Daidai lokacin da su Zainab suka fad'o d'akin a gajiye lik'is. Zainab ta d'aka mata duka a zafafe ta ce "Wallahi kin cucemu kin ga kuwa Dinner? Ke na manta tashi kije In ji Hisham yana waje yana jiranki yace a gaya miki sam yau ba zai iya barci ba har sai ya gan ki. Gaskiya Hisham yana matuk'ar son ki da gaskengaske, shi fa ya kawo mu daga can gidansu don
Kawai ya gan ki."

Saudat ta ja tsaki ta ce "To aku ni kin cika min kunne mai zan je in masa bayan ya dawo daga wajen masoyiyarsa?" Dariya sosai suka yi har da buga k'afa Zainab ta ce "Kishi k'umallon mata." Bata kula su ba ta fice daga d'akin don itama tana muradin ganinsa.

A tsaye a k'ofar gidan ta same shi yana nad'e da hannunsa a k'irjinsa. Kicin-kicin ta yi da fuskarta had'e da cewa "Ga ni." Ya bud'e ido yana kallonta sosai "Me kenan Saudat wace irin magana ce wannan ba rusunawa bakomai. A haka kike so ki mallaki soyayyata ke kad'ai, ya zafin kishi yake son saka ki ki aro tarbiyyar da ba taki ba." "Me zan yi da ragowar wata?" Ta fad'a cikin karyayyiyar murya Da sauri Hisham ya ce "Ni ne ragowar? Shikkenan nagode sakayyar da zaki min kenan? Duk da na biyo dare don na gan ki. Zo mu je mota na baki ragowar cake d'in dinner ne na rago miki? Kema ina so na baki a baki mu yi hoto." Wannan karan Saudat kasa mallakar kanta ta yi sai ji tayi hawaye na zubo mata ta dinga jijjiga kai tana cizar lab'ba ta fara zabga masa harara. Da sauri ya rik'o gefen gyalenta ganin tana shirin shigewa gida "Ni ki ke harara? Wallahi zan yi maganinki ashe tsiwar tana nan rusunawa ta yi, yarda Faree..." Ai bata bari ya k'arasa ba ta figi gyalenta ta shige gida da gudu. Hisham dariya ya yi sosai kafin ya ce "My Heart kenan."


**********

Ranar lahadi ne ya kama d'auri. Aure. Don haka kowane gida damk'am yake da jama'a babu masaka tsinke, musamman b'angaren ango, inda dandazon jama'a suka d'unguma suka tafi gidan Sule Jami'i don halartar d'aurin auren y'ar senatorn. Mutane da yawa ma ba su san har da y'ar gidan Mustafan za'a d'aurawa aure ba.

Can kuwa b'angaren su Saudat Limamin unguwarsu Alh.Hamza ne kawai da wasu tsirarin mutane suka wakilci uban ango daga b'angarensa. Sai ko angon da wasu daga cikin abokansa wad'anda suka bawa abin duniya baya. Mahaifinsa Alh. Hamza a cike yake da shi musamman da ya tambayeshi kud'in sadaki ya ce ya basu. Ya dinga surfa bala'i tamkar zai aro baki.

Duk da zuciya mai laushi irin ta Abba Mustafan, tabbas abinda yau suka masa ya tab'a zuciyarsa, ganin ba wani d'an uwansa li'abbi (na wajen uba) da ya halarci d'aurin auren y'ar tasa, duk da cewa wanann shine auren y'a da zai yi na farko. Duk don matsayin da Allah ya ajiyeshi na zamowarsa talaka. Babu wanda zai masa Waliccin y'arsa sai abokinsa. Allah ya kyauta.

A ranar da aka d'aura auren, ranar ne ya zama ranar kai amare. Inna Maryam ta ce da Umman Sauda "Shigar sauri
Zamu musu tamu ta zama uwargida ko an k'i ko an so.." Shi kansa Hisham dalilinsa kenan da ya dinga yiwa Inna Maryam waya akan ya turo motocin d'aukar amarya. Inna maryam babu ja ta ce "Su taho maza ayi a kaita an shiryata." Hisham ya zubawa abokinsa Nura ido ya ce "Nura ka hanzarta d'auko min matata please!" Nura ya zabga masa harara ya ce "Wallahi Hisham ka ji tsoron Allah, don na lura k'iri-k'iri kake nuna banbanci ka ji tsoron Allah kada ka tashi da shanyayyen jiki wallahi." Hisham tsaki ya yi yace "Ce maka na yi bana musu adalci? Ina adalcina a inda naga zan iya zuciyata kuwa ba ni nake iko da ita ba Allahn da ya yi ta shi ya saka min don Saudat fiye da na Fareeda. Sai yaya?" Duk abokansa suka zuba masa ido ba tare da sun ce komai ba.


***********

Hakane kuwa ya kasance k'arfe 4:00 na yamma dandanzon motocin suka ci burki a bakin lungun su Saudat. Ta sha kuka sosai har ta bawa jama'a da dama tausayi tabbas yau ta tabbatar da maganar hausawa da suke cewa Aure yak'in mata. Yarda ta kanainaye Ummanta shine abinda ya sosa ran wasu har suka fara zubar da hawaye. Haka suka yi sallama da Ummanta tana sake jaddada ba sai na ce miki komai ba Saudat in dai kin biyo ni ba yabon kai ba zaki zauna k'alau cikin aminci a gidan mijinki tunda dai kin san ni ko yaji ban tab'a yi ba."

Gidan Amaren babu kowa don kuwa ba su san za su musu shigar sauri ba. B'angarenta ya yi kyau sosai daidai gwargwado ba zaka ce min d'iyar Abba Mustafa bace ta samu wannan tagomashin. An had'a mata kicin d'in nata daidai da tsarin y'an boko ba wani tarkace. Hakanan falukanta sai son barka. Haka kowa ya shiga yabon b'angaren nata.

K'arfe 6:00 daidai dandazon motocin suka kawo fareedah, da tunanin ita aka fara kawowa. Sai dai murnarsu ta koma ciki sanda suka tarar an kawo Saudat d'in Ta tabbata babu musu itace Uwar gida. Haka suka shige suna shewa da habaice-habaice ba tare da Addu'oin da malamai suke kwad'aitarwa a yi ba idan an kai amarya. Sab'anin Saudat da suka shiga da addu'oi fal bakinsu.

Ba su yi k'ok'arin kaita d'akin Saudat ba sai ma harara da kallon banza da suka dinga watsa wa d'akin.

Dangin su Abba Mustafa ne suka shiga sashen Sauda ga tunaninsu za su ga fayau, sai dai suka ga sab'anin haka ga mamakinsu Abba Mustafa ya yi tasa bajintar sai dai madadin yabo sai ka ji suna cewa "Ai Hisham ya yi k'ok'ari don Mustafa ba shi da kud'in da zai yi wannan."

Kafin 8:00 gidan ya yi wayam, idan ka d'auke sashen Fareeda da k'awayenta suke zaune jingin suna jiran siyan baki. Suna kuma aikin zuga Fareedan akan kada ta amince ta tsaya ta jajirce ta zama itace uwargida duk da an Riga kawo Saudat d'in......

Jikar Nashe ce... 😊😊🙏❤️

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now