Ranar Momma bata kula Ummi da Ammi ba har Ummi ta gama zaman ta Saif yazo ya dauke ta suka koma gida.
After 2days
Jiddah na kwance a cinyar Momma tana kallon T.V, afalon Ammi,
Saiga Ammi ta fito daga daki ta iske su zaune a palour tace ahhh Yar lelen Momma dadin cinya ake sha yau?
Jiddah ta tashi da murna ta nufi wajan Ammi tana cewa Ammi dama ke nake jira wlhy.
Toh gani Jiddodooo yar Momma ya akayi ne?
Ammi fura nake so na dakan hannu irin wanda kikeyi dinnan.
Ammi tace tohhhhh yau kuma rigimar ta wajan fura ya nufa.
Jiddah ta gyada kai kaman wata karamar yarinya.
Ammi tace toh bari sai na shirya zan miki saboda na dade banyi daka ba.
Jiddah ta daka tsalle tace yaaaayyyyy my best granny harda rungume ta.....sai taji Ammi tace
Jiddah ya kamata kema ki koya dakan furar ki ringa yiwa mijinki tunda ankusan maki aure.
" Jiddah ta tashi daga rungumar datai wa Ammi tace Aure kuma Ammi....wa zan aura?ni da ma nake karatu yanzu wani aure zanyi!
Ammi tace au wai Momma kuna nufin har yanzu baku sanar da yaran nan ba, ke Jiddah ance maki aure yana hana karatu ne kajimin iyayi irin naku na yan boko""and ke kuma Momma kun dauki magana ta da wasa kenan shiyasa baku sanar dasu ba koh" ta dubi Jiddah tace ke je kira min Yayanki Faisal.
Jiddah ta tafi zata kira faisal, dukdama ta kasa kwantar da hankalinta akan maganar data ji, bata jima ba suka dawo da Faisal.
Ammi tace zauna Faisal, kema Jiddah zauna.
Momma na kallon ta batace mata komai ba sanin halin Ammi idan ta kafe akan abu to babu wanda ya isa ya canja.

Ammi tace Faisal kana da wacce kake so ne?
Faisal yayi mamakin tambayar Ammi, wanda yaji tambayar kaman daga sama lokaci daya ya dago kai ya dubi Ammi,
Ammi tace yas tell me, kana da wacce kake so ne?
Faisal ya girgiza kai saboda ya rasa me zai ce lallai yana da wacce yake so, bakowa bace illah Jiddah kuma ita bata sonsa, beside shi son maso wani yakeyi tunda yaji kishin kishin awajan momma cewa Jiddah tana son wani dukdama baiyi wani bincike akan maganar ba....."Ammi ta katse shi da cewa, toh tunda baka da wacce kake so, Ni amatsayi na na kakarka wacce na isa dakai nayi maka mata kuma matar nan ba kowa bace illah Jiddah kanwarka.

Kut!!!ai karku so kuka yadda Jiddah take zaro idanu jin maganar Ammi, to which brain dinta ma ya kasa daukar maganar, bin Faisal kawai takeyi da kallo at thesame time Hafiz na fado mata arai tana tuna irin son da take mashi, sannan tayi alkawarin zata jira har zuwa lokacin dazai neme ta.....Amma all of the sudden Ammi ta shigo da wata magana, Wai Yaya Faisal zata aura.........
Faisal kuwa Jin maganar yayi kaman saukar aradu acikin kwanyarsa, ya kalli Ammi aranshi yace lallai idan dagaske kunnuwanshi sun jiyo abinda Ammi tace toh cewa tayi taba shi mata, kuma matar nan ba kowa bace illah Jiddansa, kanwarsa, abin qaunarsa.......Lallai ya rasa farin ciki zaiyi ko bakin ciki saboda yasan dai yana matukar son Jiddah amma ita ba sonsa takeyi ba and zaisha wahala ne kawai.. (niko nace har kayi concluding zaka sha wahala kenan)
Ammi ta cigaba dacewa, Jiddah na zaba maki Yayanki amatsayin mijinki, ku daidaita kanku, nan da sati biyu masu zuwa za'a sanya maku rana.

