PART 3

6 1 0
                                    

🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*@GWANDOU* .
©2022.

                 DENA KULANI.

'''DEDICATED TO
MOMMAH...
'''
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

page.3
....Zaune suke acikin parlourn juguum..kamar ba wata halitta aciki.
Bakajin motsin komai sai sautin na'urorin dake aiki acikin parlourn.
Ɗago kai mommy tayi tare da watsa idanuwan ta akan Hajjo wadda take zaune akan ɗaya daga cikin kujerin parlourn mai zaman mutum biyu..ta harɗe hannuwan ta aƙirji tana mai dannawa Alƙasim harara.
Gyaran murya mommy tayi haɗi da faɗar ku nake saurare kunzo kun wani sakani a gaba kuna aikawa da juna harara kamar kunje filin yaƙi.
"Shin kin nuna masa yarinyar ko kuwa"ta ƙarara faɗa tana mai kafe hajjo da idanuwa..no mommy Ina zanje na nuna masa bayan ya tareni da nashi Uzurin...ya nuna maki yarinyar ne?...ehh!,ya nunamin wata yarinya barima kigani.

Miƙewa tayi tare da ƙarasawa gun ƙasim haɗi da faɗar"lemme show her the pics"...mayarda wayarsa bayan hannunsa yayi tareda buɗa baki cikin yin ƙasa-ƙasa da murya ya
"furta naƙi".
Juyowa hajjo tayi tare da fuskantar mahaifiyar tasu wadda ta zuba masu ido tana kallon ikon Allah...mommy yace bazai bayar ba "allow him",ranƙwashi hajjo takai mishi a Kai yayi saurin gocewa haɗi da danna mata harara.
"Kamo mishi hoton yarinyar"juyar dakai mommy tayi tana mai ƙara haɗe fuskar ta.."gashi" faɗar hajjo tana ƙoƙarin miƙawa mommy...no miƙa mishi yaganta...mom...shiiii! Banason shirme...ka amsa nace.
Miƙa hannu yayi tare da karbar wayar haɗi da zubawa screen ɗin wayar idanuwa...ɓata fuska yayi sannan yace "whatt! Ke kuma? Ya ƙarashe maganar kamar mai neman tabashi amsa.
"Kasanta kenan"mommy tafaɗa tana mai tsura mashi idanuwa dan jin ƙarin bayani..yeah! But baifi sati biyu da muka fara chat da'ita ba..ɗan numfasawa yayi sannan yaci gaba da faɗar"a Instagram tamun dm..bayan mun gaisane take gayan wai tagani tanaso..ya ƙarashe faɗa tare da hararar gefen shi kamar da wani agun.
Ba hajjo kaɗai ba har mommy saida abun yabata dariya.."to meye aciki"faɗar mommy tana mai kallon hajjo...cigaba tayi da faɗa"meye aciki hajjo, ai abun farin ciki ne kasami mace mai ƙaunar ka kuma Fadeelah galau batada matsala,a ƙasar america ta kammala master's ɗin ta sannan kuma tanada aikinyi..kuma kaff! Faɗin ƙasar nan mahaifinta shine ƙadai ya kusa cimma mahaifinka a arziƙi da kuma tarin dukiya..dan haka ka shirya wa aure idan ma har kanajin cewa baka tashi ba,.. sannan maganar yarinyar da kakeso mayi maganar daga baya ok.
"Wacce yarinyar mommy?faɗar hajjo tana mai yamutse fuska...wadda yace yana so mana..idan yaji zai iya da wahalar mata biyu sai yayi, ba ruwana.
"Mommy she's a poor girl fah" faɗar hajjo tana mai ya mutse fuska..whatt!..kallon mai cike da tambaya mommy ta jefa masa...da gaske ƴar talakawa kakeso?.
Tambayar da mommy ta jefa masa kenan..Alƙasim.. gayamun abunda Hajjo ta faɗa gaskiya ne?...cikin sanyin jiki ya ɗago kansa haɗi da jinjina mata kai..tare da faɗar"ehh! Mommy...but babanta babban malami ne a ƙasar....shut up my dear...alƙasim sai yau naƙara tabbatar da cewa baka da wayo...ƴar matsiyata kakeso ka kawomin acikin gida..acikin zuri'a ta a shafa muna fentin tsiya..ka sake tunani dan wlh Fadeelah zaka aurah..itace uwar jikokinah ba wata ƙazamiya ba.
Dariya Hajjo tasa haɗi da faɗar"Ni wallahi mommy bansan me suke gani a jikin su suke macewa akansu ba.
cigaba tayi da faɗar"Jiya-jiya Hajiya kaltum kemin ƙorafin ƙaninta daya nace sai ya aure wata yarinya..har fahari nake nawa ƙannan basa ƙasar bare har suyi soyayya dasu..ashe muna can muna bacci anai muna minshari.
"Hmm!babban minshari kuwa"faɗar mommy tana mai ƙara kai kallon ta gun ƙasim..inaso wannan maganar abarta ƙasim, Fadeelah galau zaka aura.. itace dai-dai dakai.. sannan inaso kasan dacewar acikin ahalina bazan lamunce haɗa jini da matsiyata ba,idan har kanajin sonta aranka..to kayi gaggawar yakice shi,dan muddin naji wani banzan zance..nasan ta yanda zanyi na kawar da maganar kawai"..ta ƙarashe faɗa tana mai nuna zahiri a hannun ta.
Idanuwa ya fitar waje tare da haɗiye wasu yawu da suka tsaya masa a maƙoshi..yasan halin mahaifiyar tasa.. tabbas yasan halin mahaifiyar tasa..batason abinda zai taɓa kima da mutuncin ta..dan wannan su agurin su babbar hanya ce ta zubar da girma saka jinin talakawa acikin ahali..kuma yasan wannan hanyar da yake neman ɓullawa bamai yiyuwa bace dan zai iya saka ƴar mutane acikin halaka,cikin yanayin sanyin nan nashi yaɗago kanshi haɗi da faɗar "na amince".
Murmushi mommy tayi haɗi da faɗar"is better.........

