Ranar Alhamis
Thursday itace ranar dasu Hafiz zasu koma hospital kuma same date as Jiddah.

In the morning Jiddah ta shirya cikin shiga ta Pakistan kayan India mai tsada wanda Yaya Faisal ya siya mata, Riga da wando ne milk and black color Yana da adon stone golden, ga cover black na kayan, veil din kuwa daure gashin kanta tayi da band sannan tayi rolling da veil din ta fito sak India saboda doguwar fuskar dake gareta amma black in completion, Faisal kallonta kawai yakeyi yana admiring dinta a zuciya har saida muhammad ya dafa shi yana cewa "be a man bro" Faisal ya daka masa duka suna dariya sannan suka bar wajan Momma da Jiddah na biye dasu.
Suna zuwa hospital din suka iske layi, appointment letter suka duba sai suka ga karfe 12pm Dr.Rahul Jay zai gansu,so suna da sauran 2hours, don haka Faisal and co. suka fita waje while Momma da Jiddah suka samu waje kasan bishiya akwai kujeru anan suka zauna suna hira abinsu.
************
10am Hafiz da granny suka iso hospital din dukda cewa sai 1pm zasu ga doctor amma is better su iso da wuri.
Hafiz yace Honey idan Kika shiga cikin reception zaki gaji gwanda ki zauna a waje mai fresh air, muje wajan bishiyar cen akwai kujeru awajan.
Granny tace okay muje, dayake wajan da dan girma hakan yasa Hafiz bai waiga ganin mutanen dake zazzaune a wajan ba, ya sama ma granny waje ta zauna sai yace zanje wajan ogan mu yana nema na, Amma 12pm zan dawo inshallah
Granny tace okay toh sai ka dawo "
"Honey kina bukatar wani abu ne kafin na tafi" karaf wannan statement din ya shiga kunnen Jiddah, Sanin cewa da tayi magana Momma zata iya yimata fada sai tayi shuru Amma hancinta ya soma jiyo mata kanshin turaren Hafiz Wanda ko kana nesa dashi ne sai kaji wannan kanshin., Jiddah cikin wayo tace Momma baki ga wani dan saurayi fari awajan nan ba?
Momma ta dan waiga hagu da dama, gabas da yamma alokacin Hafiz yabar wajan granny ya bada baya yana tafiya, Momma tace aa Jiddah mutanen dake wajan nan ma duk Mata ne sai wasu yara daga cen gefe"
Jiddah ta gyada kai acikin ranta tace maybe scents din turaren ne kawai to me ma zai kawo Hafiz nan, lokaci daya ta share maganar ta cigaba da yiwa Momma surutu.
Granny na zaune ita kadai tana facing din su Momma ganin zaman kadaici ya isheta hakan yasa ta tashi ta nufi wajan su Momma tai masu sallama cikin girmamawa.
"Jiddah taso dauko muryar tsohuwar Amma ta kasa sai ta daga kai kaman tana ganinta Amma shadow kawai take gani, ji tayi tsohuwar tace "Bayin Allah sannunku dai, nace zaman kadaici ne ya ishe ni kuma naga kaman kuma yan nigeria ne"
Momma tai murmushi tace kwarai kuwa mama kema yar Nigeria ce?
Granny tace eh nazo ganin likita ne"
Momma tace Allah sarki muma likita muka zo gani 'ya tace za aiwa aikin idanu"
Sai alokacin granny ta kare wa Jiddah kallo sosai taso ganeta amma ta rasa a ina ta santa sai kawai ta samu waje kusa da momma ta zauna tana cewa bata gani ne?
Momma tace wlhy matsala idan ya samu shine akace idan muka zo nan mukaga Dr. Rahul Jay inshallah zata warke.
Granny"tace Allah sarki to Allah yasa ayi a sa'a, miye sunanki 'yar nan?
Jiddah tace "Hauwa'u"
Granny"Lahh nikam bake bace kawar Lema wacce kika zo gaishe ni a kaduna?
Kut! Kada kuso kuji yadda gaban Jiddah ya fadi jin ta samu daya daga cikin family din Hafiz" tace cikin murnarta  granny nice wlhy"kiyi hakuri na dau murya amma nakasa tuna inda nasan muryar gashi babu ido da na gane ki"
Granny tace ayya babu komai takwara, ke kuma haka abu ya kasance makanta Hauwa'u, to Allah yasa ayi aikin lafiya, Allah ya baki lafiyar ido"
