PART 5

5 1 0
                                    

🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*@GWANDOU.*

_©2022._

                 *DENA KULANI.*

'''DEDICATED TO MOMMAH......'''

_BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM._

_Page.5_

~~~Zaune yake a ɗaya daga cikin kujerin parlourn yayin da daddy ke zaune a gefe har lokacin yana aiki..ka sake yin magana da Muhammad?.. tambayar da daddy ya jefo masa itace ta mayar dashi daga duniyar da ya faɗa.
"Ehhh! Dad.."ya canza shawarar ne"?faɗar dad Yana mai ɗagowa daga aikin da yakeyi..no..yanxu haka ya turomin bayanin komai da ya shafe makarantar..idan nasamu dama zuwa next two weeks za'ayi bikin buɗata.. jinjina kai daddy yayi tareda faɗar"ok..kayi ƙoƙarin yin duk abinda ya dace.."insha Allah"faɗar ƙasim..cigaba sukayi da tattaunawa akan yadda abubuwa zasu kasance.
•••••
Tsaye take jikin motar ta..yayinda hankalin ta kacokan yake gun wayar ta..fita takeson yi tasha iska amma tarasa ina zata nufa..yau batajin zuwa gidan Hajjo(granny) dan kusan kullum sai taje kuma sometimes da faɗa suke rabuwa..sai yanzu ne take jin ciwo da kuma kewar ƙawaye..a faɗin ƙasar nan batada wata ƙawa wadda zata nuna da sunan Tata..tsaki ta ƙaraja a karo naba adadi..ranki ya daɗe da akwai abunda za'ayi miki ne?..maganar Na Manzo ce ta mayar da'ita daga dogon nazarin da tafaɗa.
Hannu ta ɗaga masa haɗi da faɗar"no jeka kawai..bana buƙatar komai..a huta lafiya ya faɗa yana mai gota ta.
Juyawa tayi da nufin komawa cikin gida..buɗe gate da kuma horn ɗin da akayi a lokaci guda be yasata ɗan sassauta tafiyar da takeyi..ganin motocin dake shigowa ne yasa taɗan ja tsaki tare da faɗar"mai baƙin yawo"... Shema'u ce ta fito acikin ɗaya daga cikin motocin..yayin da wata housemaid take riƙe da jakar ta..takowa takeyi a hankali..yayinda kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar girman kai ya zauna agurin.
Ƙarasowar su gurin Ameerah ne yasa sukaja birki.."ke kuma fah..ina zakije yanzu da safen nan"?
..harara ameerah ta watsa mata tare da faɗar"kedai da kike da aure ba'a miki wannan tambayar ba saini da banada nauyin kowa akaina..ehhh! Nima ina da dalilin fitowar..marar kunya.."ba wani rashin kunya sai gaskiya"ta ƙarashe faɗa tare da cigaba da tafiya.
Harara shemaah tabi bayan ta dashi tare da cigaba da tafiya dan ƙarasawa cikin gidan.
••••
Zaune suke acikin parlourn yayinda kowanne daga cikinsu yake using da wayar shi.
Hajjo ce ta ɗago daga gurin da take zaune tare da ƙara sawa gefen mommy..tare da cewa"Mommy duba kigani waɗan nan sune videos ɗin bikin engaged na ɗan  gidan prof.Buba Tanko...karɓar wayar mommy tayi yayin da hajjo taci gaba da nuna mata mabanbantan videos na bikin ƴaƴan manya.
Miƙa mata wayar tayi bayan ta ƙarasa gani sannan tace"ki manta da waɗannan..dole zamuyi ƙoƙarin ganin munyi abunda zai jawo hankalin duniya kacokan akan mu..so nake bikin saka ranar alƙasim ta zama kaff! Acikin wannan shekarar ita kaɗai ce abar nunawa a kafafen sada zumunta..karki manta ko yanxu inada ƴaƴan da nake burin su samu ƴaƴan hamshaƙan masu kuɗi na duniya,..idan har wannan shagalin ya tafi yanda nakeso babu shakka ba Muhammad kaɗai ba har ameerah zata samu zaɓin da nakeso daga nan kuwa har ƙasashen ƙetare.
"Yawwa..yaaya duba wannan kigani yayi"faɗar shemaah tana miƙawa Hajjo wayarta..wani haɗaɗɗen leshi ne ruwan toka wanda ya ƙawatu da manya da ƙananan beat-beat masu ƙyalƙyali..wow! Gaskiya yayi na wacce ƙasane..na ƙasar Thailand ne..a kwanakin nan zamuje can shiyasa na fara duba kayakin ta online kafin naje can na ƙarasa sauran.
"Da wannan cikin dake jikin ki zakije har Thailand Shema'u..anya kuwa kinsan ciwon kanki..faɗar mommy tana mai kallon shemaah cikin sigar mamaki..to mommy ai tafiyar ta zama dole ne,dan nagaji da wannan ƙasar kusan fa wata biyar banje ko ina ba..then.. barrister Yanada wani aikin da yake so yayi acan..ga kuma siyayyar da nakeso nayo na wannan engaged partyn da za'ayi.
"Tsawon wanne lokaci zaku ɗauka acan?Hajjo ta jefo mata tambaya..bazan ɗauki tsayin lokaci ba gaskiya dan duka-duka bazan wuce 1 month ba..taɓe baki mommy tayi haɗi da faɗar"wahalar dai kikeso..juyawa tayi gun hajjo taci gaba da faɗar"kince kinyi magana da companyn Angels ko?..ehhh! Mommy da kuma intelligent mall na ƙasar London insha Allah kayan zasu kammala nan da ƙarshen watannan.."ok hakan ma yayi..kiran da ya shigo wayar mommy ne ya katse ta daga maganar da tasoyi..ɗaukar wayar tayi yayin da Shemaah da Hajjo sukaci gaba da duba abubuwan da suke buƙata.
~~~~
Ya kamata kibar kukan nan haka Khadijah..duba fah Nima har kin sakani kuka.. oum-salmah ta ƙara sa magana cikin Muryar dake nuna alamar cewa zuciyar ta a karye take.
Ɗago kai Khadijah tayi daga kwancen da take.. jikinta ta jingina a daidai kan gado..ci gaba tayi da share hawajen ta..cigaba Salmah tayi da faɗar"ya kamata kigane cewa fah su mommah bazasu taɓa zaɓa maki abinda zai cutar dake ba..You know ,I know yayaah Hisham bazai taɓa cutar dake ba..yanason ki haka kema You love him too..so meyasa zaki tsaya ɓata hawaye ki..nasan bafa zakiyi farin ciki yau ace anfasa auren ki dashi ba yaje ya aure wata..saurin ɗagowa Khadijah tayi tare da watsama oum-salmah harara da jajayen idanunta.. dariya ta saka tare da cewa  "ƙaramar mara kunya Ni bari ma kigani dan tsayawa gunki ɓata lokaci ne bari naje gun aunty munaya naji meya kamata mu tattauna.. ta ƙara sa faɗa cikin shaƙiyanci..hannun ta Khadijah ta jawo..mayar da'ita tayi a inda ta tashi sannan tace"haba Salmah na lura fa gaba ɗaya ko tausayi na bakyaji..bafa banason shi bane..kawai dai naso nafara karatu kafin nayi aure..kuma yanxu da nayi aure fa sai haihuwa..kawai dai inaji nayi yarinya da aure wallahi..bayanin ta na ƙarshe ne yasaka Salmah faɗawa saman bed tare da ƙyaƙyalewa da dariya.. dariyar da takeyi ce ta baiwa Khadijah haushi..duka takai mata a tsakiyar baya.."dariya ma nabaki ko..faɗar Khadijah tana mai ƙoƙarin sake kai mata wani..gocewa tayi..haɗi da sauka daga saman gadon har lokacin tana dariya.
Ɗan tsagaitawa tayi tare da faɗar"ai kuwa dai Nima sai yanxu na lura da kinyi ƙanƙanta da aure..jinjina kai Khadijah tayi cikin nuna alamar ashe kingane..to amma zanyi magana da yayaah Hisham..idan an kaiki karya taɓamin sweety sai ranar da kika girma..amma fah zan bashi permission na kisses and touchs then little roman...ganin Khadijah tayo kanta ne yasa tayi saurin ficewa daga ɗakin tana mai ƙyalƙala dariya....
•••••
            *...LAGOS NIGERIA...*
.....Zaune suke acikin babban parlourn wanda ya ƙawatu da kayan more rayuwa,su biyar ne acikin parlour,prof,Tanimu tare da matarsa Hajiya hafsatu sai kuma ƴaƴan su namiji ɗaya mata biyu.

"Ni gaskiya Alhaji ban gane wannan abun ba.. wannan ai nuna wariyar launin fata ne..ta yaya munada ƴan mata a gida za'a wani tsallake kansu aje a ɗauki wasu acan.. Hajiya hafsatu ce take wannan maganar cikin fushi..
Kallon ta Alhaji Tanimu yayi tareda girgiza kansa..baisan ta yanda zaiyi Hajiya hafsat ta gane ba..tun lokacin da taji zancen cewa za'aje yiwa ƙasim tambaya duk tabi ta tayar da hankalin ta.
Mubarak dake gefen mahaifiyar tashi ne yaja tsaki haɗi da faɗar"manta kawai mom amma gaskiya ba'ayin abinda ya dace a familyn nan..haka fah na nuna cewa inason yarinyar nan Ameerah amma Uwar ta ƙiri-ƙiri tanuna bata ra'ayi,dan alokacin cemin tayi ameerah yanzu tafara karatu kuma tanada babban buri akanta.. katse shi Hajiya hafsat tayi ta hanyar faɗar"fita batun ƴar baƙin ciki"..wai yanzu mom kina nufin narasa yayaah ƙasim kenan..ɗaya daga cikin matasan ƴan matan dake gefe tafaɗa..to zuhrah me zanyi tunda mahaifin ku bazai tsaya yayi miki fighting akan abinda kukeso ba..ƙafafu ta fara bugawa ƙasa kamar wata yarinya..ɗayar budurwar dake gefen tace ta buɗe baki tare da faɗar"wahala"miƙewe tayi dan barin gun..da harara mom tabita haɗi da faɗar..zanzo ta kanki ne..gyaran murya daddy yayi tare da faɗar"Hafsatu..na'am..meyasa akoda yaushe kike haka ne...a kullum inason ki zauna kiyi tunani aduniyar nan babu Abinda muka rasa sanin kanki ne Abdullahi shams ɗan uwana ne, haka kuma babu ta gefen da yarage ni da komai..bani kaɗai ba kaff! Dangin mu babu wanda a yau zai buɗe baki ya faɗi sharrin sa...to menene na wani nacewa kice lalle sai ƴaƴan ki sunyi aure agidan shi...acikin ƴaƴan ki ba wadda ta rasa miji tun daga ƴaƴan governor's har kan masu faɗa ajiya acikin ƙasar nan..meyasa kikeson siyoma kanki wulaƙanci ne.. acikin halayyar Na'eemerh ba wadda za'a baki labari sai-dai ki bayar..kuma yanda kike da buri akan naki ƴaƴan haka itama take da nata buri..ƙatseshi tayi ta hanyar faɗar"to meyasa bazakayi magana da ambassador ba.. wallahi nasan daka gaya mishi zuhrah Alƙasim takeso bazai ƙiba.
Jinjina kai yayi alamar bazaki taɓa ganewa ba.
•••••
Oum-salmah! Oum-salmah..kiranda ake ƙwalla matane yasa tayi saurin ajiye wayar dake hannun ta..gaida mutanen dake cikin parlourn tayi sannan tace"gani aunty tafaɗa tana mai ƙarasawa cikin parlourn mommah da aunty munaya ne zaune acikin parlourn yayinda ƙanwar mommah da gwaggon Khadijah suke zaune..ta daina kukan faɗar mommah..ehhh! Tun ɗazu.. yanxu haka ta shiga toilet zata yi wanka..Tau yayi.."yawwa oum-salmah amshi wayar nan ki kai mata ta zaɓi colours ukku daga ciki..faɗar aunty munaya tana mai shiga kitchen dan cigaba da abunda takeyi..juyawa Salmah tayi tare da komawa cikin ɗaki..
"Wannan kuma ƴar gidan waye" faɗar gwaggon Khadijah dake gefe.. murmushi mommah tayi tare da faɗar"ƴar gidan Ibrahim wakko ce itace ta biyun..ɗiyar A'isha ce wannan..ehhh! "Itace"..haɓarta ta riƙe tare da furta ikon Allah.....

*#GWANDOU.*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸

DENA KULANIWhere stories live. Discover now