BABI NA SHA TARA

9 0 0
                                    

*SHIN SO DAYA NE?*
     _mijin kaddarata...!_

  

   *HAFSAT HAFNAN*
     _Hafnancy..._

*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*

     https://my.w.tt/JNyQzygfvcb

  *BONUS PAGE*
     

         *BABI NA SHA TARA...!*

 Yammaci ne mai tattare da ni'imomin ubangiji.Sararin samaniya ya mugun hade rai alamun dai kiris ya rage ruwa ya sakko.Ga wani daddadar Iska dake tashi ahankali Wanda na tabbatar awannan lokacin, zuciyoyin al'umma na cike da nishad'i sabida dadin iskar.Adaidai wannan lokacin ina kwance saman gadona, ina operating system, ban wani dade da dawowa daga makaranta bah.

Gani nayi iskar da ake ta soma yin karfi da yawa,hakan ya sanyani mikewa naje na kulle windows din d'akin.

Rigar sanyi na dauko na sanya donni akwai ni da saurin Kama sanyi. Gama sanya rigar keda wuya,naji an doko sallama cikin d'akin. Suhaima ce,ina gama amsa mata sallamarta, na haye gado tare da maida hankali kan abinda nake. Don tun randa taci mutuncin Leedar agabana, ban sake bata wani fuskan kirki ba.

Zama tayi akan gadon,duk na lura jikinta asanyaye yake.

"Yaya Fadima barka da warhaka... " hakan naji ta fad'a cikin sanyin murya.

"Yauwa barkanki.... " Na bata amsa atakaice.

"Lovely sisturh dan Allah ki yafemun da rude actions d'ina na rannan, wallahi bazan sake ba

"Never mind my dear... Haka rayuwar take, babu wanda yafi karfin yayi kuskure...Suhaima na tambayeki mana? "

Da sauri tace"Ina jinki sis... "

"So nake ki fad'a min tsakaninki da mahaliccinki.... Shin akwai wani abu ne daya dad'e yana damunki azuciya? Koh kuma wani ya taba miki laifi ne da har yau kika kasa yafe mashi?.... Ki fad'a min gaskiya kinga baki da 'yar'uwa mai Sonki kamar ni....  " Nayi mata wannan tambayar tare da tsareta da idanuwa.

Lol! Kar kuso kuga yadda yanayin Suhaima ya koma,remember yadda yanayin Wanda yake shirin k'arya yake komawa right? Toh hakan yanayinta ya rikid'e ya koma.

"Seriously sis babu abinda ke damuna wallahi..... amma meyasa kikamun wannan tambayar ? Koh kinji wani abin ne? " Yanayinta ma ya nuna she's so confused.

"No, juz feel lyk asking such questions, Toh naji.... Yaushe zaku soma jarabawa? "

"Ran Monday insha Allah... " acewarta

Nace "Good, Allah ya bada sa'a....ko zaki zamanto free ran juma'a? Jibi kenan?.... "

"Yea... Throughout ina gida... "

"Alright ki shirya..... ranar zamu je ABU tare,want u to study the environment kafin ki samu admission anan.... "

Cike da murna tace"wow sis thank you so much wallahi kamar kin san ina masifar son naje naga environment d'in ABU kafin na sami admission.... amma hope ke da kanki zaki sanarwa su Umma...?"

"Wannan bah matsalarki bace... I will take care of that, tashi ki tafi please kada ki cikani da surutu, kinga ina yin abu mai matukar muhimmanci ne anan kar kisa nayi mistake... "

At once ta mike ta fice daga d'akin ba tare da ta min wata gardama bah.Tunanin Mubeen d'ina ne ya fad'o min arai.Agaskiya ni kaina nasan nayi matuk'ar missing d'insa wanda atake anan naji zuciyata na son taji daga gareshi inji ko yana lafiya.

Samun kaina nayi da daukar wayata,nayi dialing lambarsa,ai kuwa nayi sa'a call d'in ta shiga har ta soma bada wannan boring tune d'in nan wato 'bum-bum'

SHIN SO DAYA NE?Donde viven las historias. Descúbrelo ahora