Aranar kuwa aka fara daurata akan medications cikin ikon Allah kuma headache din yayi sauki sai idanun da suke yawan mata ciwo, tsahon sati uku sannan Dr.majdeed ya kara dubata, kuma yaga ana samun improvement saboda hawan jinin yana sauka,dukda baida tabbacin dawowar ganin nata amma yaji dadi ganin tana samun sauki,hakan yasa yayi discharging dinsu akan zai ringa zuwa har gida yana dubata sannan maganin ciwon idan zasu cigaba da anfani dashi ne har sai anga alamun sauki.

***********
Zuwa wannan lokacin Jiddah ta fara sabawa da sabon rayuwarta ta makanta saboda she is partially blind but, she can see only shadow"Inuwa take iya gani, kullin tana makale da Momma idan kuwa Ummi tazo ta rinka yi mata shagwaba iri iri kala kala, har sometimes"Abba nacewa Mamana wannan ciwon baisa kin natsu ba sai ma shegantakar taki ta karu over" Don kuwa Jiddah ba kowa ta kyale ba wajan shagwaba da sangarci, su ko suna yi mata saboda basu ganin laifinta na  "Mama tace ooooo Jiddodooo ai Autace😁 Kuma Auta bata laifi"
niko nace kudai cigaba da sangartata.😜
*****
Bari mu waiwayo bangaren
Hafiz Abubakar a qasar Pakistan suna cikin sahara suna ta faman aiki.

Zaune yake a wata rumfar su da suke kafawa mai kama da bukkan fulani 😁Amma tasu ta Yan gayu ce😂 cikin runfar babu komai sai katifu guda hudu, hudu akowacce rumfa, katifun an shinfida fararan bedsheets da pillow case, sai bag dinsu da kowa ya ajiye a gefen katifar sa, abindai achan achan gwanin ban sha'awa,Hafiz Abubakar yana kishingide hannunsa rike da phone dinsa dukdama dokan forces ne idan sukaje mission to babu wanda zaiyi anfani da waya musamman ta wuraren sahara, har sai sun gama sun koma gida kafinnan, to amma dayake Hafiz kam shi oga ne, sai yayi dabara ya cire SIM card din, sai ya kunna wayar kawai, kallo daya zakai masa alokacin kayi zaton wani important abu yakeyi da phone din,Wai ashe hotunan Jiddahn sa😍 yake kallo, Hafiz dukda yawan aikin da suke dashi hakan baya hana ya ware specific time don zama ya kalli pictures din Hauwa'u, yana missing dinta sosai, jira yakeyi su karasa mission dinsu ya koma ya cigaba da neman ta....Yana nan zaune bayanshi colleagues dinshi ne su uku suna ta faman hira, sai yaji suna cewa naji wani circular fah oga yace dole zamu shiga India saboda nanma wani aikin zamuyi.....Hafiz ranshi ya baci dajin maganar shikam gaba daya hankalinshi ba anan yake ba yana Nigerian so yake ya koma yaga Hauwa'u don baisan wani hali take ciki ba kuma baisan yaya matsayin soyayyar su take ba moreover he missed her characters.
Tashi yayi yabar wajan don Allah yaji ya gani bayason irin wannan maganan yanzu, shifah dama labari ne akan Jiddah to dayafi kowa son sauraron labarin😉
Samun wani fancy chair yayi ya zauna yana maida nishi ahankali, illai kuwa yana nan zaune saiga ogan yazo wajan suka gaisa lafiya lau sai ogan yake cewa Hafiz  meyasa kwana kinnan mood dinka is dull to which har yasa dole naji Ina son nayi maka magana yace Hafiz what's wrong with you this days kwata kwata baka son aikin da mukeyi"
Hafiz ya girgiza kai oga kayi observing kenan(Hafiz ya fadi haka ne saboda tsakanin su babu boye boye 5&6 ne🤗)
Ogan yace ofcux I observed you Hafiz karka manta da idan akaje mission kaine kan gaba akomai ko da kuwa ba kaine commander na squad din ba, Hafiz nasan ko kaiwaye shiyasa suddenly na fahimci kaman kana da damuwa,tunda mukazo qasar nan baka walwala, though kai baka cika hira da mutane ba "wannan na maka uzuri" Amma me, ka dena yin aiki yanda yakamata why Hafiz?
Hafiz ya dan gyara zaman sa yana kallon ogan yace Oga Ina tunanin gida ne Family na am just missing them.....
Ogan yace Ohh I see, to Amma ai ba kai kadai kabar iyali ba koh, wasu ma da auran su kuma haka suka bar iyalan suka taho and this is not the first time daka taba barin family ka tafi waje mai nisa kayi wanda yafi wannan so what's the essence of shiga damuwa please try and focus on your work, in banda abinka Com.Hafiz duka kwana nawa ya rage mana....
Hafiz ya gingina kai alamar maganar ta shige shi dinnan, yace zan yi kokari Oga, naji coursemate na cewa zamuje india?
Ohhhhh kamaga na sha'afah wallahi, zamuje India akwai aikin da zamuyi Amma duka bazai wuce 1month ba saboda zamu halarcci taron sojojin India ne, ana masu karin rank ne and AVM.Ibrahim Kaura yace idan muna da time zamu iya zuwa, ka shirya ka kuma fadawa sauran.
Okay sir.
Ya tafi yabar Hafiz zaune yana ta bata rai shi ala dole bai maga anfanin zuwa Indian ba, saboda bawai yazama dole suje bane, ranar haka sukayi ta aiki batareda yayiwa kowa magana ba.
________2 weeks later_____________
India
Filin taron sojojin India, Lallai taro yayi taro to which baka ma iya gane wanda yake gabanka saboda tsabagen cika da akayi, ana ta Kira kirayen sojoji ana masu karin rank, ni kam naita wulga idanuwa ko zan hango Hafiz Abubakar Amma ko keyarsa ban gani ba......cen na hango shi cikin jerin sojojin Nigerian bangaren Airforce Base, yana gaba gaba, sanye yake da kakinsu na sojojin Airforce dark blue uniform yai mashi kyau fiye da tunanin mai karatu, aka gama taro suna ta faman gaisawa da manyan mutane awajan, lallai sojojin India sun mutuntasu sosai sun kararrama su don har masauki suka basu...ko da Hafiz ya koma daki kulle dakin yayi dama shi kadai ne kuma ya gaji da hayaniya intashi ne ma baiso yaje taron ba don sai da oga ya takura ma rayuwarsa yasanya sa dole sai yaje, yana kwance saman gado ya daga wayar sa ya lalubo number Daddy yayi dialing, ringing daya aka daga...cen cikin wayar akace Baban mom, tun da kuka tafi nake kiran contact dinka baya shiga, ni nama manta kuna kashe SIMcard.
Hafiz yadan shafa suman shi, yace Daddy ai kashe wayar mukeyi nima naso yin waya daku wlhy, and yanzun ma muna India ne munzo wani taro Amma zuwa  jibi inshaAllah jirgin mu zai sauka a nigeria.
Daddy yace India?me kukeyi acen toh?
Daddy mun halarcci wani taro ne na soldiers and successfully aka gama taron.
Okay okay, yauwa gwanda ma da ka kirani son, dama granny dinka zata zo India ganin likitan ta, saboda lokacin komawa yayi so why not ka jira tazo idan ta gama sai ku dawo tare!
Hafiz yayi shuru Jin and kara Masa wani nauyi, yace Daddy ba damuwa yaushe zata zo ne?
Jibi flight dinsu zai tashi inshallah
Okay tohm Allah ya kawo ta lafiya, Ameen Daddy ya amsa.
Suka koma hirar su ta Uba da Da.
************
Katsina state
Barhim Estate