~~🩸🩸🩸~~
     *. A GARIN MAIDUGURI.*
...abun mamaki..kamar jiya fa muka shiga school amma gashi har mun kammala..hmm! Kedai bari kamar wasa kuma gashi har result yafito.
Matasan ƴan matane kuma budare abin so ga samari..kusan dai kowa yasan yadda ƴan mata waɗanda suka kammala S.S.C.E. suke da farin jini agun samari acikin shekarar yarinyar zata ga tarin manema sannan kuma duk inda kika fita zakiga samari sai binki da kallo suke..to daga shekarar nan ta ɗaga ta biyu tazo ta ukku..dakin kai ta huɗu batare da kin fidda gwani ba to tabbas za'a fara mantawa dake samari zasu fara janye ƙafa..idan kuwa kinada ƙannai mata sai kallo ya koma agunsu(wannan ina faɗa maku wasu abubuwa dake faruwa a ƙyauyen mune,ba lallai ko wanne gari za'a samu hakan ba)..

Oum-salmah..kin kuwa san murnar danayi lokacin da naga result ɗina..ai har daddy na saida ya riƙeni dan shine ma yaduba min..faɗar wata Matashiyar yarinya tana mai cigaba da magana.. wallahi kedai rawa nayi zaune ina dirka ba ƙaƙƙautawa.
Dariya oum-salmah tayi tare da faɗar"rawa fa Khadijah da wannan jikin naki..ta ƙarashe faɗa haɗi da nunata da yatsa..ehh mana to meye aciki ƙiba nafiki ne?...chabb tambaya ma kikeyi..ai kema kinsan ina Ni ina ke..harara Khadijah ta dalla mata tare da faɗar" Salmah banason wulaƙanci fa,idan wani yaji kina faɗar hakan sai ya ɗauka gaskiya ne..yi haƙuri"Tawah"faɗar oum-salmah tana mai haɗe hannuwan ta guri ɗaya.
Yen!yen! Sai an cuce mutum sai kuma arinƙa yi masa ƙaramar murya..dariya suka saka gaba ɗayansu haɗi da tafawa.
Keni Salmah Bama wannan ba..yanzu wace makaranta ce kike ganin yakamata muje.. Khadijah kenan ai kinsan komun tsara bashi zai sa akaimu wadda mukeso ba..no nasan daddy na zai barni nayi zaɓina kema haka abban ki dan haka muyi searching kawai..ok Tau yayi ki bincika muna mana..but ina maganar auren ki da Yaah!Hashim?. oum-salmah ta jefa mata tambayar kai tsaye..whatt.. Salmah ai wannan maganar tuni na jijjigeta haka kawai.. tabbas inason shi amma banajin zan iya auren shi batare da na kammala koda degree bane, kin sanni babe..Ina ƙaunar karatun nan...ko jiya mommah tayimin maganar kamar na mutu naji..wai an tsayar da magana kuma nan da ƙanƙanin lokaci za'a saka ranar biki.. wallahi ina gaya maki da kuka nayi bacci,abunda yasa kika ganni haka normal da aunty munaya mukayi waya da safe itace ta tausar dani..tacemin idan har bana ra'ayi baxa'ayi min auren ba, shine kawai dalilin da yasa kikaga nabar komai.
