Jin abinda tace yasa Hisham zare ido had'e da cewa, "kin san abin da kike cewa kuwa Fareeda?  amman dai ina so furuncin ki yazama gangan. don kuwa rana d'aya zan aure ku ku biyu."
Fareeda ta yi murmushi, lokaci d'aya kuma ta sha mur had'e da fad'in, "Bari Hisham a rayuwa ta ina son kowanne irin wasa amman ban da na kishiya."
Hisham ma ya gintse fuskarsa, kafin ya ce. "Da gaske nake fareeda, babu batun wasa rana d'aya zan aure ku ke da saudat......
 
"Dakata Hisham!! Wallahi indai har da gaske kake na hak'ura da aurenka ko kai ne autan maza....... Daga haka ta bud'e k'ofar mota ko waiwayonsa ba ta yi ba.
Zuciyarsa ta yi zafi, ya rintse idonsa yana fadin,"Oh God " menene mafita kuma?"

Fareeda tana shiga gida ta sakawa mahaifiyar ta kuka, hakan ya rud'a mamin tata, ta shiga tambayar ta dalilin kukanta.
Fareeda ta rattabo mata bayani.
Zuciyar mahaifiyarta ta  tunzira , ta ce  "share hawayan ki, shi d'in banza. ai wallahi ya yi kad'an ya wulak'anta ki  yanzu zan Yi waya gidansu na ji dalilin wananan tozarcin. naji.shin ,da saninsu ko babu?"
Wayarta ta D'auka ta danna lambar mahaifiyar Hisham, bugu d'aya Hajiya laraba ta d'auka.

Hajiya sa,a cikin kausshiyar murya ta ce "laraba Sak'on da ku ka turo Hisham da shi ya isar mana, sai dai ina so ki sani ban zauna da kishiya ba, d'iyarta baza ta yi kishi ba, don haka idan Hisham autan maza ne fareeda ta bar auren sa.......
Laraba ta zaro ido tace "Hajiya sa'a wallahi saurare ni don Allah, sam ba mu muka turo Hisham ba,kiyi hak'uri zan samu mahaifinsa da maganar."
Sam Hajiya sa'a ba ta saurare ta ba illa D'uf  data yi ta kashe wayar, cikin jin zafin Hajiya laraba
Ita kuwa Hajiya laraba tana ajiye wayar tagumi ta zuba tana tunanin irin asarar da Hisham ya ke Shirin janyo musu, amman kuwa tabbas zai zo ya same ta,ba ta yi kasa a gwiwa ba ta kira mahaifinasa ta sanar dashi abunda yake faruwa
Tsam mahaifinasa ya yi da ransa yace," barni da dan banxan yaro,zan dawo daga kadunan gobe _ gobe kuma sai na yi abinda saii ya gwammace bai ce yana son d'iyar Mustafa mai k'ashin tsiya ba daga haka ya Kashe wayar cikin matuk'ar zafin rai Ita ma hajiya laraban zurfin tunani ta afka tare da hasasho irin hukuncin da za ta yi wa zuriyar Mustafa ma'kurar basu k'yale Hisham ba. Ta zabga tsaki,ta rasa har yaushe ta yi sake da Hisham ya fara zuwa gidan Mustafa.

Ko da ya dawo da daddre sai da ya isa sashen sashen mahaifiyarsa don cin abincin dare, wani banzan kallo ta watso masa tare da shigewa D'akinta . Hakan ya tabbatar masa ta samu labarin abinda ya aikata a gidan su Fareeda, sai dai shi ko a jikinsa Allah yasa ma a fasa auren, sam ba shi da damuwa.

Kashegari Alhaji Hamza ya dawo ko zama bai yi ba ya danna kiran wayar Hisham, cikin sakin fuska ya amsa wayar tawa, Alhaji Hamza yace, "ka zo ina son ganin ka yanzu."
Daman yana cikin gidan,don haka babu bata lokaci yaxo, abban nasa da walwala fal a fuskarsa ya tare shi yana fadin angon mata biyu Hisham ya sunkuyar da kansa don yana zaton abban nasa gatse yake masa, ga mamakinsa sai yaji abban nasa yace,tashi muje gidan mustapha a tare na ji ba a yi wa yarinyar miji ba.

Cikin matuk'ar mamaki Hajiya laraba ta kalle shi had'e da cewa, "Alhaji daure masa gindi zaka yi? Ya d'an  d'aga mata hannu, "Ba ruwanki mustapha jininane, kuma ba zan k'i jinina ba saboda wani, muje Hisham."
Hisham kuwa dadi ne ya lullube shi ya ayyana a ransa Allah kenan,Al_hakimu dubi dai yardda cikin hikimarsa ya shirya mahaifinasa a rana daya lokacin daya wa ke da wannan ikon banda Allah.

A kofar gidan Abba mustapha Hisham yayi parking din motarsa cikin zakwadi da tsananin murna ya fito ya zira kansa cikin zauren gidan Abba mustapha,da fara'a fal a fuskarsa ya shigaa gidan sauda da take gefe tana yanka alaiyahu tayi saurin d'agawa ta haska shi da wadatattun idanunta cikin sakin murmushi.shima murmushi ya sakar mata, sananan ya ce" Abba na nan kuwa sauda?"

