PART 6

10 1 0
                                    

🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*@GWANDOU.*

_©2022._

                 *DENA KULANI.*

'''DEDICATED TO MOMMAH......'''

_BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM._

Page.6
•••Zaune take a gefen gadon Khadijah..wayar aunty munaya ce a hannun ta yayin da take duba hotunan ɗaya bayan ɗaya...cikin hakan ne Khadijah ta fito ta sameta.."me kike dubawa ne hakan" faɗar Khadijah tana mai ƙarasawa gaban madubi dan kimtsa jikin ta.
Me nake dubawa kuwa bayan kayan da sarauniyar yayah Hisham zata saka lokacin biki,ta ƙarashe faɗa cikin sanyin nan nata murmushi kwance saman fuskar ta..babu zato taji tsayuwar mutum saman kanta tamkar zasu kifu.. lemme see it dear Khadijah tafaɗa tana mai karɓar wayar daga hannun oum.
Pictures ɗin tashiga dubawa ɗaya bayan ɗaya..dogayen riguna ne ƴan ubansu na yayi..waɗanda kallo ɗaya zaka musu kagane cewar anyi sune kawai domin amare.
Wow! Salmah wacce kike ganin tadace naɗauka aciki ta ƙara sa faɗa tana mai kaiwa zaune a gefen gadon kusa da salmah.
Dariyar da Oum ke ƙunshewa ce tafito..ai kuwa tashiga yin kayanta har tana mai kaiwa kwance saman gadon..ɓata fuska Khadijah tayi tare da kaimata duka a baya.. sannan tace"ke nifa banason tsiya salmah daga tambaya sai kuma kimin wani fassara ta ƙarashe faɗa cikin alamun son yin kuka..saurin ɗagowa salmah tayi tare da ɗaga hannuwa alamar surrender..haɗi da faɗar"yi haƙuri Allah na daina..muga wacce kikeso aciki..tafaɗa tana mai matsowa kusa da'ita.. "gayamun me kikewa dariya"faɗar Khadijah..haba ƙawata mene kuma abun fushi kawai dai naga keda kike kuka bakyaso amma kuma gashi yanxu har kin ware kina neman zabar wedding dress...but kiyi haƙuri Allah nadaina kinji ta yayanta..ajiye wayar Khadijah tayi tare faɗar to nama fasa..miƙewa tayi tare da fara shirinta..dafe kaii salmah tayi haɗi da faɗar ohh ni kaina ɗiyar babban mu......

             BAYAN SATI BIYU.

....Shirye-shiryen buɗe makarantar da Alƙasim keyi ya kankama..dan kuwa a kwanakin nan sam baya samun zama.. kullum da abunda za'a kawo ko kuma anemeshi dan duba wasu abubuwan..tun yana ɗaukar abin kamar wasa har ya gane cewa abin babbane..dan kuwa makarantar ba ƙaramar makaranta bace duk da kasancewar makarantar bata tara wasu courses masu yawa ba,amma kuma gininta da komai nata shine zai tabbatar maka da ba ƙaramar makaranta bace.. makarantar ta ƙunshi fannin lafiya da sauransu..sai yanzu ne yake gane zallar wayon da Muhammad yayi mishi..
Nannauyan numfashi ya sauke tare da jingine bayansa ga kujerar da yake zaune haɗi da furta"Finally.." dariya Jalal ya saki tare da furta"ai Muhammad ne dai-dai dakai..da yanxu mun nemeka mun rasa..but yanzu gashi ka zauna guri ɗaya..tsaki ƙasim yaja haɗi da shafa gefen fuskar shi sannan yace"bari kawai Jalal ai haɗuwa ta dashi bazata yi kyau ba..dan wannan wahalar sai shi tunda shine yajiyo,kuma yaji zai iya..kawai dai nayi iya abinda zan iya..koshi fa acikin taimakon sa, dan kasanni Allah abubuwan sunmin yawa.."ai kuwa dai daka kammala..meya rage haba mann"..idanuwa alƙasim ya buɗe tare da watsa su akan Jalal tare da kafeshi dasu"amma Jalal bakada tausayi..tunda na dawo ƙasar nan dai-dai da rana ɗaya bantaɓa baccin kirki ba saboda wannan aikin..a haka zaka wani ce naƙarasa?..to naƙi Allah duk abinda ban ƙarasa ba daga baya idan ya dawo yaje ya ƙarasa da kanshi..na gaji.. dariya Jalal ya saki tare da furta raggo kawai anya kuwa ƙasim.. menene ɗan iska nifa nan dakagan Ni bana cike da iskanci Tau yayi.