Jiddah ta kama kanta wanda take Jin kaman zai fita tsabagen Sara mata da ciwo dayake mata lokaci daya taji wani abu a saman forehead dinta kasan idanunta ji tayi kaman anzare wani abu awajan......and at thesame time tayi kara mai karfi sannan ta fadi kasa alamar suma tayi,.
Tashin hankali, Momma ta rugo da gudu ta kamata, haka zalika Faisal ma, Ammi ko tunani takeyi wai ko Jiddah nason tai masu na yan boko ne hakan yasa ta tashi tai shigewarta daka tana cewa aure dai babu fashi....Jin kukan Momma yayi  yawa saboda sun watsa mata ruwa taki farfadowa, Wanda har Mama taji ita da jikokinta suka taho falon da gudu, bashiri itama Ammi ta fito tana cewa wai dagaske Bata motsi Maryama, matsamin nagani,Faisal yace let's take her to the hospital please.
Momma tana kuka tace dauketa Faisal muje.
Haka suka kwasheta sai hospital
K/dara
Suna Isa nurses suka taimaka masu aka shigar da ita emergency room.
Likita mai suna Dr.Majdeed ya duba ta,ya yi iya bakin kokarinshi ganin ta farfado Amma abin yaci tura hakan yasa yai mata pain relief kawai sannan aka canja mata daki domin akwai wasu bincike dayake sonyi don ya lura condition dinta yayi high hakan yasa ko da yafito ya iske su Momma sunyi jugum, kwantar masu da hankali yayi sannan yace kada su shiga su jira ta farfado tukunna.
Suna nan zaune har dare misalin karfe goma, Nurse din da take dakin Jiddah ta fito da sauri ta nufi office din doctor, su Ammi suka mike tsaye hankali tashe suna ta faman leka dakin da Jiddah take ciki,suna nan tsaye sai ga doctor da nurse sun dawo suka shiga dakin hade da rufe kofa.
Tsahon minti ashirin suna cikin dakin kafin Dr.majdeed ya leko yace su shigo jiki asanyaye ya koma gefe ya tsaya yana son fada masu wani abu amma ya kasa,yana cikin tunanin ne yaji suna ma patient din magana.

Suna shiga suka iske Jiddah kwance idanunta abude tana kallon ceiling sai da Momma ta karasa wajan da sauri ta kama hannunta tana cewa Daughter kin farfado sannu Jiddah!
"Me zai faru sai taga Jiddah na hawaye tana jujjuya kai kaman makauniya tana cewa Momma, Momma bana gani idanuwana zafi suke min.
Faisal ya nufo wajan su da sauri yana cewa"Jiddah me idon ke maki ba gashi kina kallon mu ba!
Jiddah da dafe kanta tana kuma jin wani zafi da ciwo tace na shiga uku Yaya , Momma kaina ciwo ido na ciwo, ku tai make ni!
Dr majdeed yace uhmm Hajiya please ku dan je waje akwai analysis din dazan dauka, condition dinta is very critical, excuse me please.
Hakanan su Momma suka fita sukayi cirko cirko suna jiran Dr. Ya fito, sai ga su Ummi sun iso.
suma dai joining saukayi suna jiran fitowar Dr. Majdeed.

Misalin karfe 11:20pm Dr.Majdeed ya fito yace su sameshi a office." Suna shiga yace su zauna, sannan shima ya dade yana ta bincike a laptop dinsa kafin ya dago kai ya kalle su daya bayan daya" sai daya sauke ajiyar zuciya sannan yace ina jin tsoron fada maku abinda ya samu yar ku by seeing your faces nasan zaku shiga tashin hankali babba amma da fari Ina so ku kwantar da hankalinku, dukkan abinda ya samu bawa toh daga Allah ne,sai kuyi tawakkali,kuma ku sani komai yayi farko zaiyi karshe.
"Faisal yayi saurin katse shi da cewa look Dr.majdeed please ka fada mana abinda ya sameta"
Abba "yace yes Dr.majdeed fada mana kawai mu musulmai ne kuma munyi imani da kaddara mai kyau da mara kyau"
Zuwa wannan lokacin Momma Bata iya cewa komai hawaye ne ke Shirin zuba a idanuwanta, ita ko wani irin abu ne ya samu Jiddarhn ta,tun kafin likita ya fadi tafara ambaton "Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairun minha"Kalu inna lillahi wa'inna illaihir raji'un"
Sosai Dr.majdeed ya tausaya wa Momma ahankali yace kece mahaifiyar ta koh?
Momma ta daga kai itama idanuwanta duk sun ciko da kwalla.
Dr.majdeed ya fara magana.

***********
Tohhh ghost readers ba'a magana, yakamata kuzo kuyi comment fah.
Ina team Hafiz
Ina team Faisal
Kuma kuyi naku comments din via comment box,ko advice ku bani eheen inajira kuma.
Happy reading 👏
*************

Vote
Comment

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now