraye idanunta cikin firgita take fa'din "Kaico na ni Fareeda, ciki a jikina ba na miji na ba, na k'aninsa?"

Don ta San ko giyar wake ta sha bata isa ta doshi Hisham da cikin nan ba, mutumin da rabonta da shi tsawon wata uku ga cikin wata biyu a jikinta? Mutumin da bai tab'a ma kusantarta ba....

Shi kansa Mahmud na sa hankalin ya fi na Fareeda tashi, sai yanzu ya ankara da wautar da suka aikata, da kuwa idonsa ya rufe da tarin soyayyarta. Zuciya a jagule yake share mata hawaye.

"Relax Fareeda, abinda ya faru ya Riga ya faru mu samu mafita kawai. Mafitar kuwa itace shek'ar da wannan cikin da yake jikinki." Cikin amincewa da shawararsa ta shiga share hawaye duk da tana tsoron abortion ta San yana jawo matsaloli da dama. Ya ja hannunta yana matsawa "Ko ke fa? Ba ki San yarda nake ji ba idan kina kuka."

Ya tada motar suka nufi gida da zummar a goben za su samu mafita. "How I wish da aurena kika samu cikin nan da yaron nan ya sha tattali da kulawa da an ga 'd'an Soyayya musamman idan macece ta biyo kyawun ki.." Murmushi kawai take ita kanta zata so hakan zata so ta mallaki Mahmud matsayin mijinta amma ya zata yi da auren Hisham da yake kanta?

__________

Umma Falmata ta shiga gidan su Hisham da sallama ita da masu mata hidima, Hajiya Laraba da fara'a ta tareta tana fa'din maraba lale da Uwar alkhairi.

Umma Falmata ta zauna tana mayar da numfashi sama sama dalilin k'iba da take da ita. Ko ta ta yi tafiya ta dinga haki kenan.

"Daga gidan Mustafa nake, naje gaisuwa dalilin sanda aka yi rasuwar ban samu na lek'a ba ina fama da ciwon Kai."

"Ayya haka aka yi, ai kuwa ban ganki ba duk da nima shiga na yi fito saboda ba wajen zama a gidan Kai talauci ya samu mahalli a gidan Mustafa, Allah ka raba mu da talauci Masifa!"

Falmata ta tab'e baki "Ai tun kai kaya naga haka Allah dai ya mana jagora, daga waje na tsaya ake sanar da ni Sun tashi wai 'd'an su Khalilu ya siya musu gida a rijiyar zaki. To har zamu wuce na ce da Bala driver Ya tsaya a gaisa na tambayeki Hisham don na rabo na da shi tun gabannin zai yi hatsari."

Cike da takaici Mommy Laraba ta tab'e baki "Bar ni da kayan takaici, ai Hisham tunda muka sa ya rabu da matarsa yake Fushi da mu ya ma sa k'afa Ya bar k'asar, Fareedan ma anan ya barta. Falmata ta hangame baki "Ku kuma ku saka idanu kuka k'yaleshi Mustafa da Matarsa Sun gama mallake muku 'da ba zaku mik'e tsaye a kansa ba ku saka a musu farrak'u ya ji ya tsani kaf ahalin Mustafan" Mommy Laraba ta ce "Ke ma kya fa'da na gayawa Alhaji ya ce na jira akwai lokaci..."

"Ai kuwa laraba ba kiga ta zama maza mik'e mu je ki raka ni na yi gaisuwar nan daga can mu dangana da gidan Malamina aikinsa kamar yankan wuk'a yake. Tsanarsu zai yi sosai kamar annabi da kafiri."
Cikin fara'a Mommy Laraba ta mik'e tana fa'din "Yanzu na ji batu na san lamarinki ba wasa Hajiyata..."


Akwai yiwuwar samun posting sau biyu a rana idan naga ruwan comments 😀

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now