BABI NA ASHIRIN

6 1 0
                                    

*SHIN SO DAYA NE?*
_mijin kaddarata...!_

*HAFSAT HAFNAN*
_Hafnancy..._

*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*

https://my.w.tt/JNyQzygfvcb

*BABI NA ASHIRIN...!*

Cikin mintunan da basu wuce goma ba, Mahmood ya isa kofar gidan Mubarak. K'iransa yai awaya ya fad'a masa cewar ya fito ya sameshi awaje don sauri yake.

Mubarak dake zube akasan carpet yayi saurin mik'ewa don amsa k'iran dan'uwan nasa.Gama cin abincinsa kenan ya kwanta awurin, don shi da kansa ya sake shiga kitchen ya dafa masu abinci mafi sauki wato indomie da kwai.

Kallon Hanan yayi wacce ta tsareshi da sexy blue eyes d'inta tana mai jiran yayi mata bayanin wanda ke k'iransa awaje.

"Matar Mubeen kallon ya isa hakanan idan ba so kike in kasa fita ba... " Ya fad'i hakan tare da kashe mata ido daya.

Murmushi tayi wanda ya sanya har sai da dimples d'inta suka lotse cikin kumatunta, tace"Rufa min asiri mijin Hauwa'u.... Wake nemanka awaje? "

"Asirinki arufe matata....Yaya Mahmood d'inne ya iso... " Don dama ya riga ya fad'a mata cewar zaizo.

Da mamaki tace"Laah! Kaji Yaya shine bazai shigo bah? Sai kace wani bako? "

"Wai sauri yake, barin inje in sameshi kar ya gaji da jira... "

Tun ranar da Labeebah tayi masa gorin rufe gida, toh tun daga ranar ya soma barin gate d'insu abud'e.Sanin hakan ne ya sanya Hanan son jin dalilin daya sanya bazai shigo bah.

Jasmine ce tabi bayansa da gudu ganin ya nufi hanyar waje, sai faman nanata magana d'aya take"Daddy Nima zanje wurin Daddy Mahmo.. "

Bai saurareta bah, ya sanya Kai ya fice tare da rufo kofar falon, don ya tabbatar magana ce zasuyi mai muhimmanci da dan'uwan nasa, shi yasa yaki barin Jasmine d'in ta biyoshi.

Yana jin sanda Hanan tace"Ni dai Allah yasa lafiya dai... "

Mahmood da kansa ke kwance akan sitiyari,yayi zurfi cikin tunani,k'arar bud'e gate yaji, wanda hakan ya sanya yayi saurin d'agowa ya maida kallonsa gun Mubarak wanda yaga ya tunkaro motar.

Lek'o da kansa yayi waje,yayi magana yadda Mubarak d'in zai jisa, yace"Dan'uwa zagayo ka shigo ciki... "

Mubarak yayi hakan kamar yadda Mahmood d'in ya umarcesa.

"Brother barka da dare.... " Mubarak ya fad'i hakan ah sa'ilin daya zauna kan kujerar mai zaman banza.

"Barka kadai.... Ya yinin iyalin naka...? "

"Alhamdulillahi kaseeran!!... Brother lafiya kuwa kake nemana da gaggawa haka? " Mubarak yayi masa wannan tambayar cike da fargabar amsar da zai biyo baya.

"Lil calm down.... Pls kada hankalinka ya tashi,lafiya sumul, sai ma maganar alherin dake tafe dani... " Ya fad'i hakan in a matured voice.

Murmushi Mubarak yayi tare da sauke wata sassanyar ajiyar zuciya,yace"Alhamdulillah! yanzu hankalina ya kwanta.... amma brother shine zamu tsaya acikin mota muyi maganar? Why not mu shiga cikin gida muyi discussing atsanake? "

"A'ah basai mun shiga ciki bah, as I told u earlier, sauri nake... Ina da abubuwa da yawa agabana... Maganar da zamu tattauna bazai wuce juz 10mins bah.....Afterall, tambayoyi kawai nake son na maka, kuma make sure u give me back sincere answers.... "

Ahankali Mubarak ya furta"Insha Allah brother zan fadi maka abinda na sani....Don haka am all ears. "

Ya fad'i hakan tare da tsare Mahmood da idanuwansa yana mai jiran yaji tambayoyin da zai suburbud'o masa.

SHIN SO DAYA NE?Where stories live. Discover now