Uhm uhm uhm Momma ni bana so naje India wlhy, ba Dr. Majdeed yace zan samu sauki ba?
Ooooo Jiddah me yasa kike da rigima ne, tun jiya kike ta faman nanata abu daya "ke bazaki India ba" to ki fadamin zamu zuba ido ne mu barki abin yayi girma, kinaji Dr. yace yanzu kin samu sauki saura a fara treating eyes dinki and the best solution is gwanda akai ki India, har bamu address din Dr.  da zamu gani yayi, amma kina nan kina ta Mana rigima bakyason ki warke ko!Momma ke ta fada tana gamawa ta tashi tabar Jiddah awajan kwance.
Kafin Jiddah ta tashi tabi Momma, taji wayar ta na kara gashi babu kowa awajan dazai iya daga mata, haka ta rarrafa ta nufi inda wayar take ta soma guessing yanda zatayi answering call din, Momma ta labe tana kallon ta, sosai ta bata tausayi yadda taga tana ta shan wahala har call din ya tsinke, aka sake bugowa har sau uku kafin ta samu ta daga., Momma ta zubar da kwalla ta juya tabar wajan tana cewa ai gwara ki wahala kisan rashin ido babu dadi, in banda Jiddah ma ana nema mata sauki amma ita ba wannan take dubawa ba.

Jiddah ko tana ansa wayar taji muryar Fatima, tayi murmushi tace Besty na ya kike?
Fatima Ina lafiya Jiddah ya jikin ya idan?
Alhamdulillah"da sauki besty"
"To Allah ya kara sauki"
"Ameen besty"
Fatima tace gobe zamuzo katsina da Mama.
Jiddah ta buga tsalle tana murna tana cewa beb are you serious?
"Yes I am Jiddah, Yakamata mu zo mu duba ki, and school are resuming in 2weeks,yakamata muyi magana yadda abin zai kasance because bana so kiyi asarar karatunki Jiddah"
Jiddah tace alright Allah ya kawo ku lafiya"
"Ameen"bye Mama na kirana I'll call you later.
Okay bye, tana aje wayar ta tashi ta fara tafiya kamar mai sanda ahaka ta Isa dakin Momma tana kiranta ahankali har ta isa wajanta, ta fara bata hakuri da kyar Momma ta hakura.
Washegari Fatima tazo murna wajan Jiddah kaman me, Fatima ko tasha kuka ganin yadda idanuwan Jiddarhn ta ya koma.
Kwanan su uku suka koma kd, the following day Faisal da Muhammad suka fara processing tafiyar Jiddah India, 2days suka gama komai online har inda zasu sauka sun biya rent, kuma sun tura ma Dr. da zasu gani Email, yanzu kawai tafiya ya rage inda Faisal, Muhammad, Momma and Jiddah ne zasu.
Ranar asabar flight din ya tashi, suka sauka a India, so ranar Sunday Basu fita ba saboda weekend ne sai Monday suka shirya suka tafi Hospital din.
Dayake suna da appointment da Dr. din hakan yasa suna zuwa time nayi suka shiga sun jima aciki like 2hours suna ciki yana duba idanun nata, sannan yai masu bayanin aiki zai mata, ayanzu ranar aikin kawai zasu sanya idan sun shirya sai su zo ayi mata.
Sun ji dadi sosai, sannan sukace mashi cikin week din suke son ayi mata,aranar doctor yai masu signing ya basu date and time din dazasu zo, sannan sukai mashi godiya suka tafi.

**********
Ma'assalam 👏

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now