Sosai Hisham ya ji Kiran sunan har cikin ransa, don haka cikin azama ya 'dago ya zubawa Abban idanuwa cike da rauni. Sab'anin hasashensa da zatonsa sai ya ji Abban ya ce "Lokaci yana ja Hisham,  har yanzu ban ji komai ba. Zuwa yanzu ya kamata na san matsayar wajen da muka kwana kai ka samu hutu, itama yarinya ta huta da aurenka da yake kanta take yawo da shi, da nauyinka da yake kanta. Abu 'd'aya yasa har aka kai yanzu ban maka magana ba, shine na baka lokaci ka nutsu ka yi shawara da zuciyarka ko kai da kanka zaka gane rabuwarku itace mafi a'ala sai aka yi rashin sa'a soyayya ta k'unshe maka ido. Zaman aure ba zai tab'a yiwuwa tsakaninka da Saudatu ba, bisa la'akari da tarin hujjoji da bai zama lallai kai ka hangosu ba tunda sonta ya rufe maka ido. Akwai nisan banbanci a tsakaninku mai tarin yawa. Dama na amince wa aurenku bisa bin umarnin Baffan Wudil kada ya ce ban mayar da shi uba ba. Don haka a yanzu nima ina son sanar da kai ko yaya ka kai ga Son Saudat ba zan amincewa zaman aurenku ba, wallahi ka ji na rantse maka ba Zan amince Saudat ta koma gidanka ba, ba kuma fushi na yi ba ko kuma ina ganin laifinka ba a'a ko ka'dan har abada kana da k'ima da mutunci a idona kuma ko yanzu zan iya baka dama ka aurar da Saudat ga duk wanda ka so don in nuna maka kana da iko da Saudat. A kullum ba na banbanta ka da yaran da na haifa a cikina Soyayyar da nake maka ce ya sa bana son ka fa'da fushin sab'awa iyaye, fushin iyaye yana salwanta rayuwar yaro ya tab'arb'arata, tunda ba su amince da aurenku ba to nima ban amince ba ka dubi girman Allah ka kawo k'arshen badak'alar nan da ta k'i ci ta k'i cinyewa. Ka tuna su iyayenka tuni suka tsammaci ka saketa don haka kaje na baka kwana uku kacal ka kawo min takardar Saudat nan gaba na, Allah ya maka albarka ya baku hak'uri da danganar rashin juna." Daga haka Abban ya ja baki ya tsuke Hisham kuwa ya rasa a duniyar da yake sam bai gama gane zantukan Abban ba, wani irin jiri yake ji. Abba kuwa duk da tausayinsa ya dabaibaye zuciyarsa bai nuna masa ba madadin haka sai ya dinga jan adduoi a zuciyarsa na nemawa Hisham 'don sauk'i da taushin zuciya.

Sosai zuciyar Hisham take bugawa jikinsa ya jik'e sharkaf da gumi da kyar ya mik'e idanunsa na neman zubar da hawaye ya kalli Abban ya ce "Abba Nagode, sai da safe."  Ya mik'e yana ha'da hanya ya fice daga gidan.

Abba ya bi shi da kallon tausayi yana jin kamar zuciyarsa zata karye ya ce yazo ya amince masa ya tafi da matarsa, sai dai baya jin ko mutanen duniya za su ha'du zai amince da hakan.

Umman Saudat ce ta fito daga 'dakin fuskarta fal murmushi ta ce "Sai yau na samu Saida Abban Saudat, wallahi da na zata mayar masa da Saudat za ka yi ba ka ji yarda zuciyata take taratsatsin bamabaman b'acin rai ba. Yau kam ka burgeni Abban Saudat su je can su ci arzikinsu mu ma mu rungumi talaucinmu. Yana kawo takardar sakin a ranar Zan aika a jide kayan tas daga gidan 'dansa. Idan ya so bayan y'ar senator su ha'da masa da y'ar shugaban k'asar amuruka ma."

