PART 2

7 1 0
                                    

🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*@GWANDOU* ..

_©2022_ .
               
               *DENA KULANI* .

_Page.2_

                      *ASALIN*
( *AMBASSADOR ABDULLAHI SHAMS* .)

...Mahaifin Ambassador Abdullahi haifaffen jihar Kano ne,a inda mahaifiyar sa take ƴar asalin ƙasar Niger a garin agadaz,.. dangin ambassador Abdullahi masu arziƙi ne,yayin da wasu ma suka ce sungadi arziƙi tun daga kakannin ka kanni.

Ambassador Abdullahi shams ya gadi arziƙi ta uwa da uba dan kuwah ko dangin mahaifiyarsa ba baya ba wajen dukiya, suna cikin jerin masu arziƙi na farko a ƙasar niger.

A yanzu haka ambassador Abdullahi shams,babban ɗan kasuwa ne wanda sunan sa yazagaye kaff, ƙasashen duniya,yake kuma da hannayen jari a ƙasashe da dama.
Yanzu haka yana tareda mahaifiyarsa da iyalinsa a garin Abuja Nigeria,.. ƴaƴansa shidda (6)maza biyu mata huɗu,Balkisu Al-ƙasim, Muhammad, Shema'u, Ameerah,sai kuma El-herm.
Matarsa Hajiya na'eemah bata ga maciji da talaka ko ƙadan, wannan aƙidar Tata itace ta zauna ajinin ƴaƴanta mata musamman balki da Shema'u dan ita ameerah hankalinta bai zaunu ba kuma yawancin zamanta a gurin kakarta take yinsa saboda basa wani shiri da mahaifiyarta...ba komai ya jawo hakan ba kuwa sai ɗan banbancin halayyar da suke dashi a tsakaninsu.

            *CI GABAN LABARI* ...

...Matashin saurayi ne zaune akan dining, dogo ne fari tass, sanye yake da shadda kaftan ruwan zuma,wadda ta ƙawatu da aikin brown ɗin zare.
Abincinsa yakeci hankali kwance batare da wata damuwa ba yayin da yake aiki da wayar shi murmushi ne kwance akan kyakkyawar fuskarsa,hakan zai nuna maka cewa yana wani nishaɗin ne.

Jan ɗaya daga cikin kujerin da akayi ne ya mayar dashi daga duniyar nishaɗin daya lula, murmushi ya saki yana mai ajiye wayar dake hannun shi,tareda faɗar "good morning mommy,.. murmushi Hajiya na'eemah tayi tareda faɗar "morning dear, numfashi taja sannan taci gaba da magana, meya hana Muhammad dawowah ne?hmm! Ko har yanzu yana fushi ne?.

Ajiye cokalin dake hannunsa Al-ƙasim yayi tareda juyowa ya ƙara fuskantar mahaifiyar tasa, No mommy ba wannan dalilin bane ya hana shi dawowah ba akwai ƴan ayukkan da yake so ya kammala ne, dan har mun shirya tafiyar tare kuma sai wani aikin ya taso masa shine kawai dalilin.
Numfashi ta sauke, haɗi da kallon ɗan nata,tareda faɗar"ka tabbatar Wannan ne..ehh! Mommy...ok shikenan dama na tambaya ne dan nasan halin murɗaɗɗen halin shine.

Fitowar ameerah ne yasa suka bita da kallo gaba ɗayansu,sanye take da kayan bacci hakan ne ya tabbatar musu da cewar lokacin ta tashi daga baccin, Good morning mommy, ta ƙarasa faɗa haɗi da zama ɗaya daga cikin kujerin dining ɗin, "welcome back brother,ta faɗa tanamai fara serving na kanta... thanks sister, ya exams...kwanaki dady yake gayamun kin kusa kammala exams ɗinki.

Cokalin dake hannunta ta ajiye tareda kallon mommy sannan ta mayar da kallon ta agurin shi, wai yaya ƙasim kar-dai kacemun bakasan har exams ta fito ba?
lallai kam, gashi har ameerah na batun wucewa ƙasar Paris karatu,..cike da mamaki ya furta"Paris kuma mommy, duk makarantun da suke acikin Nigeria basuyi ba har sai ta sake zuwa ƙasar waje karatu? Uhm!.
To meye aciki, naga dai kaima a waje kayi karatu kuma yanzu haka acan kake rayuwar ka, wani abun yasa meka ne?...naga dai acan tayi secondary school gashi kuma ta gama lafiya ƙalau dan haka kar nakuma jin wannan maganar.

Nifa mommy a naija zanci gaba da karatu na, dan haka karma ki kawo min wani zance dan nagaji da rayuwar can... rayuwar doka anan. kawai zan cigaba da karatu na, tomm.
Faɗar ameerah tana mai cigaba dacin abincin ta hankali kwance ba tareda tasake cewa komai ba.
..bazakiyi anan ba nace, bazakiyi ba dole kije ƙasashe masu cigaba kiyi karatu hankali kwance,kai kuma idan har bazaka goye bayan taje waje karatu ba na fitar dakai acikin maganarr...buga teburin da akayi shine ya dakatar da'ita daga ƙarasa maganarta.
Dakata Malama,shin dakike wannan maganar karatunki ko nawah,haba dan Allah karfa kiso ki takurawa rayuwata yanzu fa nakai matakin da zan iya yanke wa kaina ehh! Ko a'ah! So be careful ok.
Juyawa tayi cikin fushi,cike da sassarfa take taka matakalan da zasu fitar da ita daga dining ɗin kamar zata tashi sama.

Ruwan da Al-ƙasim ya miƙa mata sune suka mayar da'ita daga nisan da tayi,ajiyar zuciya take ta saukewa ba ƙaƙƙautawa.
Kinga illar fitar da'ita wajen ko?,..yanzu mommy ki duba fah kigani secondary kawai tayi a ƙasar London amma ki dubi idanuwan ameerah yanda suka dawo tsakiyar kai, batajin maganar kowah..idan zaki yarda da magana ta mommy yanzu haka ameerah tanashan ƙwayoy...
"whatttt!!..mekake shirin faɗa ne ƙashim..kafita daga hankalinka ne? Kodai kafara ƙiyayyar ƴan uwanka ne? Ƴar tawa?..calm down mommy..bafa nafaɗa danki tayarda hankalin ki bane, kawai dai abinda nake hasashe ne ok.
Kaci ƙaniyar ka dakai da hasashen, Ni banyi shashanci da kuruciya taba,dan haka bazan haifi ƴan iska ba..sorry mommy.

Kwafa tayi sannan taci gaba da faɗar" Bama wannan ba..kunyi magana da hajjoo (balkisu)?..kallon ta yayi cikin yanayin dake nuna mamaki sannan yace" bayan gaisawa kuma akwai wani magana da zamu tattauna da'ita ne?...ok kenan bata gaya maka komai ba..ehh! Nikam ba abinda muka tattauna..but tunda gaki kuma ina ganin abu ɗayane kifaɗamun kawai ok.
"Bari nazo" faɗar mommy tana mai mayarda hankalinta gun wayar ta.
"Hello,..hajjo kisameni a dining area yanzun nan kinji.
Ajiye wayar tayi tana mai ƙara fuskantar sa...Uhm! Ya ayyukan naku daddynku ya gaya mini cewa abubuwan sai gaba suke Masha Allah..
ehh! Alhmdllh gaskiya komai yana cigaba da tafiya da kyau, yanzu haka Ni ina ƙoƙarin zuba hannun jari da wasu kamfanoni da suke a ƙasar _england_ da kuma _Paris._ ."wow that's my son" faɗar mommy tana washe haƙora.. lallai yarona ya zama babban mutum.. Muhammad fah..mug ɗin da ke gefen shi ya jawo tare da ɗaukar ƙaramin cup ɗin dake gabanshi, tsiyaya lemon dake ciki yayi sannan ya ɗago..no mommy kinsan fah my bro bayason ana fallasa mishi secret then,yafiso yafaɗa da kanshi,so kijira dawowan shi..zai gaya maki komai about him ok.

Al-ƙasim!..takira sunan shi tana mai kafeshi da idanuwa..."Yes mom"yafaɗa cike da sakalci,..gayamun me Muhammad yayi achieving banason shashanci..kodai har yanzu yana tareda damuwa ne.. Please ƙasim karkamin ƙarya.
"Hhhh" best mommy in the world..ok ƙasim dariya ma nabaka..no sorry mommy..kawai dai inaso kigane cewa Muhammad fah yayi forgetting na komai ya kama aikin shi,..tunda kuka nuna bakwason yayi aikin lafiyar ya tattara ya watsar,..yanzu haka Muhammad ƙasa biyu sukayi masa request na haɗa hannun jari dasu.. _Qatar_ da kuma _U.k_ sannan kuma ya kammala ginin babbar University da yake yi a ƙasar nan kuma acikin garinnan na Abuja..wadda take ƙunshe da fannoni da dama.. sannan yananan yana nema mata greatest teachers daga ƙasashen waje har nan gida Nigeria..sannan makarantar tana ɗauke da special and desirables men and female hostels..so calm down mommy your son's wanna be famous of the world.
"Wow!Alƙasim ka faranta mun rai ba kaɗan ba,ina alfahari daku ta ƙarashe faɗa tana mai murmushi irin na ƙasaitattun matan nan,to maganar aure fa,Kanada wadda kake nema ne?
Gaban sane yayi wani dukan ukku-ukku,cike da gargada ya fara faɗar,
"mom..mom..Ina..da but..ƙarasowar Hajjo gurin ne ya katse mishi maganar da yake kanyi.
"Barkan ku da hutawa"
hajjo ta faɗa tana mai ƙoƙarin zama...tsayar da'ita mommy tayi ta hanyar cewa"no hajjo muje can cikin parlour dan maganar bata nan bace,kinsan ƙannan naki sai nayi da gaske..naji yafara kawomin zancen yanada wata..muje naji ƴar waye acikin ƙasar nan.
Dariya hajjo ta saka tana mai kallon ƙasim da yayi wani kalar tausayi duk jikinsa yayi sanyi,gaba mommy tayi tana mai faɗar "hajjo!..jawomin kan ƙanin nan naki nayi dashi yanxun nan.
"Oya tashi muje mana"cewar hajjo tana mai ƙoƙarin jan hannun shi,ɗan ɗagowa yayi tareda leƙawa ta  bayanta ganin mommy tayi nisa ne yasa ya mayarda hankalin shi gurinta tareda faɗar
"Please sister ki taimakeni da wannan alfarmar,nasan mommy na ɗaukar shawarar ki sosai idan kinka bata shawara zata ɗauka kinji.
wai menene kaketa wani magiya kaje kai tsaye ka gayan abinda kake so mana.
Wayarshi yayi saurin jawowa.. buɗe ta yayi tare da shiga cikin galleries ɗinsa,hoton wata yarinya ya shiga tareda mika mata wayar.
Wow! Wacece wannan, tanada kyau.. murmushi ƙasim yayi tare da jinjina kai,"but who's her father? Faɗar hajjo tana mai tsura mishi ido.
ya mutse fuska yayi tare da kallon ta.. "menene kuma na wani tambayar babanta"
..tambaya nayi dan nasan ƴar gidan waye.."to sannu mommy.. ahh..sannu tunda haihuwa na kikayi da zaki wani tsureni da tambaya,barima kawai na gaya maki ita ba ƴar kowan kowa bace,..abinda nasani kawai su talakawa ne..babanta babban malami ne a garin su..daga ƙarshe abunda zan gaya maki shine itace matar da zan auraah...
Idanuwa hajjo ta fitar waje haɗi da faɗar"whatt".....

🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*@GWANDOU* 😍

DENA KULANIWhere stories live. Discover now