Duk suka amsa da Ameen Ameen.
Momma tace Jiddah kin santa ashe?
Jiddah tace Momma, grandma din Hafiz Abubakar ce tana fada tana wasa da yatsun hannunta,
Momma sosai abin ya bata mamaki to kenan Jiddah har tayi sabo da Hafiz to which har ta iya zuwa gidansu batareda saninta ba"
Kamar JIDDAH ta dago inda Momma ta dosa, sai tace Momma watarana ne a base, Nan take Jiddah ta baiwa Momma labarin yadda haduwar su da granny da Leemarh ya kasance"
granny ma tace ashe ku ba kawaye bane, Ashe Hafiz kika sani,
Jiddah tace ehh Amma shima ogan mu ne a asibiti inda nayi practical.
Sosai hankalin momma ya kwanta tayi hamdala acikin ranta dama tasan Jiddah bazata taba aikata wani abu batareda saninta ba don tayi trusting dinta fiye da tunanin mai karatu.
Momma tace MashaAllah Mama Ina jikanki Hafiz?
granny tace call me with granny shi kowa ke kirana.
Momma tace alright granny!
granny tace Hafiz yanzu yabar nan ai tare muke ya danje wani waje ne Amma bazai jima ba.
"Momma ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya hade da kallon Jiddah wacce ta kasa kunne tana sauraron su, hakika Jiddah tayi matukar farin ciki dajin haka Ashe dai zuciyar ta batai mata karya ba, Ashe scents din turarenshi ta jiyo,ashe da akwai ranar da zata kara ganin muradin ranta wayyo Allah ina ma zata iya data rungume Momma da granny tsabar farincikin da take ciki ayanzu to which smiling kawai takeyi tana tunanin inshallah ta kusan ganin Hafiz"
Momma suka cigaba da hira da granny saboda bata son ta shiga maganar yaran ta fitoso granny taji komai daga bakin yaran don haka ta canja topic conversation suna ta hira abinsu, Jiddah kuwa hankalinta ya tashi ta kosa taji ance ga Hafiz ya dawo har 11:50 tayi lokacin su Faisal suka dawo sannan Momma ta amshi number din granny sukai mata sallama sannan suka shiga wajan doctor.
Suna nan zaune misalin karfe 12:30 kafin afara aikin Jiddah tace tana jin fitsari, Dr.Rahul Jay yace Momma ta raka ta toilet, suka fita, Bayan ta fito daga toilet dinne Jiddah bataga momma awajan ba haka ta fara lalube ga mutane awajan batareda saninta ba taci karo da mutum sai jinta tayi kawai a kirjinsa ga wani irin shock daya shiga jikinsu moreover kanshin turaren shi kadai ya isa ta gane cewa Hafiz ne.
Da kyar ta dawo hayyacinta ta matsa baya tana saukar da numfashi ahankali tayi kasa da kanta azatonta Hafiz bazai ganeta ba......Amma to her own surprise sai taji miryarshi na rawa alokacin dayake kiran sunanta
"HAUWA'U JIDDAH JUNAID"
dago kai tayi amma bata iya ganinsa idanuwanta suka soma zubar da kwalla in such a way that bazaka gane hawaye takeyi ba, "Hawaye farin ciki Jiddah takeyi, wlhy ji takeyi kaman ta ruga ta rungume shi tsabar son da take masa.
Inaaaa ae shima Hafiz bai san lokacin daya matsa kusa da ita ba atunaninsa tana ganinsa, yace "HAUWA'U" kimin magana mana,Jin tayi shuru sai ya cigaba kawai dacewa, Hauwa'u I waited for you so long on that very day,sai kuma ya bata rai kaman zaiyi kuka yace "and ke kuma baki je wajan ba ranar ko,I knew it nasan baki karanta letters dina ba" Amma don't worry Hauwa'u am not angry with you anymore, Alhamdulillah tunda na samu na ganki Hauwa'u"bazaki gane yadda nakeji ba ayanzu Alhamdulillah Hauwa'u don Allah kar ki kara yin nesa dani! "Hauwa'u say something please" Adai dai lokacin Momma ta karaso tana cewa Jiddah where have you been, Ina ta nemanki, me ya kawo ki nan kinsan ba gani kike ba!
"Hafiz ya razana dajin kalmar ba gani kike ba"ya sake kallon kyawawan idanun Hauwa'u" sai alokacin ya lura da wani farin Abu cikin kwayar idanta wajan black dinnan, idan ba ka lura ba wlhy zaka dauka Jiddah tana gani"
Hafiz was very shocked by hearing that,to which ya tsaya a tsaye bai ma san sanda suka bar wajan ba Jiddah ma kasa magana tayi saboda ta rasa yadda zatai masa bayani sai kawai tabi Momma suka wuce, sai da suka wuce ne Hafiz ya dawo daga trance din daya shiga yana ta dube dube Amma bai gansu ba.(yaga samu yaga rashi)
Ya murza idanuwanshi ya bude ahankali ya soma cewa kodai ba Hauwa'u na gani ba gizo take min, yana nan tsaye granny ta iso wajan sa tana cewa Dr. yace mu kara jira nan da 2pm bai gama ba....Hafiz yace okay to muje koh....suna cikin tafiya ne granny tace Hafiz duniya abin tsoro ne!
Hafiz yace meya faru Honey?
granny tace Ina yarinyar nan da tazo gidanmu Leemarh ta kawota wajena ta gaisheni, Hauwa'u"
Hafiz ya amsa surprisingly Yana cewa na gane ta me kika gani Honey?
granny ta cigaba da cewa wlhy naganta ne dazu bayan ka tafi dinnan, ta makance fah Kuma duka idanun biyu bata gani.
"Hafiz ya kalli granny da mamaki kaman baisani ba "yace subhanallah granny da gaske ta makance wai"
granny tace eh fah tana kokarin gyara zama tana cewa ai saika ganta ma abin zai kara baka mamaki, ai Ina fadama ka yarinyar nan gata lafiya lau bazaka taba cewa ta makance ba gashi Allah ya taimaketa iyayenta nada Hali tunda yanzu aiki za'ai Mata,,nidai fatana ma Allah yasa ayi a sa'a ta warke.......granny tai ta zuba masa surutu batasan cewa Hafiz baya tare da ita ba, ya fada zurfin tunanin Hauwa'u dukda baisan abinda yasa ta makance ba Amma tausayinta ya shiga ranshi sosai samun waje yayi kusa da granny ya zauna suna jiran Dr.Rahul Jay.
Suna nan zaune su Momma da Faisal suka zauna,Sosai Faisal ya tsurawa Hafiz idanu yace acikin ranshi "shakka babu wannan Commander Hafiz Abubakar ne to Amma me yake yi anan, ko yazo wajan Jiddah ne yana ta tunani daga karshe ma ya koma Hira da Muhammad har yana fada masa cewa ga Hafiz wanda Jiddah take so.
Muhammad yaso zuwa ya samu Hafiz Amma Faisal ya dakatar dashi da cewa ka jira mugani ko wajanta yazo.
Tsahon awa daya 2pm Dr.Rahul ya fito ya kira su Momma gaba daya suka shiga ciki, sai da ya zauna kafin yace mun gama mata experiment din yanzu sai dai mu saurari outcome of the result nan da kwana uku zuwa hudu kafin mu bude idon.
Momma tace to ya za'ayi idan zata ci abinci ko wani abu?
Dr.Rahul yace yes zata iyayin komai Amma karku yadda ruwa ya taba fuskarta sannan kusan irin food din da zaku rinka bata,wanda zai kara mata karfin ido, yanzu Ina da appointment idan na gama zamu hadu anjima.

Alokacin itama granny akayi mata nata aikin amma nata kwana daya ne, Hafiz na zaune a waje Yana kallon su Faisal suna Shiga dakin da Jiddah take ciki one after the other, lokaci daya yaji yana son ganin halin da take ciki don haka ya tashi ya nufi wajan sallama yai masu sannan ya mikawa su Faisal hannu suka gaisa, sai kuma ya rasa abin cewa, Momma kallo daya tayi masa ta gane shi, ahankali ta kira sunansa cikin murya mai dadi tace "Hafiz"
Da mamaki ya dago kai, yace na'am Momma ina yini"
Lafiya lau ta amsa masa cikin fara'a sannan tace kana son ganin Jiddah ne?
Ya gyada kai cike da kunya, sai tace zaka iya shiga tace bacci take ji Amma ban sani ba ko ta fara"
Yace okay Momma nagode ya fada yana tafiya kofar dakin ahankali ya soma turawa ya shiga.

*************

Vote
Comment

RAYUWAR JIDDAH ✔Donde viven las historias. Descúbrelo ahora