Inna Falmatan ce dai ta sake magana da cewa "Ai hakan ya yi kyau ya kyauta, ya kuma hutashshemu musamman kai lefen gida biyu ne can muka kai na kishiyarta gidan Senator Sule Jami'i yanzu ina kayan suke?"

Umma ta mik'e tana mamakin yarda ba wanda ya mata kara da kanta ta dinga janyo manyan akwatunan masu tsadar gaske tana direwa a gabansu. Baki sake cike da mamaki suke kallon kayan ko kad'an ba su san kayan za su kai haka ba. Yayar Hajiya Balaraba ce ta kasa jurewa ta ce "Kan uban can amma Balaraba ta yi sake kun shanye mata d'a tsaf irin wannan narka dukiya haka tamkar za'a kai gidan wani k'asurgumin k'usan gwamnati ko d'an kasuwa." Inna Falmata ma jinjina kai ta ke ta ce "Ai kuma daga gani ba sai an yi tambaya ba, yarda dai aka sammace Mustafa a allon almajiran ubanta haka aka summace Hisham to Allah dai yasa ita ba jininki na tsiya ta d'auko ba ta tsiyata shi a banza da wofi." D'if Umman tayi tabbas maganganunsu sun yi tasirin da suka haddasa mata matsanancin bugun zuciya da b'acin rai. Ta saki ajiyar zuciya ganin yarda suka mik'e suna tsallake kayan ba tare da sun gani ba idanunsu bayyane da haddasa k'iri-k'iri. Tana jiyosu suna cigaba da cilla mata bak'aken maganganu ita da iyayenta, ta runtse ido murmushi gami da hawayen takaici suna zubo mata duka a lokaci guda a fili ta furta tabbas talauci bai yi ba, don bakomai ya janyo mata wannan wulak'ancin ba sai talauci, yau da su masu kud'i da murna da zakwad'i za 'a so auren y'ar su amma ji yarda ake gudunta yanzu duk a dalilin rashin kud'i. A fili ta ce "Allah ka fitar da mu daga wannan k'angin mu ma." Ta fad'a tana d'aga hannayenta sama.


_______________

Shirye-shirye ya kankama daga can d'aya b'angaren na masu hannu da shuni, shiri ake gagarimi na bikin ba ga dangin angon ba ba ga na amaryar ba kowa so yake ya nuna k'aryar arzikin da yake da shi. Su Saudat dai sai dai godiyar Ubangiji suna ta kayan d'aki ma wa yake ta wani hidimar biki.


Hisham ya shiga gidan nasa mai d'auke da sassa biyu d'aya Saudat d'aya Fareedah. Murmushi ya saki ganin yarda gidan ya fara d'aukar haske da yake gidan Fareedan ya fara shiga kaya ne na goge raini ake zuba mata zubi da k'irar turkey
Komai da yake gidan kayan waje ne. Sanda ya shiga sashen Saudat sai da ya ji tamkar ya yi hawaye don babu komai sai malalan tiles sai a yanzu zuciyarsa ta tuna masa da Abba Mustafa ba shi da komai kuma bai bawa kowa ajiya ba, da kuwa sam ya manta kamar wanda aka kawar masa da tunaninsa. Cikin azama da sauri ya juya ya shiga motarsa ya figeta a guje, har mai gadin yana mamakin dalilin saurin nasa.

Isarsa gidan ke da wuya ya shiga da sallama, ba kowa a gidan daga Umman Sauda sai Abban Sauda ita Sauda a lokacin ta tafi rabon I.vn Walima.

Jikin Hisham a sanyaye ya samu gefe ya zauna cikin ladabi ya fara gaishesu. Da walwala sosai a fuskokinsu suke amsawa kai ba zaka ce akwai wata matsala tattare da su ba.  Abban Saudat ya ce "Malam Hisham ya shirye-shirye? Dafatan dai ba matsala?" Cikin jin kunya sosai ya yi k'asa da kansa kafin ya ce "Babu komai Abba sai godiyar Ubangiji." "Masha Allah!" Abban yace yana cigaba da danna counter d'in da take hannunsa. Tsawon mintuna Hisham d'in yana son furta abinda yake ransa amma yana shakkar Abban gani yake kamar ba zai amince da buk'atar da yazo masa da ita ba. Da kyar ya yi k'undunbala ya ce "Abba dama da wata magana na zo." Abban ya mik'e yana gyara zamansa sosai, Umma ta yi nufin mik'ewa Abban ya dakatar da ita "Sha zamanki, na san babu wani abu da Hisham ba zai so ki ji shi ba ni ma kuma kin san ba ni da sirri in dai a wajenki ne, Ina jinka Hisham fad'i abinda ke tafe da kai Allah yasa mu ji alheri."

Hisham ya shiga wasa da yatsunsa kafin ya ce "Abba dama alfarmarku zan rok'a don Allah bana son a kai Sauda da ko cokali gidana zan mata komai a aljihu na."

Farin ciki sosai Abba Mustafan Yayi tabbas Hisham ya cika d'a na gari abin alfaharin ko wane iyaye sai dai ba anan gizo ke sak'ar ba yana gujewa Sauda gori irin na dangin miji musamman aka ce muku dangin miji masu k'arancin ilimi da tunani "Madalla da d'a na gari, na ji dad'i sosai Hisham sai dai ka yi hak'uri buk'atarka ba zata amsu ba, bisa dalilai da hujjoji masu k'arfi babban dalilina GORI bana son a dinga mata gori musamman gidan kishiya, bayan wannan kada ka manta mahaifinka ya kafa mama sharad'in duk ranar da ka sake taimakon mu bai yafe maka ba, don haka ka bar zancen a iya nan, zan kai Sauda da duk abinda Allah ya hore min, kuma a tarbiyyar da na bata ina tabbatar maka da ko da karauni na kaita kishiyarta tana da gadon diamond ba zai damu Sauda ba, ta san matsayinta ta kuma san waye ubanta ba ni da shi ban bawa kowa ajiya ba, na kuma d'orana y'ay'ana a turbar samu da rashi duka na Allah ne, don haka kada ka damu. Allah ya yi maka albarka akan kyakykyawar niyyarka na kuma ji dad'i sosai." Hisham ransa bai so ba amma haka ya mik'e zuciyar sa cike da tunanin ta inda zai taimakawa Abban ba tare da ya san shi ne ya taimaka masa ba.

Ko da ya koma office tunanin da ya dinga yi kenan, ga shi da kud'i tamkar su kasheshi amma ba ta halin da zai iya taimakawa matarsa duk a sunan wai kada
A mata gori, Allah ya kaisu lokacin da zata tare a gidansa ya siya mata duk abinda yake so idan ya so yaga uban da zai ce masa don me? Da Abba Mustafa ya barshi ko kud'insa za su k'are duka sai ya mata irin kayan da aka k'awacewa Fareeda gida da su. Company uku gareshi banda na Atamfofi da shadda akwai companyn gine-gine da na kwangilolin titi ga kuma kamfanin yin taliya da fulawa, amma mahaifinsa ya masa karantsaye ya hana shi taimakawa bayin Allahn nan don son zuciya. Bai san sanda ya runtse idanunsa ba kawai sai ji ya yi suna zubar da hawaye. Murmushi ya kubce masa tunanin hanya d'aya jal da ta rage masa yana tunanin wannan hanyar kam babu mai ce masa don me? Don musulunci ne ya bashi dama.

___________

Ana yin sallahr Isha ya isa gidansu Saudan amma ba shiga ya yi ba, waya ya yi mata ta fito ta sameshi a waje. A gajiye take sosai don ba k'aramar zirga-zirga suka sha ita da aminiyarta ba Maimunatu.

Tana jan k'afa ta isa motarsa, shi kuwa idanu ya zuba mata yana hango yarda gaba d'aya jikinta ya nuna mabayyaniyar gajiya. Ya sake ware idanunsa yau kam yana morewa kallonsa ganin irin kyawu da k'irar jiki da Allah ya mata. Ya ja kalmar Hamdala ga Allah a zuciyarsa.

Da sallame ta bud'e motarsa ta shiga tana sakin murmushi ta gaida shi. Hisham shima murmushin yake ya ce "Ran amaryata ya dad'e. Duk na lura yau kin wahalar min da kanki." Tsam ta d'inke fuskarta murya a shak'e ta ce "Uwargida dai." Hisham ya tuntsire da dariya ya ce "Tuba nake da girman kujerarki Uwargida, amma kuwa a yi haka Fareeda ta ta girmeki girma ba kad'an ba." Ta sake cono bakinta ta ce "Wallahi ko haihuwa ta tayi ni nafi son na zama uwargida akan ace ni ce amarya." Da sauri ya kawar da zancen don baya son ya tunzirata ta sake masa fushin da ta masa wancan karan. "Amarya guda ba gyaran jiki bakomai haka za'a kai ki gidan mijin? Ke haka ake uwargidan ba zaki tambayi kud'i gyaran jiki ba, tun yaushe Fareeda naga ta fara ko so kike ta fiki haskawa?" D'if ta yi da fuskarta duk wani annurin fuskarta ya kauce ko kafin Hisham ya ce komai Hawaye sun fara zuba a idanunta...

Daga  taskar jikar Nashe❤️🙏

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now