PART 1

35 2 0
                                    

🩸🩸🩸🩸🩸🩸
*GWANDOU* ..1
_©2022._

                *DENA KULANI* .
_Page._ 1

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_ .

'''DEDICATED TO MOMMAH..'''
••••••••••••••
*IBRAHIM ALI WAKKO PALACE* ...

Matashiyar budurwa ce zaune a ɗaya daga cikin manya royal chairs ɗin da ke zube acikin haɗaɗɗen parlourn, kishingiɗe take a ɗaya side ɗin kujerar da take zaune, hannun ta ɗauke da wani book da alama shi take dubawa.

Zirrrr-zirrrr! Kukan da wayarta keyi shine ya mayar da ita daga duniyar littafin da tafaɗa, hannu ta miƙa ta ɗauki wayar haɗi da ɗaurawa a kunnen ta.
"Na'am Khadijah, lafiya ƙalau nake kamar ke".
bansan me ta cikin wayar ta gaya mata ba naga ta zare idanuwa haɗi da xabura tare da faɗar,
yaushe?

O.ok-ok bari nayi sauri Nima aduba min tawah".
Saurin ajiye wayar tayi agefen kujera saura ƙiris ta faɗi,batama lura ba saboda tsananin saurin da take zabgawa.

"Ummah-ummah! Wa'ec tafito wallahi Ummah exam ta fito", take ta faɗa ba ƙaƙƙautawa.

Ganin wanda yake zaune a gefen Ummah da gani suna tattauna wata magana mai muhimmanci ne, yasa ta fara tattara natsuwar ta.

Kallo na nakai gun wadda take kira da Ummah,Masha Allah wata matashiyar matace Zaune a saman sallaya yayinda wani matashin saurayi yake zaune a gefen ta kallo ɗaya zaka yi musu ka gane cewa dukan su jinin Fulani na yawo a jikinsu.

"Lafiya oum-salmah kike min wannan kira kamar zaki ƙara Arar baki,meya faru"
Ummah ta ƙarasa faɗa tana mai zuba mata idanuwa.
Ganin yanda tayi tsuru-tsuru da idanuwa ne yasa Ummah girgiza kai haɗi da kallon saurayin dake zaune a gefen ta wanda shima ya zubawa Oum-salmah idanuwa yana mata kallon mamaki janye idanuwan ta tayi daga kansa tare da faɗar
Abdul...na'am Ummah...kaje ta baka cards ɗinta na wa'ec aduba mata, dan nasan idan nace sai gobe yarinyar nan bazata samu baccin kirki ba.

Ok Tauyayi, ke.. je.....maganarsa ce ta maƙale ganin yanda tayi wata sufa kamar fatalwa, kasa rufe baki yayi saboda ganin ikon Allah, murmushi Ummah tayi tare da faɗar "Allah ya shirya ki Salmah"da Ameen yaah Abdul ya amsa dan tana buƙatar addu'ar.

Shigowar tane yasa Ummah ƙara Binta da kallo haɗi da faɗar"kifayi a hankali,duk kinbi kin susuta kanki...

Uhm!!"Tauyayi"
Salmahh ta ƙarashe faɗa idanuwanta na cikowa da hawaye.
Miƙawa Yaah Abdul slip ɗin tayi haɗi da faɗar"Please yaah Abdul dan Allah kayi sauri...ɗagowa yayi tare da hararar gefen ta haɗi da faɗar matsamun aka kada kifaɗa akaina, dan nalura kinyi loosing control ɗinki, saura balance.

Tura baki tayi tare da komawa gefen Ummah ta zauna,...zaro wayarshi yayi daga cikin aljihu, ganin ya fara duba slip ɗin tata hakan ya tabbatar mata da cewa acikin wayarshi zai duba mata,nan take kuwa jikinta ya ƙara tsuma,Rufe idanuwan ta tayi tare da cusa fuskarta a tsakanin cinyoyin ta, addu'a kuwa babu kalar wadda bata jawowah amma kowacce daga tafara daga tsaka sai kuma tafara ta kasa ƙarasawa...wannan shi ake kira da Anxiety.

Yes..yes..yes! Jin irin yanda  yaah Abdul keyi shine ya mayarda ita a hayyacinta,saurin miƙewa tayi kamar zata kife ta ƙarasa gunshi...zubewa tayi dai-dai ƙafafun sa tare da tambayar sa"menaci yaya,menaci? Nasamu?
...kin samu sister,kinsamu gaba ɗaya B, zaro idanu Ummah dake gefensu tayi tare da faɗar B, fah kace Abdul ...kuma gaba ɗaya?

Ɗagowa yayi daga inda yake zaune tare da nunawa Ummah fuskar wayar tasa, Masha Allah Ummah tafara faɗa haɗi da fara shafa kan Salmah da tayi relax a gefen ta.

"Bari naje a fito mata da ita"
faɗar Abdul yana mai miƙewa tsaye dan barin ɗakin murmushi ɗauke saman fuskar shi,iyye Salmah yar jami'a yafaɗa yana mai barin ɗakin.

DENA KULANIWhere stories live. Discover now