_Cen cikin dakunan dake kewaye da kitchen din bukka" wata yarinya mai shekara goma sha daya take tambaya,
"mama ni kam ina takalmi na ? na duba ban gansu ba" Mama wacce take zaune kofar kitchen gaban murhu tana ta faman fita wuta tace" Mairo kin san dai wacce zata sanya miki takalmi ko!
Mairo tace na shiga uku mama kuma so nake na wanke su, anjima akwai zuwa dandali pha" kuma nayi ku san sati banje ba saboda ban da lafiya" Mama tace tohhh tunda zuwa dandalin ya zama ibada sai ki jira ta dawo tukunna"
Mairo ta sake cewa wallahi mama yau sai na daki Ummi na hanata daukar min kaya amma bata ji, kullin sai ta san yadda zata nemi tsokana ta" Mama tace ni kam bazan hanaki bugun taba, yanzu haka nima ita nake jira tun karfe goma sha daya na safe na aiketa siyan kukar miya, yanzu ana neman azahar babu Ummi babu kuka, babu labarin ta" sai da maman halilu ta bani" babu irin neman da Halilu baiyiwa yarinyar nan ba amma bai ganta ba"

Mairo ta fito tasamu kujera ta zauna kusa da mama tana taya ta gyara wuta tace Mama ki duba halin da kike ciki Amma kiyita faman aiki" don Allah kawo kije daki ki kwanta" dayake Mama ciki gareta kuma tana gab da haihuwa ne" Mama tace aa Mairo barshi kawai ke fa kikayi tuwo jiya kikayi miya sannan kikayi wanke wanke dazu" ki bari miya ce ta rage bari na karasa"
Mairo tayi murmushi tace naji to kawo dai in miki hakanan Mama ta sakar mata tace to ba daki zani ba, nasan ina zuwa bacci zai dauke ni, ni kam bani so nayi bacci yanzu" Mairo tace toh maman mu, suna ta hira abinsu har suka gama suka koma kan barandar d'akunan nasu, suka shimfida tabarma suna hira, Maman Halilu da Mai gidan dawa suma suka fito barandar suna taya Mama hira, at the same time suna cin "Tuwon dawa miyar kuka" Mama tace Mairo kije ki dubo min ita kinsan halinta yanzu nan in ba'ai wasa ba zata iya kaiwa yamma kuma sai ta biya dandali sannan ta dawo" Ummi inba yunwa taji ba bata dawowa gida" ni banma san me ya sa na aike ta ba wallahi,
Maman Halilu tace Mama addu'a kawai zaki rinka yi mata Mama tayi shuru don ita lamarin Ummi tsoro yake bata"yarinya kamar me aljanu.
Mai gidan dawa ce dama ke goya mata baya wani sa'in, Amma yau dinma shuru tayi saboda itama lamarin Ummi na tsoratar da ita" Mai gidan dawa tace Mairo bari toh akara jimawa idan bata shigo ba sai kije ki nemo ta koh" Mairo tace toh"

Readers wai shin Ina Ummi kwaras take ne ?
Follow me👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

************************************

Tas! Tas! Tas!! Karar mari kawai kakeji a wajan shagon mai shayi na hangosu wanda shagon ma a rufe yake, kofar falangen shagon ne na hango wani dogon saurayi ba laifi zubin fulani gare sa, yanatsaye sanye cikin wata kodaddiyar green shadda duk tabi ta yayyage da wani wizyn wando black shi ma dai duk ya kokkode, sai wata jar hula da 'yan kyauye suke sanyawa kaga tayi kulu asaman kai" yana rike da kuncin shi da hannun damar sa, fuskar nan tashi ta yayyamutse kamar wanda akai ma duren ko-ko ( pap, kunu) ya kalli 'yar karamar yarinyar dake tsaye gabanshi wanda itace ta dauke shi da mari har uku saboda ya kama hannunta yana son yi mata magana ne ita kuma bata son ta tsaya"  ya cize lebe yana sake cewa " "Yanzu Ummi ni kika mara"
Ummi tace zan maka fiye da haka ma matukar ka sake gigin tabamin hannu" mara zuciya kawai" karamar yarinya ce amma ta buga masa tsoki tsabar rashin kunya dayai mata katutu"
Ya girgiza kai yace "Ummi" gidan ku babu manya ne ?
___ko dana duba yarinyar sai naga shigan da tayi bashida maraba da ta saurayin"
"Ummi dai yarinya ce wacce bazata wuce shekara Takwas zuwa Tara ba, 8-9 years, she is black in completion ( baka ce ), Fuskarta round face ne, hancinta dogo kamar an dwisana pencil, haka zalika bakin d'an tsit (very small and she has a pink lips), sai idanuwanta manya ne amma daga ciki yayi yellow yellow kadan" idan ka koma kallon tsarin surarta kuwa baza ka kirata da siririya ba kuma ba doguwa bace" dukda ma bata gama girma ba amma daka ganta kaga irin matan nan ne marasa tsayi, sai dai kasata alayin average" sanye take cikin wata shadda lace ruwan bonvita wanda akai yayinta 2003, shaddar nan ta tsufa har wani fari fari takeyi amma kallo daya zakai mata kasan tasha wanki da guga, ta daura irin dan kwalin yan kyauye dinnan blue color fuskar nan tata kuwa tasha bille da kwalli sannan akai pente penten jan-baki a goshi da saman ido, kugunta kuwa an daure/tamke shi gam da wani yalon kyalle kai kace abin tata ne saboda tsabar transparent ne kuma ya tsufa sosai ya chukurkude"ahakan pha ita kwalliyar juma'a tayi kafafuwanta kuma wasu jajayen takalma ta sanya masu tsini" hill" wanda aradu sun girmi yar mitsilar kafarta amma don jaraba hakanan ta sanya su"

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now