Umma ce ta d'aga labilan d'aki na na ga ta jijjiga kai kafin ta ce "Y'ar banza mai taurin kan tsiya, zuciya kamar ta mutanen farko, sam babu lislama a zuciyarki, wallahi idan ba ki jingine wannan bak'in halin naki ba tsaf zan jingine lamarinki a gefe, ko kuma na samu wani a dangin na ba shi auren ki, sai na ga ya za kiyi shashashar banza mutuniyar kawai."

Da sauri na zaro ido na ce "Wallahi kuwa Umma da na kashe kai na..."

"Kashe kanki? Kin san kuwa furucin da bakinki yake furtawa? Me kika d'au duniya ne? To Allah ya kyauta ya yi mana maganin masifa lamarinki kuma sai addu'a tabbas." Daga haka ta saki labilan ta juya ta fice daga d'akin tana sake jinjina kai. Na tabbata mamakin furucina take ni kuwa Iya zallar abinda yake raina na fad'a, Gaskiyar kenan, saboda yarda nake sake jin tsanar dangina a zuciyata. Kwatankwacin k'iyayyar rai da mutuwa. Me zan yi da mutanen da basa kallon iyayena da k'ima da martaba.

*************
Ba kowa a gidan ni kad'ai ce, hakan ya bani damar sakewa Abuna, ina ta wak'e-wak'ena da raye-raye na, na ware wak'a a radio mai Bluetooth, Yau kam da farin ciki na tashi zuciyata fresh na ke jinta tamkar ta yaran da ba su wuce shekara uku a duniya ba, saboda yanayin yarda nake tsalle-tsalle na. Har igiya na samu ina y'ar tsalle bayan na gama gyaran gidan tas na d'ora abincin dare tuwon shinkafa ne miyar zogale. Kasancewar gawayi ne ba ci yake sosai ba, ya sa nake ta tsallen y'ar igiya. Sam ban san da mutum a tsaye a bakin k'ofa ba, ina juyowa na yi arba da shi yayi holding hannayensa a k'irji. Sanye yake cikin farar shadda gezner da ta sha aikin brown d'in zare. Da sauri na had'e rai don sam ban san dalilin zaryar da yake yi gidanmu ba. Ba ya kwana biyu bai zo ba. To yau dai mutanen gidan basa nan, na ga da wanda zai yi hirar tasa. Na raya hakan a zuciyata.

Ban sake kallonsa Ba an burma kaina cikin d'akin. Ina jin takun takalmansa a tsakar gida ban yi aune ba na ga ya d'aga labulen d'akina. Ya kuma zuba min tsumammun idanunsa da suke lumshewa da kansu ko kuma iyayinsa ne oho. Don na lura hakan kamar ya zame masa al'ada, ko naturally haka yake oho masa.

"Ke, ya ma sunanki? Mutanen gidan ba Sa nan ne?"

Duban cikin tsakiyar ido na yi masa jin ya ce bai san ma sunana ba. Na lura k'warai mutumin d'an rainin hankali ne. Na gyara zamana sosai, na kuma sake bud'e littafina ina karantawa ba tare da na sake masa magana ba.

"Ba kya ji ne?" Wannan karan muryarsa a kaurare ya yi magana. Na lura kamar ma a kufule yake. Na d'an tab'e bakina cike da tsiwa na ce "Kai baka lura ba?"

Sake harzuk'a ya yi ya ce. "Idan na luran ai Ba Zan tambayeki ba, ke me yasa ba ki da kunya ne? Wallahi za ki gane kurenki idan ki ka k'ure malejin hak'urina." Ya fad'a yana murza yatsun hannunsa. Sannan ya fice.

A harzuk'en nima na ce "Babu abinda kurarinka zai yi min." Na tabbata kuma ya ji ni ban damu Ba sam don burina ya fita sabgata.

Ko da Umma ta dawo ban sanar da ita da zuwansa ba don na ma manta da babinsa.

