Yanayin fuskarsa Ya tabbatar
Mata da zai iya aikata fin hakan ma, shi yasa ta bi bayansa zungwui-zungwui, har taso ba shi dariya sai dai ya gintse dariyarsa tsaf a cikinsa."

Gaban motar Ya shigar da ita, shima ya zagaya b'angaren Driver ya shiga motar.

Yana shirin tayar da motar Sauda ta yi saurin rik'o hannunsa, hakan ya saka shi juyowa.

Girgiza masa kai ta hau yi idonta fal hawaye.

"Please! Idan magana ce mu yita anan ba zan bika ko ina ba."

Bai bi ta kanta ba ya janye hannunta ya sake gintse annunrin fuskarsa. Ya bawa motar mugun Speed, har hakan ya ka'da hanjin cikin Sauda sai dai ta kasa ce masa ko 'a' saboda ta tsorata k'warai da yanayinsa. Ta runtse idanunta kawai tana duk addu'ar da ta samu ta shiga bakinta.

Nisan tafiya ya yi sosai sannan ya rage gudun. A lokacin ne Sauda ta samu ta bu'de idanunta tana kallon hanya sosai da mamaki ta ke kallonsa ganin suna shirin barin gari.

"Ina za mu Yaya Hisham?"

Sai da ta furta ya kai sau uku sannan  cikin dakakkiyar murya ya ce "Gidan Mijinki zan kai ki."

Da sauri ta rik'o hannunsa

"Please Yaya Hisham kada mu yi haka da kai, so kake su Abba su tsine min? Na riga na musu alk'awarin ba zan sake kulaka ba." "Babu bi ga abin halitta cikin sab'awa mahalicci, duk duniya a yanzu ba Wanda ya cancanci ki masa biyayya sama da ni, don haka kada ki sake min magana. Na gaji da walagigi da rayuwata da ake yi dole na bi duk wata hanya da zan samu rayuwa da ke Har abada. Ba zan iya rabuwa da ke na sha kwatanta hakan na kasa Ya kike son na yi Sauda? Banda na gudu da ke na bar musu garin...."

"Ni kuma Yaya Hisham dole ka rabu da ni, don a dalilinka ba zan sab'awa iyaye na ba Allah sai ka sakeni ba inda zan bi ka."

Bai san sanda ya saka hannu Ya zuba mata Mari ba cikin tsananin b'acin rai don ya tsani kalmar sakin da take fitowa daga bakinta.

Ta dinga kallonsa cikin mamaki tana zubar da hawaye murya a sark'e ta ce "Ni ka Mara?"

"Ka'dan na Miki matuk'ar zaki cigaba da furta waccan bak'ar kalmar ba zan juri jin ta ba, ke kuma na ga kin mayar da ita lazim idan muna tare. Idan kika cika min ciki wallahi zan ganar da ke kuskurenki zan kawar da duk wata soyayya da nake miki in maganin bakin tsiwarki haba don kin ga ina son ki shine za ki dinga min wulak'ancinku irin na 'yaya mata?"

Shashshek'ar kuka kawai take, don ta tsorata da lamarinsa gani take kamar ba Hisham bane kamar an canja mata shi ko kuma Ya sha wani abin gwara ta kama kanta kada ya aikata mata fin haka a dajin Allah inda ba mai taimakonta.

K'arfe biyar daidai suka shiga cikin garin Abuja. Kai tsaye gidansa da yake Maitama Sule ya zarce da su zuwa lokacin Sauda ta galabaita da yunwa ga shi ta firgita da shi don haka ko magana ba ta yi illa barci da ta dinga yi tana farkawa. Fushi ne ta hanata cin take away 'din da ya kawo mata da ruwa da lemon duka ko kallonsu bata yi ba.

Yana sakin horn mai gadin da Ya kasance Soja ne Ya yi saurin isowa ta wangale masa gate, yana gaisheshi wannan karan ba kamar yarda ya saba ba murya a cunkushe Ya amsawa mai gadin 'dan K'abilar Yarbawa. Ya k'arasa a gajiye lik'is ya yi parking a harabar ajiyar motoci.

Duka masu aikin suka k'araso zatonsu shi ka'dai ne, suna mamakin yarda ya k'i amsa gaisuwarsu. Kaf 'din su Ya kalla ya sauke glass ha'de da amsa gaisuwarsu Ya nuna musu hanya alamar su kauce. Mamaki ya kama su ganin mace a gaban motar. Har sun yi nisa suka ji ta ce "She is My Wife don't think Rubbish." Murmushi suka yi kawai suna wucewa.

Ya zuba mata ido bayan ya yi Unlocking motar yana kallonta kamar ya tuntsire da dariya ganin yarda ta sha kunu. Buris ta yi da shi kamar bata jinsa ta ma lumshe ido hawaye na bin k'uncinta.

Ya fice daga motar Har yana y'ar wak'arsa alamar babu abinda ya dameshi. Ji ta yi Ya bu'de motar yana sunkuyowa sosai kamar zai ha'de jikinsu "Za ki shiga ko sai an shigar da ke?"

Da sauri ta ce "Wallahi ba zan shiga ba, sai ka mayar da ni inda ka 'd'auko ni."

"Fine and Good." Ya fa'da yana 'd'an sakin murmushin k'asan kumatu. Ji ta yi cak ya sunkuceta ba kunya ya fara tafiya da ita. Kunya sosai ta kamata ganin ko kunyar masu aikin bai ji ba.

"Sauke ni, zan shiga da kaina."

"Na k'i." Ya fa'da yana mak'ale kafa'da ko kunyarta bai ji ba. Duk da yana jin k'afarsa na masa zafi haka ya fara taku da ita yana 'dan 'dingishi "Abinda ya kamata kenan na shigar da amarya ta cikin gidanta." Ya fa'da yana sakar mata Kiss a lab'b'anta. Ta runtse ido tana mamakin yarda baya jin kunyar mutanen da suke wajen. Bata san su a wajensu ba komai bane sun saba ganin abinda ya fi haka musamman kasancewar su mazauna Abuja.

Har cikin falo ya direta a kan kujera yana haki "Sai nauyin tsiya y'ar lukuta kawai." Wani kallo ta zuba masa mai nuni da tsagwaron raini. Fuskarsa ya gintse sosai don shi ba namiji bane da zai 'dau raini duk son da ya kewa mace. "Kada ki sake maimaita kwatakwanci kallon nan a kaina ba zan 'dauki raini ba hope you get it?"

Tabi bayansa da kallo, yana shigewa wani corridor. Ta saki ajiyar zuciya tana bin yanayin falon da kallo. Tsaruwa iya tsaruwa komai Ma sha Allah. Sai dai ita ba anan hankalinta yake ba zuciyarta gaba 'd'aya tana kan Abbanta da yarda zai ji idan ya samu labarin ta biyo Hisham Har Abuja kada ma Umma ta ji labari. Ga shi wayarta a gida ta barta dama bata je da ita makarantar ba.

Tana nan zaune ba tare da ko motsi ta yi ba. Ya fito da alama wanka ya yi yana sanye da wando three quater da riga armless ya zauna daga wata kujera can mai fuskarntarta yana kallonta lokaci guda kuma yana danna waya "Yauwa Aliyu, maza ka shigo yanzu na iso." Ya fa'da yana sake mayar da kallonsa kanta. Ya mik'e tausayi take ba shi amma ya lura idan Ya mata da sauk'i guduwa za ta yi. "Ta shi muje na nuna Miki 'dakinki, kin zauna da hijab kamar wata matar Liman, ki je ki yi wanka da kayanki a ciki."

Ba musu ta bi bayansa, don ta lura idan ma ta yi musun bata cin riba. A tsakiyar 'dakin Ya tsaya yana fuskantar ta inda take tsaye a takure "Nan ne 'dakinki.. kuma ki cigaba da min rashin kunya ki ga idan za ki ci riba ba zan 'dau rainin mace ba duk son da nake mata, I can't tolerate it kada ki yi amfani da damar son da nake miki. Idan kika ji k'ara daga nan alamace ta akwai bak'i a babbar k'ofa don akwai tazarar da ba lallai ki ji bugu ba. Ki yi wanka ki yi sallah ki fito mu ci abinci na San zuwa lokacin Aliyu kuku na Ya gama. Kitchen 'din ki yana babban falo."

Daga haka ya saka kai ya fice bayan ya yi kissing lab'banta da suke fisgar hankalinsa tuntuni daurewa kawai yake Amma shi ka'dai Ya San yarda yake son ya jita a jikinsa.

Sauda ta bi shi da kallon mamakin canzawarsa, wai shi ba ya buk'atar raini ta saki murmushi tana ayyana "Zan baka mamaki Hisham, ba zan rainaka ba, amma yanzu zan hau nawa dokin fushin Har sai ka yar da girman kan da kake tunk'aho da shi ka rarrasheni ka kuma janye furucinka, zan nuna maka Matan ma suna suka tara Mari fa! Ni ka Mara?"

To fa! Ya wannan zaman zai kasance A Abuja? Me kuma Abban Sauda zai ce yayinda Ya fuskanci Hisham Ya tafi da matarsa?

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now