Bayan an gama gaisuwar kowa a d'arare Hajiya Falmata cike da Izzarta itama da nuna bajintar da suka yi wajen had'a kayan lefen ta gabatar musu da kayan tana nazarin fuskarsu ta ga wani irin kallo za su yiwa kayan. Ganin ko kallon kayan ba su yi ba ya sa Inna Falmatan ta dubi Sadiya K'aramar k'anwarsu ta ce "Bubbud'a kayan nan su gani mana." Da sauri dangin amaryar suka dakatar da ita d'aya daga cikin Aminanta ta ce "No need ta bar shi ma menene bak'o a wajenmu za mu gani later." Gaba d'aya gwiwoyin Inna Falmata dana sauran wad'anda suka san ciwon kansu suka yi sanyi, don dole suke dariyar yak'e. Inna Falmata ganin ba arziki ta mik'e ta ce "To mun barku lafiya, idan aka saka lokacin bikin a aiko mana." Saura kuwa sai godiya suke, godiyar da ta k'ular da Inna Falmata ta shiga wurga masu harara. Har sun kai k'ofa Hajiya Sa'a ta kalli wata budurwa a cikinsu ta ce "Ke zo nan." Yarinyar ta juya Hajiya Sa'a ta nuna mata wata leda mai d'an girma "Gashi nan, maza ki d'auka ki kai musu tukwucinsu ne don ni ba ni da wani lokacin saka orderr snacks."

Suna gama ficewa ko k'arasawa falon ba su yi ba na zauna falon suka tintsire da dariya, Hajiya Sa'a ta ce "Makwad'aitan banza, su nan sun zata wata tsiyar suka kawo da zamu dinga Rige-rigen gani ko menene abin burgewa a akwatina sha takwas, ga can in da ake abin arziki ana kai akwatina dozen biyar dozen goma."

Yayar Senetorn ma tsaki ta zabga kafin ta ce "Shima dai Sule ban ga dalilinsa na d'aukan santalar y'a ya bawa d'an yaronsa ba, fisabilillah ina laifin ya samar mata y'ar shugaban k'asa ko d'an mataimakinsa, amma wannan mai na sama ya ci balle ya bawa na k'asa idan banda suma su dinga harin arzikin shikkenan ka siyar da akuya ta dawo tana ci maka danga..." Hajiya Sa'a ta sake tunzira ta ce "Ke ma dai kya fad'a Hajiya, ana harkar arziki shi yana rakitowa kansa tsiya da kud'insa, dubi don Allah tururuwar da suka yi tamkar gidan biki, sam bana farin ciki da wannan auren duk da dai yaron yana tashin kud'i amma ai ba kud'i irin wanda mu za mu yi zakwad'in ba shi y'a saboda shi bane."

(Tirk'ashi shi dama lamarin duniya haka yake, idan kana ganin ka fi wani to shi fa wani ganinka yake kamar yaron gidansa don haka ba'a son tutiya da arziki."

Haka suka koma gida gwiwoyinsu a sage, sai dai babu wanda ya furta kalmar 'a' a cikinsu ba don komai ba sai don mak'udan kud'in da aka shak'a musu a matsayin tukwuici miliyan biyar cif ai ko ta rufe bakin surutu tsaf. Madadin k'orafi ma jinjina k'ok'arinsu suke ta hanyar yamad'id'i da cewa an musu harkar girma wad'annan kud'in ai sun fi mana tarkacen soye-doyen da za'a ba mu. Kai Hisham ya yi dace da gidan k'warai ya tako arziki wannan gida na su ai ko a aljanna aka baka shi sai kace Falillahil Hamdu.

Mhmmn! Kud'i kenan k'are magana!

_________________

Gidansu Sauda kuwa fal ya cika da y'an uwan Umman Sauda da y'an unguwa masu ganin lefe. Akwaninta goma sha biyu cif kuma komai a ciki mai tsada ya saka mata. Kowa fad'i yake son barka a dangin Abbansu kuwa y'ay'an Inna Halima da Inna Haliman ne kawai suka zo wanda suke uwa d'aya uba d'aya da Abba Mustafan. Zance guda ake Sauda ta tako arziki Ma sha Allah.

Da Abban Sauda ya dawo ya ga kayan fad'a ya dinga yi yana fad'in siyar masa da y'ar zan yi zai zo ya sameni Shi Hisham d'in.

Ita kuwa Sauda ba zata ce ba ta yi farin ciki ba, sai dai ta ce farin cikin nata ragagge ne, don tunda ta samu labarin su biyu zai aura gaba d'aya gwiyoyinta suka yi sanyi da maganar auren don ta san tarin matsaloline zata fuskancesu jingim. Tun ranar bata sake ganin Hisham ba don ko yazo barcin k'arya take Sam bata son had'uwarta da shi. Kishi ne yake nuk'urk'usar zuciyarta.

Da daddare Hisham d'in ya sake zuwa kamar kowane lokaci baya gajiya zai zo ko ba zata fito ba.

Shigar k'ananan kaya ne a jikinsa sun yi matuk'ar amsarsa. Sai zabga k'amshin turaren Lulu yake. Ya yi kyau sosai zatinsa ya kammala ya kuma nuna cikakkiyar haibarsa da kamalarsa ta mazantaka.

Saudat ta sake lafewa a katifarta kamar mai barci, duk da tana jin Ummanta na kiranta. Tsam Umman ta mik'e ta shige d'akin. Duka sosai ta d'aka mata a cinya ta ce "Mik'e y'ar banza , ai na san idonki biyu wallahi ki kiyayeni akan wannan banzar d'abi'ar da kika d'auka, me kike nufi ne yanzu duk halarcin da yaron nan ya miki ke k'ok'ari kike sai kin zuba masa k'asa a ido? Zaki ta shi ko sai na ba shi izinin shigowa?" Da sauri Saudan ta mik'e tana turowa baki ta ja mayafinta ta nad'e kanta da shi. Ta fice daga d'akin fuskarta a had'e. Tuni ya fice daga tsakar gidan hakan ya sa ta bi shi wajen. Cikin motarsa ta shiga gidan baya ta zauna madadin gidan gaba da ta saba zama.

Wata irin ajiyar zuciya Hisham ya sauke ganin ta fito ta saurareshi ya dinga kallonta ta cikin mudubi yarda take murza hannunta fuskarta a had'e. Farin ciki ne sosai ya kamashi ganin da gaske Saudan kishinsa take ya dinga sakin murmushi shi kad'ai ji yake tamkar ya jata jikinsa ta ji yarda zuciyarsa take bugawa kuma ko wane bugu da zuciyar za ta yi da gurin soyayyarta take yi.

K'amshin turarensa ya bi ya addabi Saudat ta dinga jin wani irin feeling na saukar mata, har bata san sanda ta dinga jin b'acin ranta yana sauka daga zuciyarta ba, ta lumshe idanunta kawai kafin ta bud'esu su sauka cikin nasa k'wayar idanun. Wata irin kunya ce ta dabaibayeta ta yi saurin saukar da kanta. Da murmushi sosai a fuskarsa ya shafa sumar kansa murya can k'asa ya ce "Saudatuna Ina yini?"


Daga taskar jikar Nashe.❤️🙏

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now