Daga haka suka yi sallama. Hisham tun a mota yake kiran saudat, sai dai tana ta ringing sauda din ba ta d'auka ba. Hakan ya sa ya yi tunanin ko tana lecture don haka direct gidansu saudat din ya wuce saboda ya sake basu hak'uri ya kuma sanar da Abbansu ya amince da auren. Ya kuma sanar da su kudurinsa na kada su tashi hankalinsu shi zai yiwa saudat komai tunda ya san ba su da hanyar da za su aurar da d'iyar tasu nan da wata d'aya.
A k'asan layin ya yi parking sai dai gabansa ya fadi!! ganin a kori kura a k'ofar gidan nasu cike taf da kayansu Hisham girgiza kai ya yi had'e da saurin fitowa daga mota.
Gaba d'aya su khalil suna kofar gidan har da Abban nasu, duk kansu sun gan shi a ciki_ciki suka gaisheshi, shi din ma har k'asa ya durk'usa ya gaida Abban babu komai a fuskar abban da walwala ya amsa masa yace, Hisham ba ka jin magana ko? Ba abbanka ya hana ka zuwa nan ba? Ko kuwa da amincewar sa kazo? Hisham ya d'aga kai cikin sanyin jiki yace da saninsa nazo abba,amman don Allah Abba ina zaku naga ana fito da kaya?
Abba girgiza kai ya ce" Yanayin rayuwa Hisham ya sa zamu sanja muhalli."
Shiru Hisham din ya yi yana tunanin tabbas Abba mustapha siyar da gidan ya yi za su koma gidan haya. Amman don ya tabbatar da zarginsa sai yace Abba wani gidan kuka sake kenan?"
Abba ya d'aga kai had'e da son ya b'oye sirrinsa ya kuma basar da zancen had'e da cewa "Bari muje Hisham kada masu motar su gaji da jira."
Tsit Hisham ya yi daidai lokacin da ya hango sauda tana share hawaye. Yana kallo suka shiga adaidaita sahu amman ya kasa katabus. Sai can ya yi saurin ya shiga motarsa yabi bayansu don ya ga inda suka koma a zuciyar sa yana yi wa danginsa addu'ar shiriya. Sam babu Allah a Al'amarin rayuwarsu.
A bakin wani lungu suka tsaya sai a lokacin Abba ya lura da shi yace "A'a Hisham dama ka biyo mu ne?"
Hisham ya d'aga kansa kawai ba tare da yace wa Abba komai ba, illa bin gidan da ya yi da kallo a zuciyar sa yana tunanin wai wananan kwarrarrababben gidan anan zasu zauna,. Duk tak'amar arziki irin na danginsu gidajen kuwa kowa ya mallake. Su na gani na fada , banda wanda aka saka haya a ciki, amman a rasa mai taimaka wa wannan bawan Allah.
Cikin tsananin tunani da yake sam bai san har sun gama kwashe kayan ba tare da ya sani ba. Sai da Abba ya matso ya dafa shi yana murmushi, yace "Hisham tunanin mai kake?
Firgigit ya d'ago ya kalle shi kafin ya saki wata ajiyar zuciya yace "Abba dan Allah ina neman alfarmar ku bar gidan nan,ina da gida mai kyau a badawa layout, wallahi babu wanda ya san nawa ne, kuzo ku koma can ku zauna Amman wallahi Abba sam nan bai dace da ku ba."
Abba girgiza Kai cikin tausassan kalamai ya ce "ba komai Hisham, ita rayuwar duniya da kake gani ba komai a cikin ta hudusun fana'un ce. Komaii na cikinta zai k'are.imanin mutum ne kawai ba ya canja wa. Don haka a duk yarda ubangiji ya bar ni gode masa nake, saboda na san ba wai k'iyayya ba ce tasa ya aikata min hakan hasali ma babu wanda yake so na sama da son da yayi min Hisham ba zan koma gidanka ba, saboda ka san Abban ka yayi furucin idan ka sake taimaka mana bai yafe maka ba to bana son fushinsa ya sauka a kanka, kayi hak'uri ba zan sake karb'ar taimakon ficika daga wajenka ba. Hakan ma da kayi nagode maka Allah yayi maka albarka ya kare ka daga sharrin duk abin k'i, ina so ka zama mai jajircewa wajen yi wa mahaifinka biyayya."

Hawaye ne kawaii yake zarya a fuskar Hisham yana jin ciwo sosai, ba ciwon komai bane kuwa sai na rashin yadda zai yi ya taimaka musu. Tabbas bai yi dacen iyaye ba, tunda har za su Hana shi aikata alheri.
Abba mustapha ya dinga ba shi hakuri yana mamakin tausayi irin na Hisham. Tabbas zuciyar sa mai kyau ce Allah kenan mai fidda rayayye a cikin matacce, da kyar ya sashi ya shiga mota ya tasheta sam ya kasa ganin Saudat balle ya sanar da ita. Maganar da ta kawo shi, zuciyar sa cikin matukar kunci ya ja motar, ba gida ya tafi ba wani park ya tafi saboda yana buk'atar kad'ai cewa.

Abba mustapha kuwa yana shiga gida yabi y'ayyansa da kallo, gaba d'aya suna zaune sun zuba uban tagumi musamman khalil da idanunsa suka kad'a suka yi jajir, Abban ma ya sake bin gidan da kallo,sam ba shi da fasali gaba d'aya,d'aki biyu ne falle _ falle a gidan, sai Wani takurarren d'aki a soron gidan, da kuma kicin din langa_ langa shi ma d'in dan mitsili. Ya san abin da yake damun y'ayan amma sam sai ya basar, ya kalli sa'ad yace ya aka yi sa'adu ka samu kuwa ka tambayo adaidaitan?"
Sa'ad d'aga kai ya yi murya a dashe ya  ce "Eeh na tambayo Abba #950,00
Abba yace Masha Allah, to yanzu abinda za'ayi sabo za'a Siya guda d'aya a sayi tsoho d'aya. Idan ya so Kai ka ja saban tunda kai yaro ne nikuwa tsohon zanja"
Sa,ad yace Abba ai da kai ka ja sabon sabida kada tsohon ya wahalar da kai"
Abba ya ce "Babu komai ba abin da zai faru In sha Allah saii alheri" ya fad'a yana murmushi.
Khalil mi'kewa yayi kawai ya fita, Abba ya dubi sauran yace khalil zuciyar sa yau K'una take na san da yana da hali da ya cire mana wannan talaucin. Abin da nake so da ku kawai ku dage ku saka tsoron Allah a zuciyarku, ubangiji ya sa hakan shine mafi alkairi a tare damu, don wani kud'in ma masifa ne.
Umma ta ce,  "k'warai kuwa malam, Allah dai ya sa mufi k'arfin zuciyoyinmuu..."

Cikin dare khalil ya kasa rintsawa ya dinga ware ido yana kallon d'akin da ya kira akurki wanda suke k'untace sosai a cikin don Y.Mahmud ma sai a zauren gidan ya yi shimfid'a ya kwanta, kamar wanda aka mintsina ya yi saurin mi'kewa, jakar kayansa ya bud'e ya d'au kala biyu,sananan ya d'ebi takardun makarantarsa, daga haka ya samu doguwar takarda da biro ya fara rubuta:
Assalamualaikum
Iyayena yayana da k'annena,ina mai neman afuwa a gareku, wallahi zuciya ta ta kasa jure yanayin da muke ciki na tsananin talauci a kullum nakan yi kuka idan na tuna babu halin taimakonku,ga shi mun gama makaranta Amman babu aikin yi. Abin ya ta'azzara a zuciya ta a yau don sam na kasa rintsawa. Hakan ya sa zuciyata ta shawarce ni da na fita nema kawaii don Allah Abba da Umma ku yafeni idan na b'ata muku rai"

Daga haka ya ninke ya ajiye sadaf _sadaf ya mik'e ya bar d'akin mahamud yayansa ya tsallake daman k'ofar gidan sayawa aka yi . Saboda iska ta dinga shigarwa mahamud don haka khalil ya fice fit ba tare da sanin kowa ba.


Jikar Nashe ina godiya da adduoinku lafiya tana samuwa. Fatana mu yi aiki da alherin cikin littafin mu yi watsi da sharrin da ke cikinsa.

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now