BABI NA SHA DAYA

9 0 0
                                    

*SHIN SO DAYA NE?*
     _mijin kaddarata...!_

  

   *HAFSAT HAFNAN*
     _Hafnancy..._

*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*

     https://my.w.tt/JNyQzygfvcb

         

         *BABI NA SHA DAYA...!*

Akalla mun kwashi kusan Mintuna talatin tsassaye abakin titin ba tare da mun sami kowacce mafita bah don motar tamu taki tashiwa, gashi gari sai dad'a duhu yake wanda hakan ya tabbatar mana da dare ya soma lulawa don wayoyinmu duk ah mace suke balle mu iya cewa karfe kaza ce yanzu.

Motoci kalilan ke giftawa, kuma duk wanda mu kayi mah waving alamar ya tsaya ya taimaka is not willing to stop sai mah dad'a k'ara gudun motar suke.

Tashin hankalina mah bai wuce wacce zanje na tarar agida bah. Muna cikin wannan halin ne na hango wata mota can da nisa apake ta hanyar kano, ta hasko wutar gaban motar, alamu ya nuna kamar motar ta d'an jima apake sai yanzu mai motar yayi niyyar barin wajen.

Tunkaro hanyar da muke naga yayi wanda ganin hakan ya sanya ban san lokacin dana haye har tsakiyar titi bah ina masa waving din ya tsaya.

Cikin ikon Allah kuwa naga motar ta soma slow down ayayin data tukaro ni, sannu ahankali muka ga ta gangara ta gefe na, ta samu wuri tayi parking ah gefen hanya.

Da d'an gudu-guduna babu koh alamun d'igon tsoro atattare dani nayi saurin k'arasawa gun motar,  kafin na gama isowa kusa har an saukar da glasses din windows din.Hakan ya bani damar sakale wuyana ta bangaran windon mai zaman banza nace"Assalamu alaykum Mallam don Allah ina ka nufa? "

"Ku ina kuka nufa? " cikin sanyin murya naji ya fad'i hakan.

"Zaria muka nufa..... Please bawan Allah ka taimaka mana motarmu ce ta sami matsala.....Don.... "

Saurin katseni yayi ta hanyar fad'in"Okay.... Bana son dogon surutu ku shigo mu tafi kada ku b'ata min lokaci...... "

Ban damu da attitude d'insa bah sabida mu muke nima kuma dole mu saukar da kai k'asa.

Da ihuna nake fad'in"Malam Iro ku taho mun sami lift... "

Ina jin Ash na fad'in"Malama ba ko wani anyhow car zamu shiga bafa.... "

Mal. Iroro naji ya bata amsa donni bani da lokacinta yanzu, burina kawai na ganni agida.

Ce mata yayi"Sai ki kwana anan.... Kin ga ni nayi nan" Ya fad'i hakan sanda ya k'arasa rufewa motarmu tanfol, sannan ya nufo inda muke.

Musabaha su kayi dana cikin motar wanda bazamu iya cewa ga kamanninsa bah balle mu tantance ko  shi d'in wani irin jinsin ne. Burinmu dai kawai mu shige motar. Ash queen has no option than to come with us.Dukkanmu mu matan abaya muka zauna, ayayin da shi kuma Mal. Iroro ya zauna agaba.

Mutumin ya tada motar mu kayi gaba.

Mal. Iroro yace"Insha Allahu idan Allah ya kaimu gobe da safe zan taho da mai gyara ya duba motar sannan na daukota.... Bawan Allah kai dai Allah ne kawai zai iya biyanka da wannan taimakon daka mana wanda kowa ya kasa mana ita... Wallahi ba don Allah ya turo mana kai bah, da bamu san ya zata kasance  damu awannan daji bah don duk wasu dabaru namu sun Kare.... "

Na lura mutumin nan miskili ne na k'arshe don ko tari beyi wa Mal. Iroro bah balle asa ran zai tanka masa.

Alhamdulillah! Alhamdulillah!!.... Tafiyar kusan 30mins mukayi sai gashi mun iso Zaria.Ban san meyasa nake son naji nayi magana da wannan bawan Allahn bah wanda na sanya masa suna da 'miskili'

SHIN SO DAYA NE?Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin