"Ummi tai murmushin karfin hali ta chiza lebe ta kalli gaba daya yaran nata, sannan ta cigaba" tace "indeed that was the greatest tragedy that ever happened to me in my life" i even regrets coming to this world on that very day""" just because of what happened and what Ammi's did was so scary, it really touched my heart not only me but all the rest of our family"
" Ammi ta zagi ABUBAKAR uwa da uba, tai masa kashedi karya kuskura ya kuma shiga rayuwa ta "she was hot to the extend that har mare shi a kumatun sa , sannan ta wulakanta karatunsa da aikin dayakeyi, "ya ilahi! " Abubakar fah akaiwa wannan cin mutuncin " ni kaina I was very shocked Ina kokwanto anya Ammin dana sani ce, Anya Ammi na ne take aikata wannan abun, tuni zuciya ta ta daskare nakasa tabuka komai " Momma ce tai ta bata hakuri tace hold on your self Ammi" please kibar yaronnan hakanan for goodness sake" ganin Ammi takiyin shuru hakan yasa Momma samun ABUBAKAR tace kayi hakuri Abubakar kaddararku kenan ka tafi gida please and kayi ta addu'a, "ni ko nayi karfin halin kiran sunan shi Abubakar ina sonka, kuma bazan dena sonka ba har duniya ta nade"
Ammi na jana Ina tirjewa ina cewa no matter what circumstances, watarana zamu kasance tare, if not us toh our children inshaAllah one day! one day destiny will repeat it self" Ina kaiwa nan Abubakar ya juyo ya kalle ni cikin so da kauna yana hawaye, hannayensa sanye cikin aljihun wandon sa, yana tsaye yana kallon mu, wani irin karfin halin kwace hannu na nayi daga rikon da Ammi tai min na ruga aguje na rungume shi dukkanmu kuka mukeyi mai tsuma zuciya, wanda ko baka da tausayi kaganmu awannan halin dole ka tausaya mana, (Toh fah wayaga indiyawa, wannan soyayyah sai kace afilm😜😂)
"Akunnenshi na sake fada masa" kalmar da har yau take zuciyar mu kuma ada nayi tunanin saboda ita Abubakar ya hada ku aure ashe babu ruwansa, wannan duk ikon rabbi ne,wanda shi ya tsara komai""""
Ummi ta cigaba da cewa muna tsaye muna kuka Ammi ta sake zuwa ta raba mu ta tafi dani, wanda tun daga lokacin ban sake zuwa kaduna ba, " Ammi mutum ce wacce bata magana biyu kuma babu wanda ya isa ya tsallake doka idan ta kafashi, hakan yasa duk family sukai shuru da lamarin har aka daura aure na da Junaid muka zauna a Nijar (maradi) ban taba tunanin zanyi aure agarin ba," Junaid baisan Ina da wanda nake so ba, sai bayan auran mu" Amma dukda wulakancin danake shuka masa hakan bai hanashi yimin dukkan abinda yakamata yai min ba, abinci wannan Ina dashi lodi lodi a store Amma sai na ga daman dafawa, kuma idan na dafa iya cikina kawai nake mawa" aikin gida kuwa bansan dashi ba, har ya gaji ya samo yar aiki ita ke komai"
Muna haka ne Allah madaukakin sarki yabamu cikin Muhammad, Hakika babu irin rashin mutuncin da banyi ba akan sai na zubar da cikin......har piya piya nayi attempting sha amma Allah baiyi ba, nayi rugima iya rigima, watarana har katsina na gudo without his knowledge nazo na shedawa Ammi cewa Junaid dukana yakeyi, nahada karya da gaskiya,  but, to my own surprised ina gama koke koke na da maganganu na, sai naji Ammi tace idan kin gama tattaro kayanki kizo na kaiki park, ki koma dakinki....heeeeee ai ranar naci kuka wai Ammi dakanta ta mayar dani daki na ta kuma yimin kashedi akan ko so dari zan dawo gida haka zata maidoni so dari"
Ta barni ina ta faman kuka aikuwa ko da Abba ya dawo rashin mutunci nai tayi masa ranar dai ko runtsawa baiyi ba yaga aya akaina yasha wahalan zama dani, har na haifi Muhammad,  Allah kuma ya daura mun son Muhammad kaman raina, daga nan na samu Saifullah tun daga lokacin na canja halaye na saboda ganin Abba yasha wahala ya jigatu kuma yaki saki na sannan duk abinda nake mishi wlhy bai taba zuwa ya fadawa Ammi ba, asali ma nidai ban taba ganin mutum mai hakuri irin Abba ba" sai da mukayi shekara bakwai sannan Allah ya bamu wani cikin, "Cikin Jiddah" Hakika babu  irin gatan da Jiddah bata gani ba awajena da wajan Abba" tun tana ciki tun kafin asan mace zan haifa, dalili kuwa shine saboda na jima ban haihu ba kuma an cire rai da haihuwan"hakan yasa na koma *Jibiya* da  zama Mama tazo ta zauna dani har Allah ya sauke ni lafiya  (shine farkon labari part 1/2) na haufi Diya mace, taci sunan KULU wato:  * Hauwa'u Junaid*. kuma alokacin nayi matukar farin ciki saboda sunan mahaifiyar Abubakar ce shiyasa na kara karrama sunan na sanya mata * JIDDAH *

Ummi na kaiwa nan sai kawai sukaji muryar Daddy daga bakin kofa yana cewa sannan kuma nima nai miki takwara *Leemarh*
Duk suka waiga suna kallon kofar" Ummi tayi murmushi tace Kuma nagode sosai shiyasa nake so abani ita na tafi da ita katsina koba komai zata maye min gurbin Autana, dama itama autan ce" duk sukayi murmushi suka soma gaida Daddy"
Sa'annan Ummi ta cigaba da cewa:
* Hakika naga darasi acikin RAYUWAR mu kuma RAYUWAR JIDDAH wanda har yanzu darasin nake gani" tun farko da na sanar da Ammi muna tare da Abubakar da hakan bata faru ba, Ammi ita awajan ta batason tayi magana biyu sannan tana son hada zuri'a da Dan Aminiyarta, Amma action din da ta dauka lokacin is too hot, to the extend that yasa har yau tsoronta nakeji, shiyasa ko lokacin da tayi maganar auran Faisal da Jiddah na amince without knowing that Jiddah nada wanda take so" kunga kenan Ammi bata da laifi, sannan dukdama lokacin nayi abinda bai kamata ba, dukdama arashin sani nayi su, zuwa gidan saurayi, haduwa dashi awaje batareda sanin iyaye na ba" it's bad" sai gashi kuma Allah ya sake hada zuri'ar mu, gaskiya ina farin ciki sosai da faruwar wannan al'amarin.
*********
*Faisal yace Ummin mu bake kadai ba wollah harda mu ko Fatima yadan saci kallon Fatima dake gefensa, sannan ya cigaba da cewa Ummi badan abinda ya faru ba da bazan so Fatima ba, da bazan san tana existing acikin rayauwata ba" Ummi gaskiyar Al'amari na dade Ina son Jiddah, nadade Ina muradin auranta, na dade ina yiwa kaina tanadin rayuwa da ita, ga Muhammad Nan shine sheda na, Amma bayan na gano Jiddah tana da wanda take so sosai, hakan yasa na soma kokari ganin na samo mata abin kaunarta just to make my little girl happy nayi kokarin cire soyayyar ta araina, and thanks to Muhammad shi yayi introducing din Fatima awajena and daga baya dana zauna na fahimci wacece Fatima believe you me ayanzu haka babu kamarta acikin zuciyata" Jiddah kuma kallon kanwa nake mata"yadan kalli Jiddah da Fatima sannan yace bawai na fadi hakan don zumuncinku ya lalace bane, na fada ne saboda kusan abinda ya faru and ya rigada ya wuce yanzu gaba muke kallo kunaji na.
* Jiddah ta hararesa😏 playfully tace ai muma bamu ce maka zumuncin mu zai yanke ba, sai Fatima ta karbe da sauri tace toh akanme ma zumuncin zai yanke" saboda wannan karamin abun🤨 uhmmmmbta karashe maganar tana tura baki gaba.

Ummi ta kama dariya tana cewa ya kuke son tarun masa ne, ko dai maganar da yayi ce ta bata maku rai naga kowa yana kokarin fada masa bakar magana.