Ta d'aga kai cikin karassahin murya, yana nan yau gaba d'aya bai fita ba, saboda baya jin dad'i, Hisham ya ce  Ashsha Allah ya sauwake, ga shi da abbana muke ya xo ne a kan maganar auren mu umman tana ciki? Sauda ta d'aga kai tace "tana ciki bara nayi mata magana"
Kafin ta shigaa cikin d'akin Umma ta fito da fara'arta ta ce "Hisham ashe kai ne a tafe."
Durkusawa yayi ya gaishe ta, sannan ya sake gyran zamansa had'e da cewa "ashe abba bai ji dad'i ba?" Umma ta gyad'a kai tace. "Wallahi jikin nasa yau ya tashi babu dad'i, kasan abinka da mai ciwon hawan jini yau da lafiya gobe babu."
Hisham yace "haka ne daman Abbane yake son ganinsa yazo ne akan maganar mu da Sauda.
Umma ta gyad'a kai tace "To Allah yasa lafiya da fatan dai ba wata matsalar ba ce ta faru?" Hisham ya girgiza kai had'e da cewa "babu komai In sha Allah sai alheri. Ya xo ne su tattauna maganar auren."
Cikin farin ciki umma ta ce kai Masha Allahu bara nayi masa magana.

Daidai lokacin yayyen sauda suka shigo gaba d'ayansu,suka mimmik'a wa Hisham hannu. Abba ko da ba ya jin dad'i haka ya k'ok'arta ya fito, bayan Umma ta isar da sak'on ana son ganinsa
Cikin walwala ya fito yana duban dan Dan uwansa Alhaji Hamza, cikin sakakkiyar fuska yace, Hisham maza kace ya shigo mana, ya zaa bar shi a tsaye?"
Hisham ya juya shima cike da walwala.
Abba mustapha ya saka umma ta Malala tabarma a tsakar gidan, ya zauna ya jingina da bango don kam matuka da gaske ba ya jin dadin jikinsa.
Fuskar alhji hamza a hade ya shiga gidan yana karewa gidan kallo, da alamar raini k'arara a fuskarsa gaba d'aya jikinsu ya yi sanyi,amman hakan bai hana Abba mustapha yi masa tarbar mutunci ba, ya mik'a masa hannu had'e da yi masa iso kan tabarmar.

Alhaji Hamza bai ko dube shi ba, ya sake tamke fuska a karo na biyu, ya saki murmushin da kai tsaye za a iya kiransa na rainin hankali, ya kai dubansa kan Hisham,  "Allah wadaran naka ya lalace, yanzu Hisham duk tarin baiwar nasibin da Allah ya yi maka na katarin samun arxiki a nan kake so ka ce min kana neman aure? to me na sama ya ci balle ya bai wa na k'asa ya juya kan Mustafa yace, Ina so ka ji ni da kyau Mustafa babu Hisham babu y'arka, ban ga yarda had'in zai had'u ba, abin da hausawa suke cewa HAD'iN GAMBIZA kun ga yaro ya taso da arzikinsa kun bi kun makale masa saboda ku kassara shi. Wallahi d'ana yafi k'arfin ku me Hisham zai yi da jinin tsiya.idan ma kwad'ayin abin hannusa kuke bud'e kunnunwanka da kyau Hisham kaji daga yau ficikarka ta k'ara shigowa gidan nan Allah ya isa ban yafe ba,duk wahalar dana yi maka tun kana cikin Uwarka." Hisham dake gefe ya rintse idanunsa sai ga kwalla na tsiyaya.

Shi kuwa Abba mustapha murmushi ya saki, ya ce "duk me ya yi zafi haka? ina ganin idan har an yi abin a hankali, komai zai zo da sauki, Hisham dai d'an kane babu wanda zai yi maka iko dashi kana da ikon saka shi ka kuma hana shi da alfarmar annabi saudat dai ko ta rasa mijin aure ba zata aure shi ba sai dai ina so ka ja masa kunne shi ma babu shi babu ita..... 
Hisham ya girgiza kai yana duban mahaifinasa ya ce "Abba bai dace ba abinda ka yi, sam bai dace ba wallahi."
Wani kallo ya bi shi da shi kafin ya girgiza kai "ko d'aya ban yi mamakin furucinka ba nasan ba haka aka barka ba, sai dai ina so ka sani, ko dame mustapha yake takama wallahi na fi shi, mu zuba ni da shi shege ka fasa. Hisham ya sake bud'e baki ya ce Abba....

Ya Harare shi " mutumin banza nuna min matsayitan mutane sun fi ni a wajen ka. Wallahi idan ba ka yi da gaske ba sai na tsine maka akan wad'annan matsiyatan tashi ka fice mu tafi, kuma ka kaddara ka yi wa gidan nan kallon karshe,don ko da wasa ka tako kafarka zuwa gidan nan wallahi ba zan yafe maka ba."
Cikin tashin hankali Hisham ya mik'e ya fice yana bin bayansa Yana sake jaddada, "Matsiyata kawai"
Suna fita umman sauda ta bi bayansu ta shige d'akin mijinta. Sauda kuwa hawaye kawai take. mahamud ya dube ta yana girgixa kai a zuciyar sa yana ayyana tabbas talauci bai yi ba . A hankali ya ce saudat ki yi shiru, Abu d'aya za kiyi ki cire soyayyar Hisham daga ranki . ki bawa mahaifinsa kunya shi ne ki ka cika 'ya'."

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now