PART 4

5 1 0
                                    

🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*@GWANDOU..1*
_©2022._

*DENA KULANI.*

'''DEDICATED TO MOMMAH..'''

_BISSIMILLAHIR RAHMANIR EAHEEM._
_page.4_

••••Mayarda kallon shi yayi gefen da Umma take tsaye..kamar wadda aka dasa agun,janye jikin shi yayi daga gun Oum-salmah yana mai sakin sanyayyen murmushi..tare da faɗar" Hajiya A'isha ya naga kin tsaya daga can,..ƙaraso manah.
Ya ƙarashe faɗa yana mai miƙa mata hannu alamun tazo..Barka da dawowa tafaɗa tana mai tunkaro dining area ɗin..yawwa na sameku lafiya..alhmdllh! "Masha Allah!"Abba ya faɗa dai-dai lokacin da take gota shi..mug ɗin dake hannun ta ta ajiye saman dining sannan tadawo daga baya.. dai-dai gunda yake tsaye taja mishi kujera haɗi da faɗar "Bismillah!.
Murmushi Abba ya ƙara saki tare da ɗaura hannun shi saman nata..ɗan ɗagowa tayi tare da duban shi,idan da sabo tasaba da wannan a duk lokacin da yakeson gaya mata wata muhimmiyar magana Musamman wadda ta shafe rayuwar su...a gaban kowa zai iya riƙe hannun ta, wannan ɗabi'ar kuwa ta samo asali ne tun ƙuruciya..a lokacin da suka kasance ma'aurata.

A'ishahh! Ya faɗa cikin sanyayyen lafazi...na'am!..ta amsa mishi haɗi da zama kujerar dake gefen damanshi.
Juyawa Oum-salmah tayi tare da ƙoƙarin barin dining area ɗin.."dawo nan" Abba yafaɗa yana mai yi mata nuni da kujerar dake facing ɗin shi.
Mayarda kallon shi yayi gun Ummah sannan yaci gaba da faɗar"ɗazu Principal ɗin su take sanar dani wani labari..ta faɗa min cewa oum-salmah tana ɗaya daga cikin ɗaliban su biyu da suka samu sakamakon jarabawa mai kyau.. kuma mai wuyar samu.. to a kwanakin baya kuma an kawo musu wasu forms na manya..kuma sabbin universities biyu da za'a buɗe acikin wannan watan.
Dan haka sunanta ya shiga cikin ɗaliban da suka samu scholarships a wannan shekarar...
Masha Allah!..Ummah ta faɗa fuskanta ɗauke da murmushi..cigaba Abba yayi da magana"shine nace yakamata nayi saurin sanar dake saboda ke uwace kuma kinada babban haƙƙi akanta.. numfashi ta sauke sannan tace"banida wata matsala ko damuwa da duk abinda zaka yanke akan oum-salmah,.. saboda nasan bazaka taɓa nema mata abunda zai cutar da'ita ba.
Mayarda kallon shi yayi gun Oum-salmah wadda kallo ɗaya zaka mata kagane cewar jikinta a sanyaye yake.
Oum!yafaɗa yana mai kafe ta da idanunsa...na'am Abba..naga result yayi kyau.. Ubangiji ya sanya alkhairi..da Ameen ta amsa tana mai duƙar da kanta.
Cigaba yayi da faɗar"kinji maganar da mukeyi da Ummanki ko?..ehh! Abba..jinjina kai yayi tare da faɗar"Masha Allah"..yanzu haka malaman ku suna jira ne suji bayani daga bakin mu..idan mun yarda ko akasin hakan.
Shiru yayi tare da tsura mata ido yana jiran jinta bakinta...cikin in..ina ta fara faɗar"Uhm!! Duk abinda kuka yanke kaina shine dai-dai..banida kamar ku a duk duniya,..kuma duk abinda zakumin aduniyar nan nasan bazai taɓa cutar dani ba.

Murmushi suka sake a tare..dai dai kuma lokacin ne yayaah Abdul yayi sallamah..a tare suka amsa masa fuskokin su ɗauke da fara'a..."Barkan ku da dare Abba"ya ƙarasa faɗa yana mai zama ɗaya daga cikin kujerin dining table..."yawwa Barka Dr"Abba ya faɗa yana amsa hannun da Abdul ke miƙa mishi da nufin suyi musabaha.
"Babban yaya kazo a dai-dai lokacin da ya dace"Abba ya faɗa..bayani yamishi akan maganar da suke kan tattaunawa,..wow! Juyawa yaah Abdul yayi gun Oum-salmah haɗi da miƙa mata hannu..congrat sister..saka fuskanta tayi acikin tafukan hannayen ta alamun jin kunya.
Dariya suka saka mata gaba ɗayansu.
Zaro waya Abba yayi daga cikin aljihun shi haɗi da faɗar" Principal ɗinku ma ta turomin sunayen schools ɗin..gobe takeso tacika miki komai dan Zuwa wani month zaku fara karatu insha Allah.
_1.THE FEDERAL UNIVERSITY OF TECHNOLOGY OWERRI(FUDO) IN IMO STATE._

