"Dakin Mama ta shiga ta same ta zaune saman kujera hannunta rike da charbi tana lazimi, tace ah ah Fatima har kin dawo?
"Eh Mama Ina kwana"
"Lafiya lau ya jikin Jiddah"
Da sauki Mama"toh Allah ya bata lafiya, Jiya ai Ummi ta kirani da kanta tai min bayanin abinda ya faru"
"Fatima tace eh Momma ce dama tace ta kiraki tai miki bayani"

"Mama tace Amma dai abun baiyi dadi ba, Allah ya daidaita tsakaninsu"
"Amiin ya rabbi"Mama nida Yaya Faisal ne zai jira nayi wanka sai mu koma hospital din"
"Auu tohhh Yana Ina?
"Yana palour"
"Toh yi maza kiyi wankan ko, Bari na daura maku abinci sai ku tafi dashi Hospital din"
"Toh Mama"

Mama ta tashi ta shiga kitchen, dama tana da parboiled rice a fridge da pepper chicken, don haka kayan miya kawai tayi blanding nan da nan ta hada party jollop rice, ta gyara pepper chicken din, sannan tayi potato frittata, tayi packaging komai a warmers masu kyau da basket, sannan ta zuba mishi nashi daban, tana cikin aikin Fatima ta shigo tace wow Mama har kin gama"
Mama tace yes am done, Zo ki hada Chapman akwai komai da komai a fridge din dinning, kiyi sauri sai ki kai masa....ki hada da doughnuts din dayake microwave kinji.
"Fatima tace okay Mama thank you"
Mama ta wuce daki ta kwanta abinta.

Cikin 15min ta gama komai takai masa falo, inda ta iske shi yana kishingide idanunshi a rufe da alama bacci yakeyi, ta fara arranging tana gamawa tayi serving dinshi, sannan tace Yaya Faisal ka sauko kaci abinci kafin mu tafi, sai alokacin ya bude idanusa masu launin bacci ya sauke idanun akanta, baisan lokacin daya furta "MashaAllahu ahsanul khalikin"
Sanye take da lace yellow riga da skirt, shape din jikinta yayi matukar fitowa, dama Fatima akwai shape zan iya cewa shine kadai abinda zata nunawa Jiddah, kuma dukkansu bakake ne Amma dukda haka Jiddah ta fi haske da kyaun fata, uwa uba ta fita kyau nesa ba kusa ba,,, Fatima kuma tana da boyayyen hips wanda sai ta Sanya riga da skirt zaka hango zaunannun shape, shiyasa da dama bata sanya veil sai hijab sometimes Jiddah na yawan kiranta da Coca-Cola saboda jikinnata ya tafi kaman robar Coca-Cola ga tsayi ga shape....to haka ya zuba mata idanu, kawai yama kasa cewa komai har ta tsargu, tace Yaya Faisal lafiya.
"Faisal yace lafiya lau zauna muci abincin mana"
"Fatima tace ban karasa aiki ba aciki ka fara ci toh"
"Faisal yace no ki zauna muci, idan mun gama sai muje na taya ki aikin.
Haka kuwa akayi tana cin abincin ma bai kyaleta ba, sai faman kallonta yakeyi kaman zai cinye ta, yana ta santi, wai abincin yayi dadi, garnishing dinma yayi haka dai yaita surutunshi, bata ce mishi uffan ba har suka gama.

Ya tattara plates din ita kuma ta dauki coolers din yabi bayanta har kitchen, anan sukayi wanke wanke tare sai Fatima ta shiga ciki don dauko wani abu, Amma kafin  ta dawo har ya gyara kitchen tsab, Wanda ba karamin mamaki Fatima taji ba, ganin Namiji kaman Faisal, Mai aji, da kyau, ga kudi, ka takama, Amma  ya iya aiki kaman mace, ta sake duba gyaran da yayi tace kai Ina wannan gyaran ma yafi na wata macen, haka tai ta faman kallonshi sai yau taji yana burgeta, sai yau ta fara hango tsantsar kyan da Allah yai masa, sai yau ta soma wani kalan tunani, Wai dama ace har yanzu Yana sonta, dama wai ita batace bata sonshi ba, so take ta gwada shi, haka taita sake sake acikin ranta""" kujimun pha"""😂all of the sudden" har ta fola mai🤣

"30min sukayi suka isa hospital din,suka samu su Ummi,anan suka dire basket din abincin, Fatima tace"Ummi,Maama tana gaidaku tace wai ga abinci nan na kawo muku"
Ummi da Momma sukace toh mungode Fatima sannu kinji"

Fatima tashiga dakin sai ta iske Hafiz zaune, as usual tun jiya, ta girgiza kai tace Allah sarki Hafiz wai baije gida ba har yanzu, yana jiran ta farka, Allah mai iko, Allah nima ka bani masoyi wanda zai so ni fiye da yanda nake sonshi.
Jitayi kawai an amsa mata da Amiin ya rabbi" tayi saurin waigawa Jin muryar Faisal, batayi tsammanin maganar afili tayi ta ba, kunya ce ta kamata sai kawai tawuce wajan gadon Jiddah, ta samu waje ta zauna, shima dai zuwa yayi ya zauna kusa da ita, batareda ya kalle taba, yace da Hafiz, guy bakaje gida ba haryanzu?
"Hafiz yace yes banje ba Faisal, but na kira gida ance min komai lafiya lau, kasan shima Daddy baya Jin dadi, but har yanzu bai farka ba"
" Faisal yace ayyahhh Allah ya Basu lafiya dukkansu, Amiin Amiin"