Hmm!numfashi Salmah taja haɗi da saukewa.. sannan tace wallahi Khadijah har kin saka jikinah sanyi,bazan so abinda zai rabani dake ba.. amma wannan karon inaji ajiki nah kamar auren zai tabbata ne..share hawajen da suka zubo a saman kuncen ta tayi tare da faɗar"Amma kuma zanfi kowa farin ciki idan har auren ya tabbata..ko ba komai na aurar da gudaliya..haɗe fuska Khadijah tayi.. yayin da Salmah ta saka dariya.
Ke har fata kike nayi nesa daku ko..dama na daɗe da fahimtar kin daina damuwa dani..muddin nayi auren na tafi shikenan zaki rufe shafina a gaba ɗaya rayuwar ki.
Baki oum-salmah ta rufe haɗi da faɗar"rufan asiri Ni na'isa na manta dake sarauniya a gidan yaya Hashim..ranƙawashi Khadijah takai mata tayi saurin gocewa tana mai cigaba da dariya..to Bama za'ayi auren ba kuma fatan da kikemin akanki zai faɗa..ɗagowa Salmah tayi tare da faɗar"a tsawon rayuwar ki kin taɓa jin wani namiji yace yana sona?.
Ta ƙarashe faɗa tana mai kallon Khadijah..to ai mijin yana kan hanya kuma inada yaƙinin ya kusa kawo kanshi a gurin Uwar ƴaƴan shi.
Dariya suka saka gaba ɗayansu haɗi da cigaba da firar su.

*°°AFTER SOME HOURS>
(bayan wasu awannin).
°°°tsaye take a jikin ɗaya daga cikin kujerin dining table.. coolers ɗin da ke jere acikin wani tire take cirewa ɗaya bayan ɗaya tana gyarawa ko wacce zama akan dining ɗin.
Aikinta take yi acikin kwanciyar hankali a yayin da kuma tayi nisa acikin tunanin firar ta da Khadijah ta ɗazu,gyaran Muryar da akayi daga bayanta shine ya mayar da'ita daga dogon tunanin data lula murmushi tayi tare da faɗar "Barka da Yammaci Abba"dago idanuwa yayi tare da ƙara watsa matasu ba tare da ya amsa gaisuwar da take masa ba.
Ba Salmah kaɗaiba har Ummah dake fitowa daga kitchen hannunta ɗauke da wani mug saida tasha Jinin jikin ta.

Ɗaya ƙafafunsa yayi tare da ƙarasawa gareta..ƙirjinta ne ya fara dukan ukku-ukku...kar-dai Abban ta yasamu labarin sunje birthday wata ƴar makarantar su itada Khadijah..tana cikin wannan tunanin ne ya ƙara so kusa da'ita..duƙar da kanta tayi ƙasa tana mai musu-musu da baki dan samun abun kare Kai.
Cikin hakan ne kuma maganar sa ta daki dodon kunne ta..yayin da yake cewa"Principal ɗinku ta kirani ɗagowa tayi a dai-dai lokacin ne kuma ya ƙara sa faɗar"sannan vice ɗinku ma yakirani cikin razana ta buɗe idanuwanta haɗi da ƙoƙarin faɗar.....

_To be continue...._

*#GWANDOU*
🩸🩸🩸🩸🩸🩸

DENA KULANITahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon