Shiyasa Abba ya ginawa Ummi gida don ta zauna kusa da mahaifiyar ta Ammi yana daya daga cikin soyayyar dake tsakaninshi da Ummi he value her much.
Ko da suka isa Jiddah su Ammi keta faman tsokanar Jiddah Amma Sam bata kula su ba karshe ma tashi tayi ta nufi Dakin da aka ware mata tun tun tuni, wanda idan tazo gidan anan take kwana, ta zauna saman gado tayi tagumi tana nadamar rayuwar data shiga though tasan dukkan abinda ya faru da ita daga Allah ne, hakan yasa ta bude wani karamin glass cabinet ta dauko Alqur'anul kareem ta bude surutul maryam sannan ta lumshe idanunta tafara karantawa cikin natsuwa da qira'a mai dadi har ta fara samun peace of mind......"dama tun fari Jiddah mahaddaciya ce tayi islamiyya da kuma Tahfiz....to which a shekara ta dubu biyu da goma sha shiddah (2016)ta sauke Alqur'anul kareem sannan kuma tayi saukar islamiyyah, Jiddah ba baya bace a fannin addini don kuwa tun tàna aji biyu tafara zuwa na daya (first position)haka har ta sauke, gashi duk sanda za'a gaiyyaci makarantar su musabaka tana daya daga cikin dalibai na gaba gaba wanda za'a zaba sannan ita ke zuwa masu na daya, bata taba zuwa musabaka tazo na biyu ba...tana da burin cigaba da Sanawiyyah (secondary school na islamiyyah) toh Amma tunda ta samu admission ta fara zuwa school sai ta aje burin.....toh wannan kenan.

