BABI NA SHA TAKWAS

3 0 0
                                    

*SHIN SO DAYA NE?*
     _mijin kaddarata...!_

  

   *HAFSAT HAFNAN*
     _Hafnancy..._

*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*

     https://my.w.tt/JNyQzygfvcb

         

         *BABI NA SHA TAKWAS...!*

"Hmm guys ni bama wannan ba, wani abu ke mugun damuna yanzu wanda na tabbatar as good friends zaku bani shawarwari na gari... " Ina kaiwa nan, na dan dakata don naji ta bakunansu.

"Muna sauraronki best.... Wacce irin damuwace wannan? Ki fada mana kuma insha Allahu yadda kika yi trusting namu, muma d'in mun daukar miki alkawarin baki shawarwari na gari.....koh ya kuka ce guys? " Leedar ne ya fad'i wannan maganar tare da neman jin ta bakin sauran.

Fresh yace"Yes! dear insha Allahu as good friends, zamuyi sharing wannan damuwar taki atsakaninmu, atake anan kuma zamu had'a kai mu samo mafita akansa, Don haka yanzu ke muke sauraro.. "

Ash queen ita dai bata ce uffan bah, illa kawai girgiza kanta da tayi, alamar itama tana tare dasu.

Ahankali na soma magana cike da tausayin kaina"Ajiya ne mahaifina ya zaunar dani... Yake fad'a min cewar lokaci yayi daya kamata ace an soma zancen aurena don kuwa bah yarinya karama nake kara zama bah..... "

"Tashin hankali wai kawata da gaske kike....? Ash ce ta katse min maganata,tsoro da kuma mamaki suka bayyana kan fuskarta.

Leedar ne ya bata amsa"Ash ke kanki kin san Fadima bata irin wannan wasar, ke dai kiyi shiru karki sake katseta, Ki bari ta kai fullstop kafin kiyi wata magana please... "

Harara ta cilla masa don ita da Leedar Sam basa wani shiri har yau.

"Dan rainin sense kawai... "Hakan ta fada wanda ni kadai kawai naji, tunda ni da ita gab da gab muka zauna, sab'anin su Leedar da suke zaune kan wata kujera dake facing d'inmu.

Na cigaba"Don haka wai ya bani juz two weeks na turo wanda nakeso ah soma magana...wai idan har kai d'in ne dai zaiyi matukar farin ciki, idan kuma bakai bane, wani ne, toh duk da hakan Alhamdulillah haka Allah ya nufa, don shi bazai tab'a mun auren dole ba, Leedar am scared idan su Dad su gano cewar ni dakai ba soyayya muke ba, tsawon lokacin nan duk raina musu hankali muke tayi, tsorona ma bai wuce kada ya kira Dad d'inka ya kara tabbatarwa ko har yanzu kana da interest akaina ko a'ah ba,gashi duk mun gama raina musu hankali....... Please friends ina mafita? Wlh ina cikin rudani...... "

Shiru ya ratsa atsakaninmu na wani lokaci mai d'an tsawo, gani nayi babu wanda keda niyyar magana wanda hakan ne yasa na soma k'araya.

Nace"Friends ya naji duk kunyi shiru ne? Kuce wani abu mana don Allah kada ku kashe mun gwiwa...."

"Ni nama rasa ta inda zana fara... " acewar Fresh kenan.

Ash tace"Kai Kama gode kana da abin fada kenan... rasa ta inda zaka fara ne kawai.... Guy kawai ka fara koda daga tsakiya ne dan ni dai aganina tayi biyu babu wanda d'an fari ke kira da *TWO ZERO* ... Ita bah Leedar bah kuma ni dai kun san bazan tab'a bata shawarar auran Mubarak ba... "

Leedar ne yace"Ke Ash kina da matsala sosai... Bash wallahi Allah ya K'ara maka hakuri don daga ganin Ayshar nan zata iya maida maka da gida ya zama gidan tv idan har ka kuskura kayi mata kishiya, kuma na lura sosai takeson ta tunzura Fadima data bi nata ra'ayin, shin kece zaki zauna mata dashi ?"

Da sauri na dubeshi, nace"Kaga Leedar wallahi nifa na sauya ra'ayi, ka sani ita d'in bata isa ta tunzurani yin abunda raina bai so ba sai in ni d'in ce dai nake da ra'ayin hakan, Mubarak d'in nake son na nuna wa mahaifina amatsayin wanda nake son na aura insha Allah... amma matsalar anan itace Ummansa da kuma family problems d'in dashi yake fuskanta akaina... "

SHIN SO DAYA NE?Where stories live. Discover now