AƘIDA TA

2.1K 75 10
                                    

Arewabooks

https://www.arewabooks.com/book?id=62332f71d5864b6d6a4e9246

TALLA! TALLA!! TALLA!!!

Ina masoya wanda suka bibiye ni a littafina na ABDUL JALAL, da kuma WATA KISSAR yanzu ma na shirya tsaf domin kawo muku wani ƙasaitaccen littafin me ɗauke da sabon salo da kuma sarƙaƙiya,
ga ɗanɗano daga cikin littafin

_*AƘIDATA*_

*PART1*
_Page 1_

*written and edited by*

_*AYSHERCOOL*
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*

Bismillahir rahmanirrahim, da sunan Allah me Rahama me jin ƙai, Wannan littafi ƙirƙirarren labari ne banyi shi dan cin zarafi ko cin fuska ga wani ko wata ko wata ƙabila ba, idan har wani ko wata yaga wani abu daya yi kaman ceceniya da rayuwar sa ko ƙabilar sa Amin Afuwa banyi dan cin zarafin wani ko wata ba.
Wannan littafin mallaka tane, ban yadda a juyamin labari ta kowane fanni ba ba tare da izinina ba.

What's App : 07063065680
Facebook : real Humaira
Watpad : Ayshercool7724
Gmail : Www.ayshertadam@gmail.com

Katafaren ɗakin Bacci ne me ɗauke da kayan alatu na more Rayuwa da jin daɗi, idan ka ƙarewa ɗakin kallo zaka tabattar da ma'abocin wannan ɗakin Allah yayi masa Ni'imar Dukiya dan ya ƙawatu da dukkan wasu kayan more rayuwa, kallo ɗaya zakayiwa ɗakin kasan mamalakin ɗakin mace ce, saboda kan madubin dake ɗakin shaƙe yake da kayan kwalliya da gyaran jiki, ga wani show glass ɗauke da takalma da jakunkuna na adon mata kamar wani kantin saida kayan ado, kai da ganin takalma da jakunkunan nan kasan bana talaka bane, Makeken Gadon dake ɗakin ne ɗauke da wata kyakywar matashiyar budurwa ta baje gashin kanta tana bacci cikin nutsuwa.

Hasken ranar da ya ratso ta tagar ɗakin ne yake dukan fuskarta wanda hakan yasa ta motsa a hankali, ta buɗe idanuwanta.
Ɗan ya mutsa fuska tayi, ta miƙe zaune ta kalli Agogon bangon dake ɗakin nata, ƙarfe tara da rabi na Safiya, a hankali ta zuro ƙafafuwanta ƙasa ta miƙe ta nufi banɗakin dake cikin ɗakin nata.
Aljannar Duniya shi kansa ba ɗaya nata ya isa a tsaya a kalla.

Wanka matashiyar tayi ta fito daga ita se towel, abun mamaki har an gyara mata inda ta tashi, ta zauna a gaban mudubi, ta shafa wannan ta goga wancan, gashi komai nata a hankali cikin nutsuwa take aiwatar dashi, riga da skirt na blouse ta ɗakko ta saka da ɗan guntun mayafi, ta ɗora akanta tasaka takalmin ta me matuƙar tsini da jakarsa, seda ta kalli agogon hannun ta ƙarfe goma da rabi dai dai sannaan ta buɗe ɗakin ta fito.

Wani irin taku take na ƙasaita, takalmin ta na bada sauti ƙwas, ƙwas, ta fito wani irin ƙaton falo ta zauna, ba ta daɗe da zama ba, me aiki ta kawo fruit gabanta ta ajiye, bata kalli inda fruits ɗin suke ba, se kallon tsintsyar hannun ta da ta ɗaurawa Agogo take yi.

"wato Isa rayuwar ƙauye akwai daɗi akwai wahala"
Wanda aka kira Isa yace

"Haba ɗan uwa wani irin daɗi a ƙauye? Kai ka taɓa ganin wanda yake birni ya koma ƙauye banda zunzurutun wahala mene ne a ƙauyen?"

"to ai Rayuwar ƙauye tafi ta birni kwanciyar hankali, ba tashin hankali ba fargaba, amma kaga birni a nan rashin gaskiya ya ƙare"

"tabdijan lallai ma sani, ai tunda Allah ya kawoni birni na samu aikin gadin nan, idan naje ƙauye to ziyara na kai Amma bani babu zaman ƙauye ina daf da dawo da iyalina nan ma"

"kai gidan nan zaka dawo da iyalin naka, kaifa kace min zaman fargaba kake a kowane lokaci za'a iya sallamar ka fa"

Isa yace "rufamin Asiri in kawo iyalina gidan nan Haya zan kama"

AƘIDA TAWhere stories live. Discover now