**********************
Back to chapter (13) inda Hafiz ya bar spicy bite.
Yana barin wajan ya tafi airport direct dukda yamma tayi kuma hanyan baida kyau Amma hakanan ya tafi yayi booking flights har na mutum hudu
Sannan ya koma gida.
Ya samu Mom, Leemarh da Granny suna hira as usual....ya zauna hade da sauke ajiyar zuciya sannan yace Mom gobe zamu je Australia dukkanmu.Mom ta kalle shi da mamaki tace wani abu ne ya faru da Daddynku?
Suma su Leemarh binshi sukayi da kallo suna son suji abinda ya faru.
Hafiz yace relax, jikin dadi ne ya tashi and nayi deciding mu tafi gaba dayan mu.
Mom hankalinta ya tashi matuka amma gudun kar hankalin yaran ya kara tashi hakan yasa ta boye nata, tai ta bawa Leemarh da Granny hakuri tace Leemarh muje ki tayani perkaging kayan mu, haka suka fara da dakin granny, sannan Leemarh kafin akayi na Mom,
Mom da kanta ta samu Hafiz a daki wanda yayi tagumi da hannu biyu, ta dafa shoulder dinshi tace babana!
Ya dago kai yace Mommm
Murmushi tayi tace kana cikin damuwa ne?
Hafiz ya girgiza kai "Mom tace idan damuwa yayi ma mutum yawa toh ya rinka yawan karanta
"Ya haiyyu Ya qaiyyum"Bi rahmatikha Astagisu la'ila ha'illallahul azimul halim"
Sannan ko wacce sallah ka karanta "Ayatul qursiyyu "amanarrasulu" ,Lakadi ja'akum"
Kaji Babana
Hafiz ya gyada kai yace nagode Mom inshallah zan rinkayi,kun gama hada kayan ne?
Eh mun gama son nazo na hada maka naka ne.
Hafiz yace Momm har yanzu bakya gajiya kullin dai kaman baby kike kara maida ni.
Mom tace idan ban kula dakai ba wazan kula dashi ku biyu fah Allah ya bani, ba dole na kula daku ba.
Hafiz "yace hakane Mom yana Sanya hannunshi acikin suman kanshi....yace muje na tayaki Mom.
Haka suka hada kayan su biyu.
Washegari kuwa karfe 7am suka isa airport sai da suka je Abuja kafin suka tafi daga cen.
***********
Australia
Sun Isa da wuri suka je apartment din Daddy anan suka hadu da Abdul yai ma Hafiz bayanin komai ya basu key sannan suka aje kayansu kafin suka nufi inda Daddy yake.
Ba laifi jikin nashi da sauki amma daka ganshi kasan yana Jin jiki, batareda bata lokaci ba Hafiz yakai shi hospital aka fara masa treatment tare da Abdul suke komai inda likitocin suke iyakar kokarinsu don ganin ya samu lafiya.
Likitocin basu wani sha wahala ba wajan yi mashi treatment saboda Hafiz ya masu bayani akan yadda rashin lafiyan tashi yake.
3weeks sukayi kafin Daddy ya soma samun sauki hakan yasa Daddy ya uzzura akan su koma Nigeria gaba daya, amma Hafiz ya dage akan bazasu koma ba har sai ya samu sauki.
*********
Bayan wannan Hafiz tunda ya tafi kullin sai yayi waya da M.malunfashi yana tambayarshi ko Jiddah tazo neman shi.....Amma to his own surprised M.M sai yace mashi "aa" hakan yasa yake tunanin ko bata duba letter dinba, yace yasan Jiddah sarai idan tace bazatayi abu ba, to fah ta fada kenan.....ya dafe kanshi yace nima nayi gajan hakuri dama nasani naje gidansu,toh Amma ai bansan gidansun ba na dai San anguwan.
Hakanan kullun idan ya zauna ya ringa tunanin Hauwa'u kenan har sai yayi bacci....ki yaita kallon picx dinta dake wayarshi( ni ko nace huhhh😲yaushe Hafiz yake da hotunan Jiddah)
*Kamar kullin yauma yana ta duba hotunan guda uku ne, Daya ya mata ranar da ya ganta a shagon turare tana zaune tana zaban perfumes shi kuma ya dauke ta batareda saninta ba."
Daya kuma yai mata ranar da ta fara yi masa dariya suna Hospital awaje tayi matukar kyau wanda yasa ya capturing dinta batasani ba.
The last one kuma ranar da ya kirata office dinshi ana gobe zai yi confessing love dinshi"Hafiz yayi kayataccen murmushi ya rungume wayarshi yana Jin farin ciki na shiga cikin zuciyarshi, Amma Duk sanda ya tuna cewa Jiddah batasan yanayi ba sai yaji ranshi ya baci...Kuma yaita blaming kanshi.
2month sukayi a Australia alokacin Daddy yasamu sauki ,suka koma saboda school din Leemarh Allah yasama basu fara exams ba second semester.
Ranar asabar suka dira a Nigeria,Kaduna kuma agidansu.
( Awashegari sunday su Jiddah suka tafi katsina).
Hafiz dai babu irin neman da bai mata ba a hospital, bai taba tunanin a time din suka kare SIWES ba...
Bayan sun hadu da M.m ne sai a lokacin M.m ke sanardashi cewa Jiddah tazo har ya bata number shi.
Hafiz ranshi ya bace sosai ya dai sitiyarin mota ya dubi M.m dake gefenshi yace haba M.m kasan line din ya samu problem ba'a samu na and duk baka iya fada mun ba da dayan network dina kuma Ina yawan tambayanka akan anzo nemana, and you knows what I mean but, you keep on telling me No.
M.m yace am so sorry oga bana so ka baro abinda kake ne ka dawo, saboda lafiyar Daddy yafi komai a rayuwarka.
Ohhhhh yes lafiyar Daddy yafi komai arayuwana amma you have no clue on how important she mean to me in my life," agaskiya M.m kamin abinda bazan taba mantawa dashi arayuwata ba, yanzu ta Ina kake so na fara nemanta, har layinsu naje but bansamu komai akanta ba ya cukurkuda suman kanshi wanda yayi yawa baya aski sai dai ya gyara, yace bana bukatar ganinka yanzu ka tafi har sai na nemeka, M.m yace am so sorry sir.sannan ya fita a motar....Hafiz ya dade yana tunanin hanyar dazai bi ya samo Jiddah amma ya kasa, at the end ya tuka motar ya koma gida.
After 2days aka nemeshi awajan aiki (Abuja)a inda ogansu yake sanardashi cewa anyi posting dinsu izuwa Pakistan zasu bi wasu sojojin Pakistan suna Lagos don su karo course, Hafiz was out of words to which ansan letter din yayi kawai batareda yace komai ba, aranar ya koma kaduna ya sanar da parents dinshi sannan Mom ta shirya masa kayansa.... Leemarh ko sai kuka takeyi wai ita bataso yayanta ya tafi kasa mai nisa, hakannan Hafiz yai ta faman lallashinta harda mata alkawarin kayan India da sari masu kyau, dayake itama jirgi daya ya kwaso su da Jiddah sai wani murna takeyi Amma bashi ya hanata yin kuka ba dasuka rakashi airport ita da Daddy, Mom kuma a gida aka barta, flight din Abuja ya samu daga cen suka hadu da wasu colleagues dinsu sannan suka tafi Lagos din.

**************
"Jiddah ta samu kwanciyar hankali fiye da tunanin mai karatu,ganinta cikin yan'uwa ga Ummi da Abba akusa da ita, Yaya Muhammad da Saif kuwa kowannensu da kulawan dayake bata dukdama Momma ta boye masu damuwar da Jiddah take ciki.
Watan su daya a katsina Faisal ya dau hutu yazo dubasu.....
Ranar Jiddah murna kaman me, haka tai ta nan nan da Yaya Faisal duk tana nan makale dashi, idan akace Jiddah dauko min abu kaza sai tace Yayanah taso muje ka raka ni, idan ko ya kiya haka zatai ta jan hannunshi har sai ya tashi sunje tare, wannan dalilin yasa Ammi hangen wani Abu to which washegari da sassafe ta kira meeting tana son ganin Ummi da Abba da Kuma Momma.
******
Karfe takwas (8am) duk suka hallara a babban falon Ammi,
Mama ma tana gefe zaune duk suna jiran suji abinda Ammi zata fada.
Ammi tayi gyran murya sannan tace.
🤐🤐🤐
Am tired 😜

*****************
Vote
Comment please

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now