BABI NA SHA BAKWAI

4 0 0
                                    

*SHIN SO DAYA NE?*
     _mijin kaddarata...!_

  

   *HAFSAT HAFNAN*
     _Hafnancy..._

*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*

     https://my.w.tt/JNyQzygfvcb

         

         *BABI NA SHA BAKWAI...!*

Around 10:05am muka fito daga wani lectures ni,Ash queen da kuma Zee.Zee tayi mana sallama ta tafi gida.

Ni kuma da Ash zuwa mukai muka sami wani silent place inda babu wata hayaniya muka zauna (Karkashin wata bishiya).Ayau ne naci alwashin fayyacewa Ash komai dake tsakanina da Leedar, da muka wasar da muke bugawa atsakaninmu.

Zamar mu keda wuya, Ash tace"Yauwa Sahibar ina sauraronki.... Wallahi na k'osa ki bani gist d'in nan kamar yadda kika alkawaranta.. "

Harararta nayi, nace"Dad'ina dake Ash akwai ki da son jin kwa-kwaf... "

Tace"Wateva... Ni dai gani nan na kasa kunnuwa ina sauraronki.... "

Kura mata idanuwa nayi, kafin na soma da"Da fari dai.... Kin kuwa san wanda ya taimaka mana ya dawo damu gida adaren da motarmu ta lalace kan hanyarmu ta dawowa? "

Irin kallon I don't care tayi min,tace"Ina ruwana kuma da wanda ya taimaka mana din? Ke ni koh fuskarsa mah na gani ne balle na san koh wani irin jinsin ne? Ke ya kamata mah ayi wa wannan tambayar sabida kece uwar iyayi...... "

Da sauri na d'aga mata hannu"Ash its okay... Ni matsalata dake kenan wallahi ba'a iya shuka abin arziki dake sai kin nemi ki b'atawa mutum rai..... "

"Okay naji am sorry anty... " Ta fadi hakan tare da turo small lips d'inta gaba.

Abin nata mah ni dariya yaban, nace"Ai dole kiyi ladabi tunda ana son aji gulma.... Hadda wani anty.... Lallai Ash agaisheki sarkin iskancin....... "

"Yo! har nawa yakai wanda aka shirya miki akano? A sister happened to be a wife hadda rabo atsakani, abun karin takaicin wai ma bai sanar da kowa batunki ba sai basajar da suka shirya shida matar tasa...... Ya salam! Kawata wannan bala'in da mai yayi Kama.....? "

Atake anan naji wani tashin hankali yayi mini sallama, nace"Aysha ke dai bari kawai.... Mubarak ya gama da rayuwata.... Na yadda da Mubeen fiye da tsammaninki tun kafin na gansa face to face, ashe Mubeen d'ina wanda nake jinsa har cikin raina yana da mata harda 'ya..... Aysha Ummata bazata taba amincewa na aureshi bah...... "

Da sauri ta tari numfashina"Ai wallahi ina bayan umma.... mey zakiyi da mai mata? balle mace ma kamarki Fadima baki cancanci ki zauna da kishiya ba, sabida kin tara komai da duk wani d'a namiji zai so atattare dake ba tare daya had'aki da wata ficikar ba.... Wallahi ni naga kokarin wannan gyatumar tasa da har ta kalli cikin idanuwana ta fad'a min cewar wai mijin aure muke nema ido arufe..... Allah na tuba mai Aysha zatayi da mayaudarin namiji irin Mubarak? Sai ke d'in da kika gan zaki iya..... Kai Fadima manta kawai bana son ina tuna wannan abu "

I felt really sorry for Ash dan ko bata fada ba, I know how she feels,ahankali nace"Ayshata am really sorry for everything,wallahi duk ni na janyo muku wannan wulakancin....... "

Da sauri ta katse mini hanzari ta hanyar sanya 'yar yatsarta saman lips d'inta, tace"Shhhhh!!.....it's okay baby gal.... Idan har kina son na hakura, toh wallahi sai idan har kin amince zaki rabu da Mubarak..... Don wallahi Leedar shine kalarki Fateenah........ "

"Well For ur information...babu kamai tsakanina da Leedar.... Ma'ana,Ni da Leedar ba soyayya muke ba... " na furta hakan with full confidence.

Cike da mamaki tace"ke babe please kibar yin wannan tsadadden wasan.... Karki raina mun hankali mana bayan kowa da kowa yasan da cewa keda Aliyu Soyayya kuke... Sannan yanzu da rana tsaka kice mun babu komai tsakaninku ? Ke kanki kin san hankali bazai dauki wannan magana taki bah.... Okay tell me then, meke tsakaninku in ba soyayyar ba ? "

SHIN SO DAYA NE?Where stories live. Discover now