_2.M.A SHAMS INTERNATIONAL UNIVERSITY ABUJA._

WOW!faɗar Abdul yana mai tafawa.
"Sai ki zaɓi ɗaya acikin su"faɗar Abba yana mai ajiye wayar shi saman dining table ɗin.
Ɗago kai tayi tare da tsurawa Ummah ido..tare da ɓata fuska cikin nuna rashin sanin abinyi.
"A'a ba ruwana ga yayanki agefen ki"
Faɗar Ummah tanaai ɗaya hannuwa sama..kallon ta mayar gun yayaah Abdul.."no sister kirufe idanuwan ki kawai sai kibarwa zuciyar ki zaɓi" faɗar abdull yana mai ƙoƙarin janyo plate daga gefe.
Shiru tayi ganin yanda kowanne daga cikinsu ya mayarda hankalin shi gurin cin abinci.
Rufe idanunta tayi tare da fara tunanin abunda ya dace..tuno Khadijah da tayi shine dalilin da yasa tayi saurin buɗe idanuwanta..karaff! Kuwa suka haɗa ido da Abba.."kin yanke hukuncin ne?..itace tambayar da Abba ya jefo mata..jijjiga kai tayi alamun A'a.. sannan tace"Abba Khadijah fah.. cokalin dake hannunsa ya ajiye haɗi da faɗar"yawwa kingama kin tunamin wallahi, juyawa yayi gun Ummah tare da faɗar"ɗazu baban Khadijah yake sanar dani an tsayar mata da miji...kuma bikin bazai ɗauki tsayin lokaci ba..duka-duka idan sun sami yanda suke so bikin bazai wuce wata biyar ba.
Ido oum-salmah ta fitar waje..yayin da Ummah ta furta "Masha Allah.. ai kuwa ɗazun nan take gidan nan fah.
Mayarda kallon ta tayi gun Oum-salmah haɗi da faɗar meyasa baki gayamun zancen auren ba..Nima fa ɗazu take gayamun..amma kuma tacemin tunda tace bata tashi ba ba lallai ne ayishi yanxu ba.."ehhh!kam tunda itace ta haifi kanta ba"...faɗar Ummah tana mai hararar oum-salmah.
Murmushi Abba yayi tare da faɗar"ai dole tayi haƙuri tunda ɗan uwanta ne ko ba shine yake aiki ƙasar Italy ba?..ehhh! Shine faɗar oum-salmah cikin sanyi.
"Tau saura ke sister, Allah ya nuna muna naki..da Ameen Abba ya amsa mishi sannan yace"kai kuma fah"..dariya Abdul ya saka tare da faɗar"very soon insha Allah" baki Ummah ta sake yayin da Abba ya saki murmushi haɗi da jijjiga kai..saurin miƙewa yayi tsaye cikin sassarfa ya shiga taku dan barin dining area ɗin..haɗi da faɗar" Sister kawai ki zaɓi M.A shams saboda akwai tsammanin samun tsaftataccen ilimi da kuma tsaro.. sannan kuma zuciya ta da hankalina sunfi gamsuwa dacan ɗin.
Tun lokacin da yace M.A shams taji gaban ta yayi wata irin faɗuwa kamar zuciyar ta zata fito fili taji har zuwa lokacin da yakai ƙarshen zancen sa.
"Kin amince da shawarar yayanki"ta tsinkayo Muryar Abba yana mai jefa mata tambaya.

Da ehhh! Ta amsa masa.. sannan ta ɗauki cokali dan fara cin abinci.....

~~~~🩸🩸🩸~~~~
Haba my excellency! Taya zan yarda da abinda ya faɗa...shine fa yake da wannan makarantar...amma yace bazai dawo bikin ɓudata ba sai-dai ɗan uwansa ya wakilce shi..numfasawa tayi sannan cikin sassauta murya taci gaba da faɗar"karfa ka manta yanzu kusan fa 5years yaron nan yabar ƙasar nan amma har yau ko take bale leƙe.. wannan wanne irin abune.
"Ki kwantar da hankalinki na'eemah Muhammad fah ba yaro bane yasan abinda keyi mishi ciwo sannan kuma yasan dai-dai da akasin hakan..to meye na wani damuwa bafa rasa shi mukayi ba yananan a raye kuma komai daren daɗewa dole ya dawo gida..nasan har yau fushi yakeyi amma haka dole zai haƙura dan abinda yake nema bamai yiyuwa bane.
Amma excellency kana ganin hak..ɗaga mata hannu yayi tare da faɗar"maganan ya wuce..karki manta su biyu kawai Allah ya bani ƴaƴa maza...haka kuma Allah ya bani dukiyar da dole saida taimakon su komai zai tafi dai-dai..dan haka abinda nakeso kawai ki ƙyaleshi zan san abunyi.."Tau yayi" Hajiya na'eemah ta faɗa tana mai sauke numfashi haɗi da faɗar "to maganar ƴar gidan Hashim Galau fah..mun fara magana banji ka sake cewa komai akai ba...ɗago kai ambassador Abdullahi yayi cikin ko in kula wadda kusan kaff! shi Muhammad ya gado ba ragi sai-dai ƙari.
Duban ta yayi tare da cewa nayi magana dasu Tanimu..kuma zanyi magana dashi Hashim Galau ɗin dan mutsayar da ranar da zamuje tambaya.
Washe baki mommy tayi tare da faɗar dakan yafi dan mahaifiyar ta ta dameni wallahi.. jinjina kai daddy yayi tareda cigaba da aikin da yakeyi da laptop ɗin dake gabanshi.

Al-ƙasim dake tsaye tun lokacin da yaji mahaifiyar shi ta kawo zancen auren da takeson ƙaƙaba mishi ne ya rufe ido..ba komai ya kawo shi sashen na mahaifinsa ba sai kiran gaggawar da yayi mishi..dunƙule hannun shi yayi tare da furta"mommm!....

*#GWANDOU.*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸

DENA KULANIWhere stories live. Discover now