****************

The next day

Yaya Faisal shi ya kawota har hospital din suna ta hira abinsu,
Faisal ya kalle ta yayi smiling yace my little girl shigar nan tayi kyau amma hope ba in-law aka samo mana ba? Ya fada yana driving.
Dariya Jiddah tayi sosai sannan tace Yaya Faisal wani In-law kuma ta lumshe eyes sannan ta bude tace nooo kasan ni yaya Faisal samari basa gabana, Ni fah har mamakin yadda ake soyayyah nakeyi because Ni banma san miye LOVE ba
Faisal ya zare idanu in a shock way yace Jiddah kina nufin baki taba son kowa aranki ba?
"Jiddah ta gyada mashi kai with full of confidence tace Yaya Faisal wai ya akeyin soyayyah toh?
"Faisal ya kalle ta surprisingly yace ashe har yanzu little girl dina bata girma ba"
Jiddah ta tura baki gaba Noooo Yaya Faisal am old enough ooooooo kawai dai ni bansan yadda akeyin LOVE bane?
Ooo oooo Jiddah na she is a little girl har yanzu ya fada adai dai lokacin dayake parking a hospital din, "Jiddah ta rasa me zata ce mishi sai kawai ta farayi kaman zatayi kuka" tuni Faisal ya soma rarrashi yana kallon cikin kwayar idanunta sosai yake jin wani abu yana dada shiga cikin zuciyarshi, sosai yake jinta cikin ranshi, yana da wani dalili wanda zakuji shi a nan gaba inshallah fans😁" back to business dariya Faisal ya soma yi ganin harda guntun hawaye a fuskarta, yace Ahankali JIDDAH dagaske bakisan Love ba? Jiddah ta gyada kai cikin fuskar tausayi "
Faisal yadan dakata yana wani tunani yana kallonta kafin yace tohm yanzu kije Lab ko idan kin dawo gida zamuyi magana, don't forget to follow your protocols"ta gyada mashi kai alamar taji*** kada kuji nace protocols, akwai sharuddan da tun Jiddah na karama Faisal idan yakaita school yake fada mata,tun bata bi har abin ya bi jikinta, yanzu ta hau kan system din ta zauna da kyau ko waiwaye batayi, hakan na daya daga cikin dalilin dayasa batasan me ake kira LOVE ba"Sukayi sallama ta tafi.

Tana shiga Lab din ta soma aiki ..
staffs din suna ta faman aikin ansan blood sample na yan recruitment wanda ba acikin lab din akeyi ba,a 061 cen wani bangare daban cikin wani babban hall, kusan student zasu kai 500 ko fin haka tsabar yawan su, "Jiddah tana daya daga cikin masu ansan sample daga inda take bata kallon kowa, ba ruwanta da surutu da coursemate dinta, aikinta kawai takeyi.
Commander Hafiz Abubakar ne yashigo tare da guide dinshi masu take mashi baya daga inda ya tsaya yana magana da (master warrant officer) AE bello  head of the lab,anan kaman ance ya kalli gabansa,zaune take well composed tana sanye da doguwar riga na material maroon and black veil sai white Labcoat dinta daya sha wanki kal kal da guga, very neat, ya dade yana kallon wajan amma shi kanshi ya rasa dalilin kallon nata.
dai2 lokacin dazai dauke kanshi asannan ne Jiddah ta dago kai batareda sanin shine awajan ba ta koh sauke manya manyan idanuwanta masu kyau a fuskar Hafiz kasancewar yadanyi nesa da ita sosai amma sai data gane shi,sai kuma suka koma kallon juna wanda su kansu basusan suna kallon ba don tuni zuciyarsu da brain dinsu suka fada wata duniyar wadda basusan akwaita ba, Jiddah ce ta fara kawar da kanta gefe ganin ta saki aikin da takeyi tai saurin cigaba da aikinta, Hafiz kuma sosa bayan keyarsa yayi ahankali ya waiga don ganin ko akwai mai kallon sa Amma sai yaga kowa harkan gaban sa yake hakan yasa ya kuma satan kallonta batareda ya s anya komai aranshi ba sai kuma yayi sa'a itama ta kalle sa baisan lokacin daya wayance ba ya juya yabar hall din, itama dai dauke kanta tayi kawai tana tunani acikin zuciyarta tare da tambayan kanta" meyasa suke haduwa ita bata so" ta rasa meyasa duk sanda ta kalli kwayar idanunsa takejin heartbeat dinta na canjawa" ita fah gaskiya zuwa asibitinan SIWES ya fara sha mata kai.....tana tunani tana aikinta ranar basu suka gama ba sai karfe 5pm na yamma hakan yasa ko da suka fito tafiya gida babu masu Napep awaje, suna nan tsaye suka ga motocin commander sun tsaya in front of them, aka sauke glass din motar da Hafiz yake ciki driver din wanda shima soja ne yace dasu, Oga commander yace ku shigo"

Kut!kace mishi yazo dakanshi" Cewar Jiddah ta fada atakaice kaman tana jira, Fatima tace Jiddah  wlhy idan akazo duka guduwa zanyi na barki tafada tana dariya "Jiddah tace sha kuruminki ma Fatima babu me dukan mu, karki manta kina tare da Jiddah fah ta fada da izza basu ankara ba suka ganshi gaban su yana masu Sallama bai ko jira amsawarsu ba yace kushiga mota ayi muku lift saboda yamma tayi yanzu bazaku samu Napep ba.
Fatima ce tayi saurin cewa okay thank you sannan taja hannun Jiddah wacce ita tunaninta ma takeyi, ganin ta kawai tayi a motar wai irin ta waiga taima Fatima magana sai taga mutum akusa da ita ta sake waigawa gefenta babu Fatima babu alamarta acikin motar ba shiri ta saki kara wanda ya rikita driver don dama driver ne da Hafiz kawai, ta kulle idanunta ta Sanya hannunta a kunnenta sannan ta cigaba da ihun" idan ka kalle ta abu 2 zuwa 3 ne zaizo mind dinka, nadaya zaka tsorata ka zata ko anyi mata wani abu ne, na biyu zaka dauka kanta ba daya yake ba, na uku kuma mamakin yadda take ihun zaka rinkayi kaman wata karamar yarinya wacce batada wayo."
Sosai driver ya tsorata wanda yasa ya ci birki bashiri hade da waigowa baya don ganin kome akai mata.
Hafiz baiyi niyan tanka mata ba, beside shi baisan ma ita tashigo motar ba ya dauka kawarta ce.....Amma sai ya daure yace "could you please keep quiet for goodness sake" Duk kin cika mana kunne and ke kuma kin kulle naki ears din,

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now