Bai sake dawowa gidanmu ba sai bayan kwana biyu. Ranar ma ba kowa ni kad'aice a gidan. Ummana haihuwa aka yi mata take suntirin zuwa gidan mai haihuwar, k'anwarta ce ta haihu. Ina wanke-wanke ya shigo, sam ba ni da juriyar aiki duk da aikin gidan namu ba wani yawa bane da shi amma yana gajiyar da ni, kasancewata mace mai son jiki.

D'akin Umma ciki da rumfa ne, su ma ba wasu manya ba bane, sai fallen d'aki d'aya da ya zama mallakina da kichin da band'aki a can gefen tsakar gidanmu. Sai k'aramin d'akin su Yaya Khalil da yake zauren gidan. Sai soro d'aya jal shima k'arami.
Tsakargidan malale yake da fasassun tile wannan dalilin yasa kullum sai an wankeshi. Sabida Umma na mace mai matuk'ar tsafta.

Riga ce a jikina brown colour, sai bak'in siket gashina kuwa a ranar raba shi biyi na yi na tufke shi gefe da gefe, kamar wata yarinya ya kuwa sauka a saman kafad'una kasancewata mai yalwar gashi ina kuma matuk'ar son gyara shi.

K'amshin mayataccen turarensa da ya bad'e tsakargidanmu ne ya sanar da ni zuwansa. Don haka na had'e rai na juya da sauri shi d'in kuwa na gani a tsaye yana k'are min kallo sama da k'asa. Haushin kaina ya kamani da kuma yanayin shigar da take jikina. Ya yi kyau Ba kad'an ba don shigar bak'ak'en kaya ya yi na english wears da suka sake haske masa farar fatar jikinsa.

Daga kallo d'aya da na masa na had'e rai, shi d'in ma bai Yi min magana ba can gefen tsakar gidan ya nemi waje ya zauna. Tsawon mintuna yana daddanna wayarsa a hannunsa ba tare da ya yi min magana ba. Sai can ya wurgo min tambaya "Ke Yau ma Umma bata nan ne?" Kamar da iska yake magana haka na sake d'auke kai na zumb'ura baki kawai na shige d'akin girki.

A k'ufule na ga ya taso ya tsaya a k'ofar kitchen d'in. Shi d'inma kallon banzan ya wurga min kafin ya ciji bakinsa ya ce "Ke wai me ki ka d'au duniya ne da kike wulak'anta mutane? Kin san kuwa illar wulak'anta d'an Adam?

Na sake watso masa manyan Idanuna kamar na ce masa "A je a tambayi tsoho wato mahaifinsa, sai dai na ja bakina na had'iye maganar ba tare da ba bashi amsa ba, na cigaba da iza wutar gawayi na. Daga baya ma sai na mik'e na rab'a ta gefensa na shige uwar d'aka.

Ina jin takun takalminsa alamar ya fita daga gidan na saki tsaki a bayyane na ce "Ka ji min kinibibi uban wa za ka yi wa wa'azi, aje a yiwa magabata su suka fi cancanta ba ni ba."

Sallamar yara ce ta sa da sauri na mik'e na d'aga labulen ina fad'in wanene nan? Yara na gani d'auke da kayan abinci suna jibgewa a tsakar gidanmu. "Kai ku tsaya wannan kayan daga ina?" Na fad'a cike da mamaki don Abincin yau ma auno shi mu kayi a kantin iliya.

Ba su ba ni amsa ba na jiyo sallamrsa ya shigo hakan yasa na ja bakina na tsuke don na fahimci daga inda kayan suke.

Umarni ya bawa yaran akan su sauke kayayyakin a can gefe daga haka ya juya ya fice. Ina jiyo tashin motarsa alamar ya tafi. Na bi kayan da kallo don kaya ne aka jibge masu yawan gaske kamar za mu bud'e shago. Komai biyar taliya shinkafa macaroni kuskus semovita, golden vita, indomie. Sai su maggi da dangin kayan shayi rankatakaf. Har da sabulu da omo. Na tab'e baki jiki a sanyaye na shige d'aki. Tabbas na ji kunyar rashin mutuncin da na gama yi masa shi kuma ya bi iyayena da alheri.

Jikar Nashe taku ce✍🏽✍🏽

❤️❤️❤️❤️❤️🙏

Zumuncin ZamaniOnde as histórias ganham vida. Descobre agora