BABI NA UKU

14 2 0
                                    

*SHIN SO DAYA NE?*
     _mijin kaddarata...!_

  

   *HAFSAT HAFNAN*
     _Hafnancy..._

*Zazzafar soyayya, Cin amana, mugunta da kuma Sadaukarwa*
 
https://my.w.tt/JNyQzygfvcb
      

         

         *BABI NA UKU...!*

Yau ta kama wata larabar wacce ta kasance sati gud'a kenan da fara haduwata da Leedar, kuma tun daga wannan ranar bamu k'ara haduwa ko ahanya ba. Hakan kuma ba karamin dadi yai min ba, don aganina ya kulle chappyna ne gaba daya. Ash queen ce ma take ban dariya data takura kanta wai tana neman hanyar da zata rama wulak'ancin da yai mata take.
   Abinda ban sani ba kuwa, ashe tun aranar da muka rabu bata dad'in rai ba dashi Leedar d'in, sai ya sanya aka fara masa binciken ko ni din 'Yar wacece, to da yake ni ba wani yawo nake acikin makarantar ba, hakan yasa ba'a wani sanni sosai ba, Sa'annan kuma wanda ya sanya suyi masa binciken akaina, basu gane wani level da dept nake ba, Ayadda yai musu kwatancena ne ya sanyasu bin 'yan mata masu d'an yanayin kamanceceniya dani, sai suke kawo masa wrong details na 'yan matan amadadina,  sai yace "Bana tsammanin itace"... har takai ta kawo sai suke taho masa da 'yan matan ko za'ai sa'a ina ciki, 'yan matan da zarar sunji cewar Leedar ke son ganinsu, to da gudu suke zuwa don aganinsu cewa zaiyi yana sonsu.
     Shigowata makarantar kenan, na k'arisa parking lot na paka motata. Cike da aji na fito cikin shiga ta alfarma ina takawa sannu ahankali cikin natsuwa, Sai ganin Wata bak'ar jeep nayi ta gifta ta gabana da gudu wanda har sai dana d'an tsorata na tsaya cak awuri daya ina kakkame jiki, nabi motar da kallo baki sake..Da gudu kuma naga motar na dawowa da baya, daidai gabana aka tsaya cak!   Zubawa dukkan ilahirin motar idanuwa nayi ina mai son ganin Fuskar wannan mahaukacin direban wanda babu kamarsa, Wani hadadden gaye ne mai zafi naga ya fito daga b'angaren direba wanda ke nuni da cewar babu tantama shine mahaukacin da nakeson gani. Kallo daya yayi mun naga yayi saurin maida dubansa cikin motar yana fad'i da k'arfinsa"Malam na gaya maka ita ce amma ka k'aryatani, Fito ka ganta da idanunka "Yana gama fadin hakan, sai kawai naga an bud'o k'ofar mai zaman banza da k'arfi..Daga kafafuwa na soma kallon irin wankan da aka dauka, sannu ahankali nakai kan fuskarsa... Gabana ne ya buga wani irin ganga adalilin fuskar dana yi arba da dashi, halittar da atunanina ta gama watsar da lamarina irin har abada d'in nan. Kun san waye? Its Freaking Leedar again!
     Fitowa yayi daga motar ba tare da ya rufe murfinsa ba, sannu ahankali cikin takun k'asaita ya soma nufoni ina d'an jajja da baya, k'irjin nan nawa kuwa tamk'ar zai fad'o k'asa tsabar tsoro da fargaba, Soma maganarsa ce ta sanya ni dakatawa daga inda nake, Azafafe yake fad'in" Tun awannan ranar na soma nemanki amma ban sameki ba, har kudi na rabar d'an abinciko mun ko da d'an digis na labarinki ne, amma hakan bata samu ba, amma gak'i yau tsaye agabana ak'yauta ba tare dana biya ko kwandala na ganin naki ba " Cak! Ya tsaya agabana gami da watsa hannaye cikin aljihunsa, sai daya had'iyi wani miyau wanda na tabbatar duk na tak'aicina ne kan ya cigaba"Wacece ke da har mutum kamata yake miki magana amma kika zab'i dizgashi agaban idon mutane fiye da goma awuri ? Ni nan da kika ganni 'yan mata murmushina kawai suke san gani amma har iyau basu samu wannan fuskar ba, ke k'in samu, har ma na zarce dayi miki magana da kalami masu dad'i, amma duk baki dubi wannan damar da kika samu ba har kika iya wulak'antani ? Shin wani sa'a ne kika taka awannan ranar kafin ki shigo inda muke har kika samu na kalleki, Kuma wai har ni Ali Haidar na kai ga yi miki magana ? Infact Ina san in sanni ko wanene ubanki a fad'in garin Zarian nan ?"