Hafiz ya kalli Fatima datake ta faman sunne kai, kaman taga surukanta, yace Fatima lafiya dai?
" Fatima ta dago kai ta zare idanuwanta ta kalli Faisal da Hafiz, sannan ta girgiza kai kawai, daga bisani ta tashi tabar dakin, ta koma wajan su Momma"

Suna hospital din har yamma, Ummi ta shigo ta samu Hafiz tace , cikin murya mai taushi" Son bazakaje gida ba, ka kimtsa,kafin ta farka"kuma fah ko abinci baka ci ba, wani irin horo ne kakewa kanka Son"
Bari na zuba maka abinci kaci kafin ka tafi gida koh"
" Hafiz ya girgiza kai yace "Ummi kada ki damu, Ummi halin da Jiddah take ciki shine damuwa na yanzu, Ita kanta rabon ta da wanka tun jiya, rabon ta da abinci tun jiya, to ni kuma awa zanci abinci, in yi wanka, bayan Hauwa'un Hafiz tana kwance ba lafiya, bazan iya ba Ummi"

" Ummi ta dube shi da fuskar tausayi tace Allah sarki Ina maka fatan Alkairi Hafiz Allah ya barku tare da Jiddah,...har yau Ina gode ma Allah daya hadaka da Auta, saboda tun kafin ma nasan waye kai, hankali na ya kwanta dakai, kuma nasan zaka kula min da Auta na har iya karshen rayuwarku, Fatana daya Allah yasa Abbanta da Daddynku su amince da wannan hadin.

"Hafiz yace Amiin Amiin Ummi ki bani labarin soyayyar ku da Daddyna because naji anacewa kun shaku sosai kuma ni sheda ne saboda har yanzu bond din yana jikin ku, nagani azahiri Ummi " Ummi tayi murmushi kadan",sai ya sake gyara zama adai dai lokacin sauran samarin suka shigo Muhammad, Saifullah da Faisal sai Fatima gefenta Leemarh ce sai bayansu kuma Momma ce, sa'annan Ammi da Abba.
Hakika family din gwanin ban sha'awa, basu da wani damuwa ......Hafiz yace Leemarh waya kawo ki, da yamman nan.
"Leemarh tace Yanzu muka zo Yaya Hafiz"  " Hafiz yace ke da wa Leemarh?

"tare da su Mom da Daddy muke," MashaAllah Daddy ya samu sauki kenan cewar Hafiz Yana murna" Leemarh tace eh dazun nan fah ya farka, Amma koda aka fada masa kana hospital shine ya matsa wai akawo shi ya ganka"
"Hafiz ya mike tsaye Yana cewa muje naganshi Leemarh"

"Momma tace ah ah ba haka za'ayi ba,suna ina?
"Atakaice ta basu amsa tace suna waje, Mom ne ta hana su shigo saboda kada suyi causing confusion"

"Momma ta juya tace Subhanallah wani irin confusion kuma" Sai ta kalli Ammi wacce tai mata signal da idanu,"
Momma ta juya tace please Faisal, Muhammad kuje ku shigo dasu,ta fada batareda ta kalli Abba ba,
"Hakanan suka je suka shigo dasu,Mom ne da Daddy sai granny"suna shigowa Abba ya tashi zai bar dakin but, tuni Ammi ta dakatar dashi tace ya dawo ya zauna.

"Ba musu hakanan ya dawo ya zauna yana daddaure fuska.

"Ummi da Mom kuwa sai yau suka hadu, sai yau Mom taga Halimar Daddy, sai yau ta yadda lallai soyayyar su gaskiya ce, saboda a,azahiri dai Ummi doguwar mace ce, and kuma dai bawani tsantsar kyau take dashi ba,balle ace saboda kyau Daddy ke sonta hasalima she is black in completion irin chocolate dinnan hasken su daya da Jiddah, kuma kamar su daya da Jiddah", Amma tana da kyau irin na fulanin katsina tana da irin kyaun nan da kallo daya zakai mata ka hango shi."
"Mom ta kafe Ummi da idanu, itama dai Ummi haka tabi Mom da idanu....Mom gajerar mace ce mara tsayi, fara ce, fuskarta irin round dinnan ne, bata da wani dogon hanci hakazalika idanuwanta kana na ne" amma kuma idan ka ganta bazaka ce mata mummuna ba saboda she is average"
Ahankali Mom ta soma takawa zuwa inda Ummi take, ta kama hannunta tace Assalamualaikum Ummin Jiddah"
"Ummi da kyar ta dago kai, tayi smiling din dabaikai zuciyarta ba, tsabagen kishin Mom dataji, dukdama kallo daya tai mata taji ta shiga ranta, Amma daga baya data tuna ta auri abunda ta fi so duk duniya sai taji ba dadi,.....Mom ta katse mata tunani da cewa ya mai jiki Ummi?
"Ummi tace Alhamdulillah gatanan har yanzu bata farka ba"

"Toh Allah ya tashi kafadun ta"
"Allahumma Amiin"
Sa'annan shuru ya biyo baya"
"Dakin ma entirely akai shuru na yan dakiku kafin Ammi tai gyaran murya just to cut the silence tace:😘

******************
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Happy Sallah FANs
yaufah Autar mu zata farka, who's ready for her?
Nidai Diela can't wait to have her wallahi"🤭

ALKALAMIN DIELAIBRAHIM ✍️
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
Vote
Comment
Please

**********

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now