BABI NA ASHIRIN DA DAYA

20 1 0
                                    

*SHIN SO DAYA NE?*
_mijin kaddarata...!_

*HAFSAT HAFNAN*
_Hafnancy..._

*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*

https://my.w.tt/JNyQzygfvcb

*BABI NA ASHIRIN DA DAYA...!*

"Good morning everyone. " Suhaima ce ta fad'i hakan alokacin da suka isa k'arkashin bishiyar.

"Morning to you too amaryarmu." Fresh ne ya amsa mata tare da kashe mata ido daya.Sauran ma duk suka amsa mata.Idanuwanta ne suka had'e dana Rukky, ta gallawa Rukkyn harara ah sa'ilin data zauna kusa da Ash.ita kuwa Rukky jikinta ne yayi sanyi ganin irin mugun kallon da Suhaimar ta jefeta dashi,hakika tayi nadamar abinda ta aikata, fatanta dai Allah yasa Suhaima da Leedar su yafeta.

Suhaima ce tace azuciyarta"wallahi ganinki ba alheri bane you bloody monster... "

"Ina fatar basai na sake maimaita dalilin taruwarmu anan ba,don kuwa kowa ya riga daya sani idan aka cire Ruheena💗 wacce ta siyasa muka samu aka kawota nan..... In that case,babyna am very sorry for that please..... Kinji masoyiyata? "

Leedar ne ya fad'i hakan tare da tsare Suhaima da idanuwansa yana mai jiran ta bashi amsa.Harara ta wurga masa amatsayin amsarsa kenan.

Daga kafadunsa yayi cikin wani salon bagunsa,alamun bai damu bah,don koh dukansa zatayi bazai iya hanata bah sabida tabbas an b'ata mata.

Cigaba da maganarsa yayi"Ruhee💗 kamar yadda kika sani wannan itace Rukky... She's here to tell her part of the story. " Ya fad'i hakan tare da nuna Rukkyn da 'yar yatsa.

"And wannan shine Yazeed, nasan bah wani saninsa kikai bah sabida so d'aya na taba zuwa dashi wurinki...he is also here to tell us the role he played in the story... "

Kallon wanda aka kira da Yazeed tayi, Kura masa idanuwa tayi babu koh giftawa,tana mai son tunano inda ta taba ganinsa.Ai kuwa ta tunoshi,Leedar ya taba kawoshi su gaisa da ita sau d'aya amakaranta.

Azuciyarta tace"Toh shi kuma meye nashi aciki?Allah dai yasa bah wani salon rainin wayon Haidar yake shirin yi min bah.....amma kodai..... "

Leedar ne ya katse mata gajeriyar tunaninta ta hanyar fad'in"Amma before anything,zanso ace ki bada labarin abinda ke tsakanina dake Suhaima.... Karki rage komai kuma kada ki boye komai..... Kiyi mana bayani in full details "

Gabanta ne ya yanke ya fadi jin abinda ya fad'a,kai dubanta tayi bangaren da Fadima ke zaune.Idanuwansu suka had'e,atake Fadimar tayi mata signal d'in ta bada labarin kamar yadda ya bukata.

*📣WAIWAYON BAYA📣*

Ahankali ta soma da"Kamar yadda dai kuka sani,Sunana 'SUHAIMA SA'AD MAI NASARA'.... Ina schooling ah 'Zaria academy',wanda ayanzu haka ina final year d'ina wato 'SS3'.Back then in SS1,Fareeda Ahmad use to be my very good friend... Ni da ita we were best of friends.Though,haduwar tamu was just recently,because ah 'SS1' d'in ta shigo makarantar, sab'anin ni dana fara makarantar tun daga 'JSS' class.Shakuwarmu ta wuce yadda mutum ke tunani.kuma abin mamaki,duk yadda muke so close d'in nan,bamu taba kaiwa juna ziyara agida bah,dayake duk iyayenmu bah masu barin 'ya'yansu suna yawon gantali bane, daga gida sai school, sai kuma islamiyya.Ni da ita ah school kawai muke had'uwa, har takai ta kawo wanda suka sanmu tare suna yawan yi mana gorin rashin ziyartar juna."

Dakatawa ta danyi,ta d'ago kanta tana bin kowa da idanu don ta tabbatar ana tare da ita,ganin an natsu ana sauraren labarinta ya sanyata cigaba da gashi.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 08, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SHIN SO DAYA NE?Where stories live. Discover now