Duk suka fashe da dariya sannan Daddy yace to Alhamdulillah Allah yasa dai Abba ya amince da wannan hadin saboda na kosa Naga na aurar da yara nima girmana ya karu a idon society.....sai suka ji muryar Abba yana cewa to me zai hana kasancewar auran" nidai ba shaidan bane , Aure kuma kaman an daura ne inshallah......Jiddah da karfin hali ta tashi daga cinyar Ummi sai data fuskanci Alkibla (Gabas) tayi sujudur shukur sannan ta nufi inda Abbanta yake ta rungume shi tsam harda mishi light peg a kumatunsa, Abba ya rungumo ta shima yai mata kiss a forehead dinta yai murmushi mai kayatarwa yace Alhamdulillah Mamana yau tsahon kwana nawa kina fushi da Abban ki banga smiling dinki ba, kuma hakan yasa bana walwala, bana jin dadin abinda ya faru, sai yau kikamin smiling yanzu an dena jin haushinna Mamana andena fushi dani ko?
"Jiddah tayi karamar dariya ta  daga gira tana lumshe idanuwanta sannan ta kwanta a kirjinshi" Ummi tace lallai na yadda baki da kunya Jiddah"

Alokacin Momma ta shigo dakin tana ce wa akwai mara kunya irin ki ne, ke wani irin abune baki aikata ba zamanin baya akan soyayyar ku" Ummi ta sunne kai tayi shuru don har Allah batason ana maganar soyayyar ta da Abubakar agaban Abba sai taga kaman tana cimai fuska ne"

*Jiddah tace Momma what are we waiting for, let's go home and start preparing for the wedding please, am feeling much better now" "see" ta karashe maganar tana  straighting hannun ta, tana mika da kafa tana tafiya wai ita adole taji sauki* sannan ta dan kanne ido daya tace " Readers, nasan kuma kun matsu da ayi auran nan, tohm karku damu ni Jiddah Junaid zan gayyace ku inshallahu saboda kuma kuzo kudan daka rawar ki wannan gagarumin biki  🤗

Hafiz me zaiyi inba dariya ba, yace Hauwa'u you are so funny" babu inda zaki doctor baiyi discharging dinki ba koo, at least yakamata ki kara 2weeks a hospital saboda hankalin ki ya kwanta sosai" ya karashe maganar yana dariyar keta yana kallon Faisal" Faisal yace exactly bro in-law, kaman ka shiga raina"
shima yana fada yana dariya"

" Jiddah tayi pouting ta zumbure baki tana son tayi shagwaba adai dai lokacin Ammi suka shigo da Doctor ta ruga jikin Ammi tana kukan shagwaba uhm uhm uhm" Ammi"

Ammi tace ya ya akayi ne Auta" Jiddah tace wai wai yaya Hafiz wai baza'a sallame mu ba ?

Ammi tace injiwa yace mai ai yanzu kuwa ta waiga wajan likita tace likita jikata taji sauki maza a rubuta mata takardar sallama"

Jiddah ta waiga tanayiwa Hafiz da Faisal gwaliyooo, Ummi  kuwa tai mata dakuwa tace kaniyanki"

" Ai ba shiri ta boye bayan Ammi tana nonnoke wa ita ala dole batason fada"

Fatima da Leemarh kuwa babu abinda suke banda dariya, suka kama hannunta suka fita waje, suna kus kus ".

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

******Kalubale Gareku******* Lallai na sanya halayen characters na RAYUWAR JIDDAH akan autan ci da sangarci, hakika kalubale ne babba, saboda idan yakasan ce an sangarta yarinya ko yaro ko kuma  yana ganin ya taso shi kadai zaiyi duk abinda yake so to fah wani zubin matsala na faruwa zakaga sun kauce hanya saboda sangartasu da akeyi ba'asan kwabarsu idan sukayi ba daidai ba" duba da yanayin Ummi ta taso itama cikin so da kauna ganin ita din Auta ce, all her taught was za'ai mata abinda take so Amma hakan bai sa Ammi tayi mata abinda take so ba " kunga kenan abinda Ammi tayi shine ya dace, dukda kuwa ta tsananta sosai* sannan Jiddah,Fatima da Leemarh dukkansu su kadai suka taso a gidajan su ma'ana basa da yan uwa mata, Amma duk da haka, soyayyar da ake nuna musu da kuma ganin su kadai ne mata a houses dinsu da Autancin dake damunsu hakan baisa suna yin rashin kunya ba, kuma hakan baisa sun aikata abu mara kyau ba" toh daga karshe dai is better kawai idan zaka nunawa yaro so kai masa so daidai misali, kada ya kasance anuna musu soyayyah da son kudi da almubazzaranci na kudi dadai sauran abubuwa irin wanda yaro zai lalace" Allah yasa mufi karfin zuciyar mu, Allah yasa mu dace Amiin ya rabbi.

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
RAYUWAR JIDDAH FANs thank you for your support.

******************
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
Comment
Vote
Share

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now