BABI NA BAKWAI

13 1 0
                                    


  *SHIN SO DAYA NE?*
     _mijin kaddarata...!_

  

   *HAFSAT HAFNAN*
     _Hafnancy..._

*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*

     https://my.w.tt/JNyQzygfvcb

         

         *BABI NA BAKWAI...!*

Tafiyar 131km mukayi, dayake motar nada gudu shiyasa acikin k'ank'anin lokaci muka isa Kanon Dabo, jalla mai babban suna..ga mata ga mota,ga naira ga kuma gwauron dutse yaro koda mai kazo an fika..k'irarinsu kenan, Throughout our journey idanuwana biyu ko gyangyad'awa banyi ba tsabar zumud'in san naga nayi ido hudu da Mubeen d'ina, adaya b'angaren kuma ina cike da fargaba wanda ban san kona menene ba.

Suhaima kuwa da Ash queen sunsha baccinsu ayayin da ni kuma da Malam Iro driver jefi-jefi muke dan tab'a fira,yana bani labarin kano da irin ni'imomin da Allah yayi mata dayake shi d'in asalinsa mutumin Kanon ne.

Umma ta k'ira yakai sau biyu tana tambayar inda muke amma sai dai na baiwa Malam Iro waya ya fada mata sabida ni ban San wurare ba kasancewar bana yawo ko tafiye- tafiye..daga scul, gidansu Ash queen sai gida ake samuna.

Mubeen d'ina ma munata waya dashi,shima idan yayi tambayar Inda muke,hadashi nake da Malam Iro ya fad'a masa.Duk acikin zancensa yafi furta"wallahi na k'agu in saki a ido my Zahra.." Mubeen d'ina kenan..shi kadai yake k'irana da Zahra if not kowa Fadima yake k'irana....Gayen yasan takan soyayya ne...Don haka taya za'ai bazan rikice akansa ba ?

Kano garin zirga zirga ne sosai, ire iren ababen hawa da kuma mutane zaka kansu suna aikin kai da komo, wannan ba shine farkon zuwana garin ba, farkon zuwana alokacin da zan rubuta Jamb ne, sannan zuwana na biyun nan ba sai na sake maimaitawa ba don kun riga da kun sani.Bamu wani sha wahala ba muka iso Na'ibawa Yarakwa Wanda shine unguwarsu my Mubeen..lallai kuwa mamaki ne ya kusan kashemu yadda muka ga Malam iro yasan takan Kano gaba daya don sanda my Mubeen ya masa kwatancen gidansu wai kusa da wani sanannan mai saida kayan dangin itacuwa ne...ya kira sunan mutumin, atake yace ai yasan wurin.

Nace"Lallai Malam iro agaisheka Kasan shiga da fita na garinka abinka"

Yayi dariya sosai yace"Ai Hajiya ni banga Wanda ya isa ya b'atar dani agarin Kano ba...ni da garina ai idan ban San wurare ba ai naji kunya"

Gaba daya muka sanya dariya kamar ba gidan rasuwa zamu ba.Ahakan muka iso layin da Mubeen ya mana kwatance,ai kuwa muka hango tarin jama'a maza zazzaune akofar gidan...su dattijai ne,matasan ne hadda yara kankananu.

Kirjina ne ya soma bugawa da sauri da sauri ganin am juz about to set my eyes akan Mubarak, driver yayi parking k'ark'ashin wata bishiya dan nesa da jama'ar.

"Hajiya Karama ina ganin nan nefa gidan rasuwar,ki kirashi kiji." Acewar Malam Iro

Murmushi nayi nace"Toh Malam Iroro"

Kafin nakai ga dialing numbarsa,sai kawai ga k'iransa ta shigo,da sauri nayi receiving. Ahankali na furta"Hello my Mubeen munfa iso..." Na soma waige waige ina masa kwatancen duk abinda na gani don mu tabbatar ko muna right place d'in.

Yace"Babyna barka da zuwa....u arrived at the right place... Yanzu k'anwata zatazo ta shigar daku ciki, driver kuma zanzo na taho dashi zuwa wurin maza "

So nake nace"Kai kana ina?" Amma sai naga yayi saurin kashe wayar.

Na fadawa su Suhaima yadda mukai dashi.Akalla mun kai kusan mintuna goma muna jiran sister d'in tasa ta fito amma shiru kakeji.

Afusace Ash queen tace"Malama nifa gaskiya na gaji gashi duk na takure cikin wannan zumbuleliyar hijabin sai kace wata matar limamin sarkin makka..."

SHIN SO DAYA NE?Where stories live. Discover now