Dakata Maryam!" Abba Mustafan ya fa'da cikin zafin rai "Bana son irin wannan kuma sam ban ji da'din furucin Ki ba. Ban kuma jin da'din kallon da kikewa yaron nan ba, haba kada ki bari fa yaron nan ya fuskanci kina k'insa fa, zaki zama butulu mai manta alheri me kika aikata haka da wani ido za ki kalleshi idan ya fahimci kina goyon bayan rabuwar aurensa da y'arki duk da tarin halaccinsa garemu? Bari in gaya miki har a zuciyata ina jin ra'da'din raba aurensu da zan yi yadda na 'dauki su Khalil haka na 'daukeshi a zuciyata sam ba banbanci. Don kuwa shima bai banbanta ni da mahaifinsa ba, ina tarin kawaicinki da kararki Maryam? Na ce Ina suka tafi? Ina kika bar fulatancinki har ki ke son ki fifita soyayyar y'arki akan 'dan wani? Anya kuwa Maryam ba za ki ji kunya ba? Ba 'a san nagartattun mutane da wa'dannan halayen ba. Mutumin kirki shine mai rufe ido ya k'i nasa akan 'dan wani don kawai kawaici da alkunya, amma nema kike duk ki zubar da wa'dancan halayen k'ek'e da k'ek'e ki ke nuna son y'arki akan mutumin da ya yi mana halarci mutumin da bai k'yamaci takaucinmu ba duk da tarin arzikinsa kada ki sake shiga lamarin nan bana so kina ji na? Ki bar ni da shi  na san ta yarda zan biyo masa ba tare da ya yi tunanin mun masa butulci ba. Ko kuma mun fi son farin cikin y'ar mu akan nasa farin cikin. Idan kika yi abinda ya fahinci hakan ba zan iya ha'da ido da Hisham ba ina tabbatr miki, ya min komai a rayuwa ya so ni lokacin da dangi suka juya min baya, ya girma mani lokacin da dangi suka k'ask'anta ni. Bai cancanci tozarci a wajenmu ba, kada ki sake Maryama Bana so!! Bana so!!" 

Cikin wani yanayi yake magana wanda hakan yasa Maryama ta fahimci ba k'aramin b'ata masa rai ta yi ba ta kuma hango b'acin ran kwance a fuskarsa. Tuni dana sani itama ya shigeta ta ji tana kunyar ha'da ido da Hisham ba da wani idon zata kalleshi?

Kina jina?" Maganar Abba Mustafan ta sake katseta da sauri ta 'daga kai "Na ji Abban Saudat ka yi hak'uri In sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba."

Ya saki ajiyar zuciya ha'de da cewa "Allah yasa Maryam, hakan na fi buk'ata."

Saudat kuwa tana shimfi'de akan gadonta kuka kawai take risgawa zuciyarta na tsananta bugu a yanzu ta tabbatarwa zuciyarta rabuwa da Hisham kamar saka ranar mutuwarta ne. Ta dinga jimanta kwana uku kacal ba ka Hisham a zuciyarta da sauri ta dinga jijjiga kanta tana fa'din kada ka soma Abba Rabani da Hishma kamar rabani da numfashina ne." 

Hisham fa? .......

Da kyar ya kai kansa wajen motarsa sabida jiri da layi da yake yi. Yafi minti talatin ya kasa sarrafa kansa ya ja motar sai da yaga lamarin yana ta'azzara sai ya kira k'aninsa Mahmoud don ya zo ya kai shi gida.

Mahmoud bai b'ata lokaci ba ya iso. Daidai lokacin khalil ya zo shiga gida har zai wuce sai ya ga rashin dacewar hakan ya dawo ya k'arasa wajensu yana mik'awa Mahmoud hannu, amma Mahmoud ya shareshi fuskarsa babu wani annuri ya 'd'aga masa hannu. Khalil murmushi ya saki don ya girmewa Mahmud nesa ba kusa ba don bai wuce sa'an Sa'eed ba. Hisham ya sauke glass 'din motar yana kallon Khalil ya ce "Ka dawo?" D'aga masa kai ya yi kafin ya ce "Ya na ganka hakan? Ko baka jin da'di ne?"

Hisham ya saki yak'en murmushi ya dafa kafa'd'ar Khalil.  "Khalil ka taimakeni kada Abba ya raba ni da Saudat ya kafa min shara'di nan da kwana uku na saki Saudat ba zan iya ba Khalil? Menene Mafita?" Mahmud da yake gefe Cikin mamaki yake kallon yayansa wato dama bai saki Saudat ba su iyayensu suna can suna hauka da zaton ya saketa cab ai kuwa a daren nan zai kai musu labari.........




Jikar Nashe.😊😊😊❤️

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now