"Ko da taga yana kallon window din sai taja baya ahankali ta kwashe duwatsun tayi hanyar fita, sai taci karo da Momma tsaye abakin kofa, da alama da jima awajan tana kallonta, sosai ta tsorata Amma sai ta wayance tace, ahhh Momma na kece!
"Momma shuru ba answer sai sakon harara "Jiddah tayi magana har ta gaji, sai da Momma ta ga dama sannan tace zaki wuce kije ki same shi ko saina bata miki rai"
"Jiddah tayi saurin boye duwatsun ta kutsa ta gefen Momma ta wuce"
Momma ta girgiza kai, ita kanta abinda taga Jiddah nayi ya bata mamaki, Jiddah kaman wata karamar yarinya dai, ta kalli dakinnata dayake gyare tsab sai faman kanshin turare yake yi,as usual tace acikin ranta kullin dakinnan agyare babu ko kaya guda daya,komai yana ajiye a muhallinsa,Jiddah ce fah, ta juya tabar dakin.

...Yana nan tsaye Yana ta waige waige yaji an wurgo masa ta bayan shi, da sauri ya waiga amma wayam babu kowa, Hafiz dai ya kulu , kaman ya koma cikin mota Amma sai ya fara zagaya motar amma baiga kowa ba"

Ashe ta kasan motar ta hango kafafunshi yana shirin zagayowa, sai tayi saurin zagayawa itama Amma aduke tayanda bazai gane ba, har tazo inda bata iya ganin kafafun nashi sai ta tashi taga baya kallon wajan sai ta wurga yana juyowa ta duka Amma abinda bata sani ba shine ya ga shatin veil dinta, hakan yasa ya zagaya ahankali har ya iso bayanta with out her knowledge ta tashi, tana shirin wurga wani sai taga baya Nan, waige waige tafarayi har tazo wajan motar shi ta bude ta leka baya ciki tana dago kai ta hada ido dashi, gashi ta bude tafin hannunta ana ganin duwatsun, zare ido tayi sai tayi saurin jefar da duwatsun ta fara ja da baya.

"Hafiz yace karki kara taku daya daga inda kike,hakannan ta koma ta tsaya tana watsa da yatsun hannunta ta kasa kallon shi, ahankali ya soma takowa har inda take tsaye, har ya matso kusa da ita ya tsura mata idanu kaman me neman wani abu a fuskar ta, cikin sanyayyar murya wacce Jiddah kadai yake mawa yace"HAUWA'U"
"Tuni Jiddah ta rude tayi saurin rufe idanunta zuciyarta na dukan uku, ita dai tasan yanzu bata tsoron shi, kawai dai tsokanan datayi ne take tsoro kada yayi punishing dinta gashi dama ance sojoji idan akai masu laifi, frog jump suke sanya mutane"
Tana nan tsaye dabara ta fado mata tayi saurin bude ido da kyar ta kalle shi sai ta saki murmushi 😁 sannan tace Uhmm Yaya Hafiz yaushe kazo ashe kaine tanayi tana rawa da kafarta tana zare takalmi, Duk Yana kallon ta, sosai ta soma bashi dariya acikin zuciyarshi....a fili kuma yayi frouning fuskarshi ya koma ya jingina da motar shi yayi folding hannunshi sannan yace" Kince nazo, and gani nazo ya akayi?
Jiddah taji wani sanyi aranta Jin ya canja topic din, atunaninta ya hakura ne ta juyo tana washe baki to which kana nan dimples dinta suka baiyana, sai kuma ta Bata rai ta turo baki gaba tana cewa, ni..... ni..... ai dama Ina so ne naganka, yau kwana nawa ban ganka ba "Mi Alma"
Yaso ya biye mata Amma sai ya sake daure fuska yace, do you mean ba wani abu serious bane yasa kika kira ni Hauwa'u"
Jiddah ta zare ido tace kana nufin missing dinka ba abu mai muhimmanci bane dazaisa naji Ina son ganinka"ta kura masa idanu kuwa"
"Still Hafiz bai sauka ba ya daga mata kafada ko ajikinshi sannan ya duba wrist watch dinshi yana cewa,Shine danazo ai kike ta wurga min stones "Idan you are serious about it ai Ina zuwa zaki fito kizo ki ganni"ya fada cikin sigar shagwaba, any way ni zan koma gida bye ki gaishar min da Momma"
Har ya juya zai shiga mota tayi saurin binshi, tana langwabar dakai ta fara bashi hakuri" Amma Hafiz yayi kaman baisan tanayi ba, sai da yadau tsahon minti biyu kafin yace idan kina so na hakura sai kinyi "frog jump"
"Tashin hankali awajan Jiddah kaman me, ruwan masifa taso yi masa, Amma sanin darajar Hafiz da Kuma matsayin da zuciyarta ta bashi shiyasa tayi shuru da bakinta, sannan tasan laifinta ne don haka dole ta karbi punishment....ta soma bashi hakuri Amma ya kafe akan sai tayi frog jump"(Hafiz na son gwadata yaga shin zatayi idan ya sanyata)"

Hakannan tayi fuskar tausayi baiwar Allah ta duka zata fara kenan Hafiz ya taso shima ya tsugunna agabanta hade da rike hannayenta wanda ta kama kunnenta dashi....ya sanya idanuwanshi cikin nata yana kallon kwayar idon ta, yace cikin sanyayyar muryarshi mai zaki
" Lahhhhh, ban Isa na sanya sarauniyar da take mulki acikin zuciyar Hafiz Abubakar ba"ban isa nayi fushi da Hauwa'u ba infact Hauwa'u bata laifi awajan Hafiz, ko tayi laifin ma Hafiz mai Afuwa ne agareta, ako dayaushe Hafiz ya yafe mata laifin da tayi da kuma wanda zatayi nan gaba"Hauwa'un Hafiz"
"Jiddah ta saki baki tana kallon yadda Hafiz ke ta zayyano kalamai, sosai tayi farin ciki dajin abinda ya fada, ahankali ta sanya hannu ta rufe idanuwanta ta kasa ce mishi komai ta tashi  zata shige cikin gida, sai datayi nisa sannan juyo tace "You look good Yaya Hafiz"and nagode dakamin afuwa" tana kaiwa nan ta shige gida da sauri abinta.
"Hafiz yai murmushi ya shiga mota, ya sauke ajiyar zuciya mai dadi yace  Alhamdulillah nima nayi farin ciki dana ganki Hauwa'u"My day will never be dull when you are with me".....ya cigaba da tunanin yadda Jiddah take aiwatar da soyayyar ta gareshi, Hakika bata taba fitowa ta fada masa tana son sa ba, Amma action dinta ya nuna, moreover tanayin soyayyar cikin kunya da tsari babu rawar jiki irin ta yan matan yanzu".... HAUWA'U JIDDAH JUNAID Allah ya bani ke amatsayin mata kuma uwar 'ya'ya na" Yana kaiwa nan  yabarbar gidan.

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now