   Sosai maganganunsa suka b'akantamun rai, Kafin in kai ga bashi amsa naji ance"So kake kasan ko ita d'in wacece ko? Well, d'iya ce ga fitacce kuma shahararren alk'ali wanda ya shahara kwarai akan aikinsa *CHIEF JUSTICE MUHAMMAD SA'AD MAI NASARA* , Nasan ka wayeshi sosai kuma ka girgiza ko ? Dak'yau haka nakeso, inga hantar 'yan maza ya kad'a, inga murdadd'en jikin wanda ya amsa sunansa da d'a namiji yana jijjiga, kuma burina ya cika d'an gaka atsaye agabana, ayanzu baka da maraba da Solombiyo, to idan kaji ana Fadima Mai Nasara to itace wannan, kaga kuwa ayanzu dodadd'iyar k'wak'walwarka zata reraye, ta tace sannan kuma ta tantance cewar matsayinku ba d'aya yake ba, sabida ita d'in d'iyar shahararren alk'ali ne wanda duniya tasan da zamansa, kai kuwa d'an matsakaicin mai kudi ne wanda ina tsammanin iyakacin garin Zarian nan ne kadai ma suka san da wanzuwarsa, Sa'annan kuma naji kana ikrarin wai an maka  wulak'anci ? Ashe ba dad'i ni kamin ? Ko kuwa Zuciyarka ce kadai take da jini, nama da kuma feelings da har zata Ji zafin abinda tayi maka ? ka tab'a tunanin abinda kayi mun arannan ka k'yauta ko baka kyauta ba? idan har baka zauna kayi wannan tunanin ba to ina mai tabbatar maka da cewa duk ilimin da
ake fad'in kana dashi to ni ban gansa atattare dakai ba, hasalima zan iya cewa k'wak'walwarka bata ja irin ta masu hankali, sabida haka d'an saurayi da sauranka, Kuma bara kaji wani abu" ta furta tana karkad'a 'yan yatsu..."Idan har kai d'in dabi'arka ce na cin mutunci 'yan mata, to tabbas ka sani akan Aysha Adam inkiya Ash queen wallahi ka daina "
    Bud'e baki nayi nabi Ash queen da idanuwa wacce ke tunkaro inda muke tana jifansa da wa'ennan zantuttukan tin kan ta kariso inda muke, sosai na jinjina irin k'ok'arinta na gaggayawa Leedar maganganu son ranta, Abokin nan nasa wanda suke tare ne naga yana yunk'urin kai mata mari, da sauri Leedar ya dakatar dashi ta hanyar rike masa hannun dazai kai Marin, Cikin zafin rai abokin yace"Haba Leedar kana fa gani wannan kucakar yarinyar take fad'a maka maganganu son ranta abinda wata 'ya mace bata taba maka ba, kuma Abin mamaki ka tsaya kana kallonta, haka wannan mai fuskar babyn robar kana mata magana rannan ta shareka ta maida ka soko atsaye, ak'arshe ma kada kai tayi tayi wucewarta, yanzu kana nufin kace mun k'ok'arin shanye wannan iskancin kake koko me shirunka ke nufi ne ? Ni kuma da nake shirin daukawar kana neman hanani, haba Abokina yaushe ne ka soma dauk'ar raini da amsar wulak'anci daga hannun 'yan mata? 'Yan matan ma low class babe's.. ? "
Doka masa tsawa Leedar yayi"Fresh it's okay, Babu ruwanka dani, bamu kasa dakai ba balle ka k'washe, kai dai zuba idanu kasha kallo " Cikin murmushi wanda nake tunanin na k'arfin hali ne naga ya juya dak'yau yana fuskantar wanda aka k'ira da Fresh, yace"Start calming down guy, saurin dauk'ar matakin na menene ? Ko kuwa mantawa ne kayi da ko wanene Leedar ? " murmushin shima ya maida masa dashi yace"Kuma fa hakane kayi gaskiya, ko kadan ban manta irin sharri da kaidinka ba "  Leedar ne ya juyo garemu yana nuna Ash queen yace"Color Ash kike ko ? To ki sani duk wulak'ancin da kikai wa Leedar sai k'in biya bashinsa , d'an baayi wata 'ya mace da har zata takani ta wuce lafiya ba, har yanzu kuma baayi ta ba, kuma ba za'a tab'a yinta ba , Ke kuma " ya nunoni da 'yar yatsa "Ina nan dawowa gareki d'an har yanzu ban gama dake ba, bara na soma nutsar da wannan shit d'in ta kusa dake sannan na komo gareki d'an ga dukkan alamu so kike muyi wasar kurame, Bash mu tafi " yace da Fresh abokinsa..
Yana gama fad'in hakan suka shige cikin mota suka figeta kamar zasu tashi sama ayayin da suka bar mana K'ura na mana shawagi.Abin haushi da dariya Ash queen k'amar zatai hauka d'an bak'in cikin rashin basu amsa da bata samu tayi ba, Har da fa cire takalmanta masu d'an tudu tana jifar bayan motarsu dashi, ni abin dariya ma ya bani.
    Juyowa tayi gareni kamar zata sauke kwandon masifar akaina, tace"Fadima anya kina da hankali kuwa ? Baki ga irin cin mutuncin da wa'ennan tsamayen gayun suka mana bane ?Wancan d'an akuyan Ma har kiranki yai da babyn roba, amma gak'i anan kina dariya kamar wata tababb'iya kin kasa daukar mataki akai, wallahi Fadima miskilancin nan naki watarana sai ya kaiki ya baro d'an nama lura k'in dauk'i abin nan nasu Leedar da bakin wasa "Maganganun Ash queen sun kaini wuya amma sai na danne na batsar, nace"Naji kin ambaci daukar mataki,  Ina kike sanda abokinsa ya kiraki da Kucaka? Wani matakin ke kika dauka akai ?... kin tab'a ganin wanda hakurinsa ya bashi kunya koya tozartashi ? K'awata shawarata agareki shine, ki fita aharkar su Leedar sabida Wasu mazan ko kadan basu da imani, zasu iya aikata wani mugun abun akanki amma bawai fata nake ba, idan sunzo inda kike pls kiyi kamar baki san da zuwansu wurin ba, idan kuma suna sossoka miki maganganu to ki ari kunnen kurame kamar yadda kika ga nayi ki sharesu kamar kashi d'an nama lura abin yafi ci musu rai, amma idan kina tanka musu shi yake k'ar sa suna jin dadi na cin mutuncinmu, My dear atleast for once ki koyi shanye ire iren ababen nan, hakan ne kadai zai nuna irin ajin da kike dashi a idon mutane, amma yawan surutu da kuma masifa Sam ba mutuncin 'ya mace bane d'an yakan janyo arainata "
   fuskar tausayi nayi mata nace"pls my Aysha ki rage yawan tsiwa da masifa... Daga yau ina son ki kulle babinsu ALI LEEDAR.. Kinji Ayshata ?"Na lura maganganuna sunyi matukar tasiri ga Ash queen don yadda naga jikinta yai bala'in sanyi lokaci guda. Ba zato ba tsammani, abin mamaki abin tausayi, Hawaye naga Ash queen ta soma zubarwa ta kamo yatsun hannayena tana d'an murzasu tace"Insha Allahu Fadima na dau miki alk'awari daga rana irinta yau na canza, zan zamo kamarki sabida ina bala'in san irin lifestyle naki, sannan zancensu Leedar Kuma I promise u na kulle babinsu ayau dinnan, babu ruwana dasu, ko sun shiga harkata hak'uri ma zan k'ara basu... Fadima Sa'ad u ar more than a friend to me...ina k'aunarki matuk'a " Tana gama fadin hakan ta rungumoni tana kuka, na shiga jijjiga mata baya ina fad'in"Haba Aysha meye haka? Kukan na menene ? ya isa hakanan kinga mutane sun fara kallonmu, kinji pls? "

SHIN SO DAYA NE?Donde viven las historias. Descúbrelo ahora