Jiddah bata dawo ba saidata tabbatar anyi centrifuging sample din, taga an dauka za'a fara test din kafin ta wuce phleb, tanayi tana shiga ciki tana checking ko an gama, after 30min ta shiga ta ansa results din  sannan ta kai reception ta bama Fatima ta shigar sannan taba su, Mom tace thank you kinji Allah yai maki albarka"
Thank you ma! Tai mata sallama ta tafi. Faisal kuwa yana zuwa office ya hadu da Isma'il brother dinshi as usual daman ya fada, yace Abban afnan ya akai kamin sammako ne, karan wani ka kawone?
Isma'il yace similar things, kafini sanin abinda ya kawo ni ai, ya fada yana hararanshi playfully yace Faisal ka canja al'amuranka kwanakinnan ,kwata kwata baka nema na,ka dena neman shawara awajena, infact problems dinka ma you don't share it with me.....Faisal Anya babu abinda kake boyewa kuwa wanda baka son kowa ya sani....
Faisal dayayi tsaye Yana sauraron Dan uwan nasa fuskar shi dauke da murmushi cike da annuri, yaace Ismail ba abinda kake tunani bane, as you can see am too busy at office kullin cikin case muke, ba hutu ko kadan, problems kuma babu ne saboda kasan inda akwai you will be the first person to know about it....so wannan ba abun daga hankali bane.
Okay yanda kafada cewar Isma'il sannan yace Amma maganar jiya fah ,is like something is really fishy between you and Jiddah, ya kalli Faisal da yake mashi kallon tuhuma.
Isma'il yace noooo don't look at me in that way am telling you the truth Faisal kasan ni Ina da hangen nesa and I don't hide things,so please my advice here is, Jiddah sister dinka ce idan kasan kana sonta ne, toh you better tell her now, kafin ta fada tarkon wani, kai kuma abarka da sakakkaken baki......Faisal yayi dariya yana cewa Ahhhhh brooo you know girls too much ehnnnnnn a"
Isma'il yace that's the fact bro kanaji kana kallo zata barka ta koma wa wani cen, and kasan dai gida bai koshi ba, ba'akaiwa dawa ba"
Faisal ya dan gyada kai yana tabe baki kaman irin maganar bata shige shiba, Isma'il yace uhmm nidai na gama nawa zan tafi, yauwa maganar tafiya na jibi ne, shiyasa nazo yima Momma sallama zan tafi da mammyn affan ma kasan karatun 2years ne (masters)and gaskiya bazan iya yin 2years without my family ba....Faisal yace kana da gaskiyan ka, kasan dama nace maka idan zaka tafi to is better ka tafi dasu saboda kewa da sauransu, "Isma'il yace yeah nima abinda nagani kenan"tohh bro bari naje office yau na maka sammako,sai munyi waya
Faisal yace alright zan kira ka before you leave."
Okay bye"
*******************
After one week(Bayan sati guda)
Ranar asabar ita ce ranar dasu Ummi zasu zo all the family..hakan yasa tun da asubahi Jiddah ta tashi,ta kama shirin tarban family dinta, SashinYaya Faisal ta nufa sannan to ta taso shi gaba, dama idan zatayi aikin snacks shi take kira don dole take masa saiya taya ta haka zata daura masa apron har da hulan chef suke sanyawa so da dama weekend sukeyin aikin kitchen tare haka abokanan shi idan suka zo weekend zasu sameshi a kitchen da ita Jiddah,sai dai su dauko masu kujerun dinning suce su zauna  sunayi suna taya su hira abin gwanin ban sha'awa.....yauma dai hakan ya kasance tana taso shi karfe bakwai na safe ya tashi yana mata mita, tace nifah Yaya Faisal karkamin wani magana dukwani mita dazakayi kayi saifah munyi aikinnan tare as team kasan dama mun saba Koh ta kanne masa ido daya wanda ba karamin killing Yaya Faisal yake ba, haka ya bita suka soma aikin snacks din which includes samosa, doughnuts and cakes along with different kind of drinks, Momma kuma tana ta fama da girke girken abinci ita da Yar aikinta Ladi kasancewar kitchen din babba ne sosai kowa yakama angle dinsa suna yi suna hira abinsu, "Momma tace karfi da yaji Auta ta maidakai Chef Faisal"
"Faisal yace wallahi Koh momma ai ki bari yanzu fah abokanai na Chef suke kirana wai babu abincin da ban iya girkawa ba, kuma Momma duk aikin Autanki ne ita ta koyamin"
Toh ai taimakon ka tayi kaga idan matar ka bata da lafiya saika tayata aiki da girkin abinci ko ba haka ba Ladi ta karashe tana tambayar mai aikin kasancewar babban macece zata kai shekarun Momma"
Ladi tace kwarai kuwa Hajiya ai ni Ina son naga namiji ya iya girki kada matarsa ta raina masa wayoooo"
Jiddah dai na sauraron su bata sako masu baki ba, "Faisal ne ya kalle ta smiling yayi ya matsa bayanta ya kai bakinshi dai dai setin kunnenta yace ahankali "My little girl tunanin me kike tunani"
Murmushi kawai tayi ta waiga gefen da Momma take tace Momma Yaya zai fasa min kunne kimishi magana Allah!" Momma ko tagansu sanda yake mata magana hakan yasa bata kula Jiddah ba, tunani barkatai ya fara zuwa cikin kwanyan ta akan ko dai akwai abinda yaran suke boyewa ne....sai kuma tayi murmushi tace da ace abinda nake tunani gaskiya ne danafi kowa murna, ta cigaba da aikinta tana ta tunani aranta... karfe sha biyu suka gama komai, Jiddah da Faisal su suka shirya komai a dinning sannan suka tafi daki don su shirya.
Misalin karfe daya da rabi (1:30pm) motocin su Ummi sukayi horn, Mai gadi ya bude musu suka shigo motor biyu ne sukayi parking a bangaren da aka tanadar domin aje motors.  Yayinda motar farko wani kyakkawan saurayi ne ya fara fitowa yana sanye da gizna(shadda) sky blue dinkin kaftan sai hula zanna sai kyalli takeyi, gefen driver seat ma wani saurayin ne ya fito wanda shi kuma ya dara dayan haske sosai to which hasken fata ne kawai zai nuna ma dayan amma banda kyau..... murmushi sukayi alokacin da suka kalli juna sai farin yace ya muhammad kalli su Ummi sai wani soyewa sukeyi da Abba sai kace yau suka fara haduwa🤣sai kuma suka maida kallon su ga iyayensu wanda suka fito tare suma adayar motar, Ummi tace yaran nan akwai gulma acikin ku yanzu me kuma mukayi dayasa ku Smiling?

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now