"Sorry i come in peace!,..yanzu dai ya Hajarr ɗinka..ananan tare kuwa kodai kayi mata halin ƴan zamani"
tambayar da Jalal ya jefowa Alƙasim kenan.. murmushi ne ya suɓucewa ƙasim.. jujjuya kujerar da yake kai ya fara cike da nishaɗi..tananan lafiya..kawai dai muna kewar juna dani da'ita..kallon shi Jalal yayi tare da buga table ɗin da ke gabansa haɗi da faɗar "shegen dawah ashe baka manta da ajiyar kaba"..ka taɓa ganin inda mutum ya manta kansa..karfa ka manta nida ita ƙaddara tasaka munzama ɗaya,..so..ako ina nake ina jinta ne acikin raina..maganar da Jalal ya jefo masa itace sanadiyyar komawar shi jikin kujera yayi kwanciyar shi.."tambayar kafa nake amma kamin banza..da gaske ne abinda naji ko kuwa".."gaske ne mana kawai dai share da zancen Ni a ganina bayada wani amfani.. jinjina kai Jalal yayi haɗi da faɗar "Fadeelah Galau"... shiru sukayi na wasu sakanni kafin Jalal ya ƙatse shirun ta hanyar cewa"but ina ganin wannan ba komai bane kayi accepting kawai daga baya sai kashigo da zaɓin ka..ina ganin hakan zaifi"
Numfashi alƙasim ya sauke haɗi da faɗar..yeah Nima nayi tunanin hakan shine babban dalilin da yasa na amince da wannan haɗin,..kawai dai yanxu babbar matsalata mommy..Dan nasan bazata taɓa bari na aure hajarr ba tunda take ƴar talakawa..
"No karka saka Wannan aranka insha Allah zaku satanta da'ita.."Allah yasa"
••••••
"Haba dear, nifa sonake taje can Paris tayi degree ɗinta na farko..ɗan saurarawa tayi da alama wanda suke wayar ne keyin magana..a'ah taya za'ayi nace ban yarda da ingancin taka ba..kawai dai gani nake kamar can zatafi zama kurum.. Tau yayi Allah yayi maka albarka...wait..wait tell me..yaushe zaka dawo..ta ƙarasa faɗa cikin taushin murya..no bazan yarda dakai ba..kayimin alƙawari kawai.. Numfashi ta sauke haɗi da faɗa" Muhammad kodai ka yafemu ne a matsayin dangi..kodai mace ta janye maka ra'ayi ne acan..bansan meya faɗa mata ba naga tana jinjina kai tare da faɗar"promise me baza ayi auren alƙasim baka kasar nan ba?..Tau yayi Son! Take care of yourself too..

"Mommy's boy" faɗar hajjo tana mai cigaba da using da wayar ta.. numfashi mommy ta sauke tare da faɗar"kinsan halin ƙanin naki hukuma ne..haka kawai fa yakirani yana gayamun wai ya bawa Ameerah admission a makarantar shi nida nake preparations ɗin nema mata makaranta a Paris..sai gashi kawai ya canza min plan..kuma nasan wannan duk aikin ƙasim ne.
"Kibari taje can kawai tunda yanemi hakan..amma koni bazanso tayi karatu anan ba gaskiya..but tunda ya buƙace hakan itama tanaso..just allow them.

Ameerah ce tashigo falon hannun ta riƙe dana El-herm wacce ta kasance kamar itace ta haifeta dan ko wanne lokaci idan  yarinyar ta dawo daga schools ɗinta muddin ameerah na gidan zaka tarar dasu atare..saboda babu wani shaƙuwa tsakanin ta da mahaifiyarta kasancewar bata samun lokacin zama,.. yanxu haka daga gidan granny suka fito dawowar su kenan..
Ƙarasowa sukayi cikin falon..dai dai nan ne kuma ameerah ta saki hannun El-herm tana mai zama ɗaya daga cikin kujerin parlourn haɗi da fadar "waiii."
Ƙasawa El-herm tayi gun mahaifiyar ta haɗi da shigewa cikin jikinta batare da tace komai ba..shafa kanta mommy tayi tare da furta my Elee meyasa kikeson bin ameerah yawo ne..gashi duk ta wahalar dake da wannan sanyin.. ɗagowa mommy tayi tare da faɗar"meyasa baki saka mata jacket a sama ba da zaki fita da'ita..bayan kuma kinsan yanzu hunturu ya shigo..ɗagowa ameerah tayi daga kallon wayar da takeyi haɗi da ɓata fuska cikin sakalci wanda idan ma baka sani ba zaka ɗauka itace a matsayin El-herm"to nifa mommy bani na nemeta ba..kuma har nashiga mota ta sameni tace zata bini Kinga a sama tazomin tam"
.a.a ba'a sama tazo miki ba a tsaka.. Allah ameerah yawon nan yayi miki yawa kodan Kinga na zuba maki ido ne.
Tashi tayi tare da fara tattare kayan ta dan barin parlourn tana mai gunguni
Ɗagowa yayaah Hajjo tayi wadda tunda suka fara wannan muhawarar take sauraren su batare da tace ƙala ba" Allah ameerah idan nasame ki agunnan sai kingane ke ƙaramar marar kunya ce..baki ta tura gaba tareda ƙarasa tattare yanata yanata ta fara tafiya domin barin parlourn"zonan ameerah "faɗar mommy tana mai tamke fuska..
tafiya taci gaba dayi tayi tamkar bata jita ba.
ganin yanda ta shareta taci gaba da tafiya ne yasa mommy furta "Muhammad ya samar miki makaranta"jin hakan shine dalilin da yasa taja birki da sauri haɗi da saurin juyowa ƴaƴan cikin ta na murɗawa..cigaba mommy tayi da magana"ehhh! Dubeni da kyau zaku fara taking lectures next week insha Allah dan haka kizama cikin shiri..yawwa inaji ma kamar a hostel zaki zaune..katse mommy tayi ta hanyar furta whatt d......

  #GWANDOU.
🩸🩸🩸🩸🩸🩸

DENA KULANIWhere stories live. Discover now