Umma a kasalance ta bi bango ta zauna turus tana zabga "Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna mugun ji mugun gani Ubangiji ka kare mu."

Ya bu'de takardar kamar haka:

Assalamu Alaikum Abba na..

A min afuwa na San na aikata babban kuskure Amma zuciyata ce ta kasa aminta da cika maka umarninka. Da gaske Abba ba zan iya ba shi yasa na 'dauki Sauda na tafi da ita duk da itama ba da son ranta bane wallahi Abba tilasta mata na yi. Don Allah kada ka ce komai ka saka mana albarka."

Hisham Mai shadda.

Tun kafin ya gama karantawar Ya dinga sakin murmushi yana mamakin kafaffiyar Soyayya irinta Hisham da Sauda. Murya a dashe Ya ce "Ba zan ce komai ba Hisham Allah Ya yi muku albarka ya kawar da dukkan abin k'i a auren nan, ba zan sake jayayya da hukuncin Allah ba, ban san me ya b'oye ba."

Ya mik'awa Umma Maryam takardar. Ita 'din ma karantawar ta yi tana sakin murmushi ta kalli Abban Sauda da har yanzu baya sakar mata fuska "Abban Sauda don Allah ka yi hak'uri ka yafe min wallahi sharrin zuciya ne da na shai'dan su kuma Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a 'dayyiba."

Sosai ya ji da'din hak'urin da ta ba shi, shi da kansa ya amince da cewa sharrin shai'dan ne ba halin Maryamansa bane. Yana kallonta Ya saki murmushi ya ce "Bakomai ya wuce, ga shi nan dai yara sun yi maganin mu sun gudu Sun bar mu, ai shikkenan Allah ya musu albarka. Ja'irin yaro da Ya fa'di inda suke ai kinga sai na aika musu da kayanta to ya b'oye inda suke don kada a bi su a k'watota, bai San ni tun bayan da Ya samu hatsari ba na janye kaina daga batun auren su kada aje a rasa rai garin jayayya."

Umma tana murmushi ta ce "Ko bakomai ai Ya yi maganin mu." Sa'ad ma da yake gefe dariyar yake Hisham kuma ba k'aramin burgeshi Ya yi ba.

         FAREEDAH FA?

Hisham yana fita ta koma turus ta zauna, ta dinga tunani da k'ok'arin gano ma'anar da yake nufi na ta jira lokaci, sai dai Sam k'wak'walwarta ta kasa bata amsa. Ta saki tsaki "Kai ka sani."

Ta mik'e tana shiga cikin 'd'akinsa don tattarewa. Anan ta ci karo da sak'on takardar da ya bar mata. Cikin mamaki take karanta takardar

"Tafiya ta sameni, zan iya 'daukan wata guda ba ki ji 'duriyata ba ko sama da haka. Duk abinda ki ke buk'ata ki sanar da Mahmud zai Maye Miki gurbina.
Fatan alheri.

Har tsalle ta yi bayan gama karanta takardar, ta sake samun damar kasancewa da Mahmud 'dinta babu shamaki."

AN SHA AMARCI.....

A tsaye a gaban gadon da towel a hannunsa da comb. Yana yarda mata ruwan da ya jik'a gashin kansa da shi. Idanunta a runtse tsam ta k'i ta bu'desu. Matsananciyar kunyarsa ce take dabdala a zuciyarta Tabbas al'amarin mai girma ne! Duk da ba shine first Night 'dinsu ba, amma shi ma wani dare na da ba za su manta da shi ba a tarihin rayuwarsu. Da wani ido za ta kalleshi bayan yarda ta cire kunyarta ta nuna masa itama yanzu y'ar hannu ce. Ta shagaltar da shi ta 'dimautar da shi Har ya dinga furta mata wasu kalamai masu zafi da ba zata tab'a manta su ba.

Ya sunkuya yana jan Karen hancinta kafin Ya kai masa sunbata da tsotsa mai zafi ya ce "Ba zaki bu'de idonki ba? Ko so kike na dawo.."

Da sauri ta mik'e tana k'ok'arin jan bed sheets don suturta jikinta. Amma Har a lokacin idanunta a kulle suke gam. Ya dinga binta da kallo yana jin sake ninkuwar sonta  a zuciyarta tabbas ya yarda Allah Ya halicci Sauda saboda shi ne, ita maha'din rayuwarsa ce.

"Ki tashi na ce ko na sunkuceki na sadaki da toilet, kada ki ce za ki nuna min sangartar mutanen novel mana ni ba mijin novel bane. Bayan ke kika yaudareni ko abinci baki bari mun ci ba ki ka ribace ni sai da na........"

Da sauri ta Ware idanunta tana kallonsa kafin ta wulla masa k'aramin fillown da yake hannunta "Ba fa kyau k'arya babba da kai..."
Ta furta cikin muryar shagwab'a. Muryar da ta sake gigita shi don dai yana jin yunwa ne, burinsa dama kenan auren macen da zata dinga masa shagwab'a.
Ya tsaya yana k'arewa bakinta kallo da yake 'dan motsi. Ganin tana shirin wahalar da shi cak Ya 'd'auketa zuwa toilet 'din don dole ta mayar da shi MIJIN NOVEL..... wanka lafiya Sauda.

A hankali take takunta, cikin salon da k'warewa na macen da ta san kanta mai son mallakar mijinta. K'afafunta sanye suke da jajayen silifas masu taushin gaske maha'din rigar da take jikinta ta companyn Ck.

Idanunsu su ka gamu cikin na juna Hisham duk da yarda yake jin yunwa tuni ta tafi da duk imaninsa. Da gaske Sauda shirin hallaka shi take. Ya mik'a mata hannu alamar ta zo cinyarsa. Sauda ta nok'e kafa'da ha'de da turo bakinta da gaske Fushi take da shi. Fushin marin da Ya mata a hanyarsu ta tahowa so take lallai sai ya bata hak'uri. Ta zauna a kujera nesa da shi ka'dan tana watso masa dara-daran idonta. Ya sake mik'a mata hannu ta sake nok'ewa. Hakan ya saka shi mik'ewa ya isa kitchen don tattaro musu abincin da Chef Aliyu ya girka.

Har ya gama jera abincin Sauda bata mik'e daga wajen balle ta isa saman daddumar da yake jera musu abincin. Ya isa gabanta yana shiga jikinta sosai ta 'd'an tureshi "Ni ka daina shiga jikina bayan ba so na kake ba."

Ya ware ido yana murumushi "Ta shi mu je mu ci abinci,
Zaki samu amsar ina son ki ko bana son ki anjima ka'dan." 

"Kana so na ka mareni? Ko tausayina baka ji ba."

Can ya tsaya yana murza goshinsa shi kansa sai yanzu yake jin takaicin marin da ya mata. Mik'ar da ita ya yi tsaye yana ha'data da jikinsa cikin wani salo a hankali a kunnenta ya fara ra'da mata "Am sorry Sweety na, bana iya controlling zuciyata ne, a duk lokacin da kika furta waccan bak'ar kalmar ki yi hak'uri kin ji Sweetheart. Kin hak'ura?"

Ta 'daga kanta tana murmushi ka'dan "Yauwa ko ke fa, ba ki San yanzu da farin cikinki, nake samun nawa farin cikin ba?" Ya jata zuwa Dinning yana jin tamakr ya mayar da ita cikinsa su zama abu guda. So Gamon Jini ne Tabbas!

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now