BABI NA SHA HUDU

5 0 0
                                    

*SHIN SO DAYA NE?*
     _mijin kaddarata...!_

  

   *HAFSAT HAFNAN*
     _Hafnancy..._

*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*

     https://my.w.tt/JNyQzygfvcb

         

         *BABI NA SHA HUDU...!*

Na dawo daga rakiyarsu Ash na tarar Suhaima da Lubna na gyara wajen da muka yi breakfast.

Ko sake kallon ita Suhaimar banyi bah,nace wa Lubna"Lubna ina Umma?"

Tace"Ta tafi bangaren Abba... "

Jin hakan ya sanya na nufi d'akina ba tare da na sake cewa komai bah.Ina shiga daki, wanka na soma yi don inji dan dad'in jikina.Doguwar riga mara nauyi na sanya sannan na dauko wayata na kunna.

Wayar tana gama booting, sai text messages suka hau shigowa kamar dama can jira suke abude wayar.

Text d'in Ash na soma budewa wanda nake tsammanin tun jiya ah Kano tayi min(idan zaku tuna sanda zata dauki Mubeen hoto tayi ignoring wasu messages.... Remembered?)

The message goes lyk dix, _*"Fadima idan kina yiwa Allah ki taho ki kwashe shanyar da kika yi.... Kayan sun gaji da bushewa...kina can kina soyewarki da Man d'inki ayayin da mu kuma kika barmu ana ta yaga rigar mutuncinmu anan.... "*_

Murmushin takaici nayi sanda na tuna da Mummyn Mubeen wanda itace Ash ke nufin taci mutuncinsu.Har yau mamaki nake da suka ce mun matan nan tayi musu rashin mutunci akaina, sabida sam koh kusa ba tayi kama da wacce zata iya yin hakan ba.Ko da yake rayuwar kenan, Dan'adam tattare yake da abubuwan mamaki kala-kala.

Sauran text messages d'in kuma wanda ake aiko wa mutum ne idan kayi missing voice call.Nayi missing kamar 20 voice calls daga Ummana wanda hakan na nufin tayi ta gwad'a layina kenan ko Allah zai bata sa'a ya shiga, she never gave up.... Uwa -Uwa kenan wacce babu irinta.

Sauran calls d'in dana yi missing kuma, daga Leedar ne da Ash, sai kuma Mubeen.

Mubeen kenan sai ayanzu ya fad'o min arai. Nasan yana ta trying line d'ina bai sameni bah, kuma na tabbata watakila yana cikin wani hali ayanzu, idan har da gaske yana sona kenan kamar yadda ya fad'a, sabida ni ayanzu na daina yadda da love stories na d'a Namiji.. *'DR. MUBARAK'* ya mugun koya mun darasi.

Ji nayi kamar na kirashi, sai kuma na fasa dan bai dace ace ni in fara nemansa ba,shi dinne ya kamata ya k'ira yaji ya muka kawo gida? Don haka zan k'yaleshi duk sanda yayi trying line d'in yaji ta shiga toh Alhamdulillah, amma idan bai k'ira bah toh Wallahi ni d'in mah bazan sake nemansa ba.

*'ENGR. MAHMOOD'* ne ya fad'o min arai.Murmushi nayi ina tuna sanyin halinsa.Namiji ne kamilalle,maganarsa ahankali cikin sanyin voice.Abinda yafi bani dariya agame dashi bai wuce yadda idan na masa tambaya.. amaimakon ya maido min da amsar tambayata, No sai dai shima ya jefo min tasa tambayar.

Abin dariya ya bani wanda har nake ta k'yak'yatawa, kofar d'akina naji an bude aka shigo.

It's Umma, ganinta bai hana ni daina dariyata bah,dariya fah hadda hawaye.

Ina kallon Umma wacce sai kallona take cike da sha'awa tace"Masha Allah! 'Yar Kareematu burina bai wuce na ganku cikin farin ciki bah akoda yaushe.... Na san koh baki fito fili kin fad'a ba, tabbas daga ganin wannan hawayen murnar, alamu ne dake nuni da cewa tabbas surukin nawa ya mugun kwanta miki arai. "

Jin kalaman da suka fito daga bakinta ya sanyani tsai da dariyata alokaci daya.

Ta cigaba"Dama zuwa nayi muyi 'yar hira ni dake... Inaso inji ko ya kika gan Mubarak d'in ? Shin ya kwanta miki arai koko a'ah ? Sai dai Alhamdulillah na riga na samu amsoshin tambayoyina akan fuskark kuma sosai nayi farin ciki da hakan... ki sani Kareematu always wants the best for her children... Allah ya sanya alheri"

SHIN SO DAYA NE?Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum