Ko da aka tashi daga lecture tana fitowa ta hango shi zaune a saman motarsa. Ba ta yi mamaki don ta san yana da time table 'din su.

Ya mata kyau sosai cikin tsarin shigarsa jar rigar polo da black jeans. Fuskarsa a ha'de take sosai duk matan da suka zo wucewa sai sun dube shi, yana rik'e da wayarsa a hannu yana dannawa.

Saudat itama fuskar ta ha'de sosai kafin ta isa wajensa. Don ba zai yiyu ya dinga 'daga mata hanci ba. Yana ganinta ya durgo daga saman motar idanunsa a kanta dariya na k'ok'arin kubce masa ganin yarda ta yi kicin kicin da fuska a zuciyarsa ya ce "Dama ya lafiyar kura..." tunda dama  k'iris take jira hakan ta faru. Ya san Saudat da fa'da da tsiwa, ta tsaya kawai a gefe har da rik'e k'ugunta tana sake tuno baki. "Ni fa ba wata motarka da zan shiga, don ban ga dalilin da zai saka na shiga motarka ba bayan kai kanka ka san rabuwar mu ta za.........

Wani kallo ya watsa mata, hakan ya sa ta ja 'dan bakinta ta tsuke a zuciyarta ta raya masifaffe kawai."  Ya dinga bin 'dan bakinta da kallo kafin ya ce "Da kin sake kin k'arasa Wallahi yau sai kin raina kan ki, ki kuma shiga mota mu tafi bana son rashin kunya."

Cikin tsiwa duk da idanunta sun rusuna ta ce "Idan na k'i fa?" Dariya sosai Hisham ya tuntsire da ita yana jan lab'b'anta ya ce "Sarkin tsiwa, abu mai sauk'i idan kika k'i sai mu kwana a nan don wallahi ba zan yarda ki shigar min motar haya ba, ba ki san yarda nake kishinki ba ko?" Saudat ta zumb'uri baki ta ce "Wallahi Y.Hisham da ka daina wahalar da kanka don kana ji kana gani zan auri........."

"Saudat!" Ya fa'da cikin k'araji. "Be careful, wallahi zan miki abinda za ki raina kan ki wuce mu tafi"

Ganin b'acin ransa ya bayyana k'arara da sauri ta shiga motar ba tare da ta sake jayayya ba.

Tunda ya ja motarsa bai sake magana ba har ya dangana da gidansu Saudat 'din. Tana ganin ya yi parking da sauri ta fice har tana ha'dawa da gudu. Hisham ya saki murmushi bayan da ya bi bayanta da kallo a hankali ya saki ajiyar zuciya ha'de da cewa "My Lovely Saudat!"

____

Alhaji Hamza ya dubi Hajiya Balaraba ransa a b'ace ya ce "Yaushe rabon da Hisham ya zo gidannan?" Sai da ta 'dan yi jum sannan ta ja ajiyar zuciya ha'de da cewa "Cab yaushe rabon da na ga Hisham a gidan nan ai na Sallama musu Hisham, Fushi yake damu tunda muka korar masa mata, ni kuwa da zamansa da wannan tsiyar gwara ya dawwama yana fushi da mu." Ta fa'da fuskarta cike da rauni da nuna zallar tashin hankalin da take ciki. Alh. Hamza ya ja tsaki "Yanzu shi sabida y'ar gidan Mustafa ya zubar da mu iyayensa." Girgiza kai ta sake yi kafin ta ce "Ni fa ba wannan ba, ba abinda nake tunawa zuciyata ta dugunzuma ta b'aci kamar idan na tuna sai da ya kusanci yarinyar nan sannan ya kusanceta fatana 'Daya da burina Allah yasa bai jefa mata k'wansa a mahaifa ba." Alhaji Hamzan ya sake b'ata rai sosai kafin ya ce "Idan ma ya shiga da fitar da shi." Haka suka cigaba da jimami da tattauna maganar yarda har ya iya ya yi burus da su, kamar ba Hisham mai k'aunarsu da gudun b'acin ransu ba...

___________

Haka rayuwar ta cigaba da garawa. Tun Hisham yana saka ran su Abban za su amince Saudan ta koma har gwiwoyinsa suka yi sanyi ya tabbatar Abban shima a wannan karan an kai shi bango tunda har ya kasa tausaya masa tsawon wannan lokacin. Tsawon wata guda ana magana 'daya ta k'i ci ta k'i cinyewa.

Yau ya ci alwashin sake k'undunbalar tunkarar Abban da zancen duk da yana gudun samun bahaguwar amsa daga Abban.

Sai da ya je gidan Abban yana lazimi don haka ya ja gefe ya zauna don ya san ko ya yi magana Abban ba zai amsa shi ba matuk'ar yana lazimi. Gaisuwar ma da kai ya amsa masa ya cigaba da laziminsa.

Sai da ya ja addu'oi sosai su da suke zaune a tsakar gidan suka 'daga hannayensu suka amsa, sannan ya sake mayar da kansa kan Hisham da yake zaune gefe ya takure. Sai da ya yi tasbihi da neman dacewa a wajen ubangiji sannan yasa harshe ya kira sunan Hisham 'din da kaurararriyar murya da bata yi kama da wasa ba.

Zumuncin ZamaniDär berättelser lever. Upptäck nu