AƘIDATA CHAPTER 19 And 20

585 44 6
                                    

_*AƘIDATA*_

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

ELEGANT ONLINE WRITER'S

PART1
Page 19_20

Gaba ɗaya Yusuf ya dirircei yace "Amm... Amma Yallaɓai wani mataki zaka ɗauka haka akanta, ina fatan ba wanda ze mata tsauri bane?"

"Yusuf kenan, ka damu da al'amarin Widad haka nan naji na yadda da kai, shiyasa har nake saka a cikin abunda ya shafi rayuwar mu, na yanke shawarar tsayar da ranar Aurenta a ƙarshen wannan watan zuwa farkon wata me kamawa"

"Amma yallaɓai baka ganin hakan ze sake jefa rayuwarta cikin hatsari, duba da yadda babu Aure a tsarin Rayuwar ta?"

"Yusuf, Widad fa mutum ce kuma lafiyayyiya tana ƙin Aurene saboda wasu dalilanta da suke masu rauni a gurina, bana so in mutu in barta cikin kaɗaici, nasan Bulama baze taɓa barin ɗansa ya Wulaƙanta Widad ba ko bayan raina, dan Allah ka cigaba da yimana addu'a, Amma insha Allah ko ba taso zan ɗaura mata aure karo na farko a rayuwata da zan ɓata mata rai, amma ina fatan hakan ya zama alkhairi a gareta, Insha Allah gobe zuwa jibi zan dawk"

"shikenan Yallaɓai, Allah ya tabattar da alkhairi ya dawo da kai lafiya"

"Ameen Yusufa nagode sosai"

Tunda sukayi Sallama da mahaifin Widad abun duniya ya damu Yusuf, ji yake matakin da mahaifin Widad ke shirin ɗauka tamkar ƙarasa rugurguza rayuwar uwar ɗakinsa ne gaba ɗaya, matakin yayi tsauri sosai, haka nan yaji wani irin matsanancin kishi na taso masa game da Widad ɗin.

Dafe kansa yayi tare da faɗin "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Allah ka tsareni da sake faɗawa hatsarin Soyayya, Allah yasa tausayinta kawai nake ji, tabbas idan na fara son Widad zan shiga matsala fiye da wadda nasha a baya"

Bacci kam se Ɓarawo ne ya kama Yusuf.

Kwana biyu a tsakani Yusuf yana zuwa gidansu Widad amma ba wani aiki da yake yi, kuma sam baya ganinta.

Abubuwa sun ƙara cakuɗewa Yusuf, tunani kala kala a zuciyarsa amma zuciyarsa tafi fargaba akan hukuncin da Daddy ya yanke ɗauka akan Widad.

Ya ɗakko wayarsa yana ɗan duddubawa kawai yaga message ya shigo wayarsa, anyiwa ma'aikata canjin gurin aiki ciki harda Abbas, an maida Abbas aiki a kudancin Nigeria, abun ya ɗaurewa Yusuf kai sosai, mafi akasari anfi yin wa mutum wannan canjin aikin ne, kodai dan wani mahimmin bincike, ko ƙarin girma kokuma dan hukunci ga wani laifi da ya aikata, sedai shi a ganinsa babu ɗaya da Abbas yayi wanda zesa ayi masa wannan transfer.

Ba shiri Yusuf ya bar gidansu Widad ya tafi gurin aikinsu, kai tsaye ofishin Oga Suleiman ya wuce, gaje suka gaisa Suleiman yace "Yusuf naga aikin daka turomin, kayi ƙoƙari sosai Yusuf sannan ina taya ka murna da sabon muƙaminka"

AƘIDA TAWhere stories live. Discover now