Muna nan zaune su Yaya muhammad suka dawo, Momma bata hana su shiga ciki ba" haka kawai naji kaman wani abu ya faru da Abba don haka sai nayi kokarin tashi na rike stick dina Ina kokarin shiga ward din"

Momma kaman ta rike ni Amma sai ta kyaleni don itama ta shiga cikin wani hali" Ina shiga dakin naga an rufe fuskar Abba da farin bedsheets , Yaya Muhammad ya rungume Ummi yana comforting dinta Yaya  Faisal ya rungume Ya Saifullah yana bashi hakuri"

Na karasa wajan Ina cewa what's going on Ummi Abba ya kwanta bacci ne, Jikin yayi sauki koh Alhamdulillah dama nayi masa Addu'a yanzunnan Abba Allah ya kara maka lafiya" ganin kowa yai min shuru babu mai cewa uffan hakan yasa na samu waje kusa da Abba na zauna, daga bisani naga suna fita daya bayan daya" ban damu ba kawai na kwanta akan kirjin Abba Ina maida numfashi har kusan rabin awa kafin naga an shigo da wani gadon karfe wanda ake daura mattatu (gawa)
Ina kallo aka yi kama kama aka daura Abba, sai alokacin na fara wani kalan tunani amma nai saurin korar tunanin acikin rai na" kafin mubar asibitin Daddy, Mom da granny suka zo, nidai Momma tace min zan bisu gida Mom da Granny zasu kwana a hospital.

A hanya nake ta faman tambayar me yasa zamu maida Abba gida, shin ya samu sauki ne? Amma shuru babu mai tanka min har muka iso gida.

Toh fah alokacin ne na gane Allah yayi wa Abba rasuwa, kullu nafsin za'ikatul maut"
washegari da za'akaishi makwancinsa abokanan shi suna ta zuwa yan maradi da yan katsina da na kaduna sun cika a gidan shi na marafa estate, Ina ji Ina gani aka kai Abba gidanshi na gaskiya" hakika nayi  kuka fiye da tunanin mai karatu" na rasa mahaifi na mai so na" duk kokarin danake na inyi hakuri Amma na kasa har ciwo na ya tashi ranar sadakar uku, Yaya Faisal ne ya siyamin maganin da likita yace na rinka sha da zaran ciwo na ya tashi kuma cikin ikon Allah a kwana biyu na samu sauki, kuma aranar granny ta kira Momma a waya take shaida mata cewa Hafiz ya farfad'o"

Wayyooo Allah dadi kaman ya kashe ni na takurawa Momma da ta kaini hospital naga Yayanah" Momma ta sanya Yaya Saifullah ya kaini" Ina shiga ward din  na hadu dasu Mom, Mom ta rungume ni tana cewa d'iyata ya kk? Kafin na amsa Granny ma tace takwara kina lafiya ?

Gyada masu kai nayi Ina mai leken inda Yayanah yake kwance"  to my own surprised sai naga yana kallon mu fuskarshi kuwa a d'aure ya fito a asalin sojan shi" al my thoughts was he will say something to me amma ko dana mishi magana idanu kawai yake bina dashi baya cewa komai" I even touched him so that he can feel my sense of touch amma duk abanza na kalli su Mom nace" Mom me ya samu yaya nah na dauka yasamu lafiya tunda ya farka?

Granny tace haka yake fah Jiddah tun jiya daya farka likitoci sukai mashi yan gwaje gwajen su, baya cewa komai har yanzu" Mom ta d'aura da cewa Jiddah doctor yace best treatment din da za'ai Masa shine a fitar dashi waje idan aka mashi aiki a brain dinshi to inshallahu ana sa ran duk abinda ya manta zai dawo brain dinshi.

Cikin kuka nace then what are we waiting for Mom, Granng please we should do something kafin abun yayi yawa" Mom tace Jiddah munyi iya kokarin muga mun fitar dashi a jiya Daddy kwana yayi yana booking flights online amma bai samu ba, yau yaje tun safe amma sun tabbatar mashi da cewa babu jirgin dazaije wani country saboda Covid-19 dinnan"

Ohhhh gosh na daki karfen gadon, Ina kallon Yaya nah wanda shima ido ya kura min kaman mai shirin yin magana" na share hawayen daya zubo min Ina cewa Yaya Hafiz inshaAllah zaka samu sauki da yardar Allah"
Mom suka amsa da amiin ya rabbi"

**********************
Akwana atashi ba wuya kwanaki na ta tafiya kamar kyaftawar ido, Ummi basu koma katsina ba sai sukayi zaman su gidan Abba na marafa ita da Saifullah wanda kullin shi yake rarrashinta, saboda condition dinta ya nemi transfer awajan aiki aka dawo dashi kaduna" shi kuma Muhammad dama Abba ya siya mishi dankareren gida a malali, so suna cen shi da Leemarh wacce take da ciki tama kusan haihuwa alokacin" ita ma Fatima ciki gareta da alama ma tare zasu haihu.

December,2020
**************

Aka fara shirye shiryen fitar da yayanah waje saboda ai mashi aiki" alokacin ciwon zuciya na ya tashi saboda damuwar danake sanya kaina aciki,
Lafiya lau nake kula da Yaya Hafiz a hospital kawai watarana na yanki jiki na fad'i shine kawai aka kawo ni Barau Dikko teaching hospital wani likita Wanda ya karanci komai akan zuciya shi yake dubani ayanzu haka labarin danake baki Diela
" Daddy ya auri Ummi kuma tana zaune a gidan ta na marafa, Yaya Hafiz kuma yana NAFhospital kuma gobe ne tafiyansu,

Nace to meyasa ba'a kaishi ba tun farkon december sai yanzu January,2021
Jiddah tace Daddy ne yace abari na samu sauki sai atafi dani Kuma alhamdulillah saukiya samu don yanzu garau nakejin zuciyata kuma Ina da hope inshaAllah Yaya Hafiz zai warke"

*****************

The next day aka sallami Jiddah kuma direct airport suka wuce suka hau jirgin dazai kai su Abuja wanda daga cen zasu tafi"
Tafiyar daga ita Jiddah, Granny, Daddy, sai Ammi su kenan"

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Littafi dai yana kan gangara Insha Allahu😁

Taku DIELAIBRAHIM ✍️
VOTE
COMMENT PLEASE

RAYUWAR JIDDAH ✔Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora