*******
Tunda suka shiga hospital din sukayi parking sannan ya fito, escort na biye dashi abaya, ya nufi assembly ground dinsu inda yaga gabadaya staffs din suna jiran isowarshi, anan akayi introducing dinshi as The new commander of the hospital, and ba wani jimawa zaiyi ba 7month zaiyi anan kawai...... welcoming dinshi suke tayi suna murna don tun kafin yazo labari ya karade hospital din cewa za'a kawo New commander Hafiz Abubakar and kowa Fadi yake ai yana da kirki sun dade suna Jin labarinshi......anan aka rufe taron kowa ya tafi office dinshi, Hafiz Abubakar ya shiga office dinshi Wanda ayau zai fara aiwatar da aikinsa kuma yana so yayi aikin dakyau dukda bawani dadewa zaiyi ba Amma ya dau alkawarin yin aikin dakyau, dukdama yana gamawa za'a kara masa Rank amma shi hakan bai dameshi ba, yana dai so yayi aiki tsakani da Allah, Although he knows that he have to achieve his goal, but sometimes we don't have to work hard for our own good.
Haka ya cigaba da having thoughts at thesame time yana aiwatar da aikinsa.

*******

Bangaren su Jiddah

Momma ce zaune gefen gado, hannunta dauke da bowl na glass da spoon hadin friut salad ne wanda yasha madara, momma ta debo a spoon takai bakin Jiddah wacce ke zaune saman gadon ta jingina da pillow ayayinda take sanye da doguwar riga na material maroon color kanta kuma ta yafa black veil, ta bude baki kadan aka sanya mata fruit salad din abaki, da kyar take taunawa Amma fah fuskar nan tata ayamutse ga wani hade rai datayi  yadda kasan kashi aka sanya mata abaki.
Wayar tace ta fara ringing takai dubanta ga right hand dinta inda phone din ke ajiye.....sannin right hand dinta shine mai ciwon hakan yasa ta tsura wa hannun idanu wanda ayanzu bata iya Koda motsi dashi tsabar tsami dayayi mata, girgiza kai tayi ta sanya Left hand ta dauko phone din ta amsa wayar sannan ta Kara a kunne, hade da cewa Yaya Faisal Ina kwana.
Cikin wayar aka amsa da lafiya lau Jiddah ya karfin jikin naki?
"Da sauki Yaya Faisal"Amma nikam fushi nake dakai baka zo ka dubani ba,
Lord! Ya furta cen kuma yace Jiddah waya ce miki ban zo ba, nazo fah kuma alokacin baki farka ba, kina ta bacci, momma batace miki nazo dubaki ba.
"Ta fadamin ta amsa" Amma meyasa baka jira na farka ba?

Ohhh my little girl kiyi hakuri kinji an kirani a office ne, shine na tafi am sorry kinji......"uhmmmm toh Yaya Faisal ai komai ya wuce".
Dariya Faisal yayi sannan yace
To thank you kinji, Ina ta faman kiran Momma Amma shuru bata picking, and I decided to call you, ina ta shiga ne?
Gatanan fah Yaya and wayar ta I think ta Sanya a silent ne tun jiya.....cikin wayar akace uhmmmm kukam ai haka kuke keda momma kuyita faman sa waya silent and flight mood bansan dalilin ku nayin hakan ba ,kuma ke Kika koya wa momma, ko dayake dama ance zama da madokin kanwa.....ta zumbura baki kaman Yana kusa da ita tace Ya ya , shikuma yace yes ai gaskiya na fada my little girl.....bani momma din nayi mata magana
"Jiddah tace toh" ta mika wa Momma phone din.
"Assalamualaikum momma ta furta bayan ya amsa ne yace "Momma na fito agida yanzu Ina shikenan abinda kuke bukata?"
"Momma tace eh sai ka karaso kawai" okay momma Faisal ya amsa sannan ya kashe wayar.
Momma ta dubi Jiddah tace, Jiddah nikam ki daure ki karasa shan fruit salad din kafin Yayanki ya kawo breakfast kinji......Amma Jiddah ko gizau kaman ba da ita ake magana ba,
Momma tace Jiddah wai nikam ba dake nake magana ba,and kikamin shuru ki daure kici kinji Jiddah na.
Jiddah tadan yi ajiyar zuciya Wanda yasa Momma dauka kaman ta sauko ne daga kan mulkin data hau tun jiya tunda ta farfado ta duba bataga sojan nan ba, toh shine tafara rigima ita ala dole mezaisa su Fatima su barshi ya tafi bayan bata warke ba, Harda cewa Ina shi yaji mata ciwon toh ae bai kamata abarshi ya tafi hakanan ba, after all ai ciwon bai warke ba so babu inda yakamata ya tafi, sai kuma hawaye kuka kaman karamar yarinya wai ita sai an nemoshi kafin zatayi shuru.....ajiyar zuciya momma ta kumayi alokacin data tuna sai da suka kira Ummi kafin Jiddah ta yi shuru, amma dukda haka batayiwa kowa magana har su Fatima da mamanta suka tafi dayake maman tazo daukar ta...Momma ji tayi Jiddah na cewa Momma Abba, Abba zan kira kafin naci wani abu banji muryar shiba tun jiya.
Ya ilahi! Cewar Momma aranta tace another problem,afili Kuma sai tace call him Jiddah nikam rigimar ki ta ishe ni.
Jiddah ta tura baki kaman mai Shirin yin kuka jin ance rigimarta yayi yawa tace Sorry my momma please karki bata rai da Jiddah, ai wannan sojan ne yasa raina ya bace shiyasa amma ni bana so ranki ya baci ta karashe maganar tana kokarin dialing contact din Abba.
Momma tai shuru tana kallon Jiddah so da dama haka Jiddah take tana da shagwaba, amma batada raina na gaba da ita sai dai idan kayi mata ba daidai ba, Amma halayenta masu kyau yawa garesu don saika zauna da ita kake fahimtar ta dakuma kyawawan halayenta..... Momma tai saurin cewa to karki kira Abba yanzu, zaki tada masa hankali ne kibari sai Yayanki yazo kinji.

Jiddah ta zumbure karamin bakinta tace shikenan....sosai Momma tayi ajiyar zuciya wanna karan dan tasan da ta bar Jiddah ta kira Abba da drama da za'ayi sai yafi na jiya ahankali take bata fruit salad din har ta shanye.....kana ta sauka daga kan gadon tace Momma zandan zagaya waje na motsa jiki na dawo...... "Momma ta zare idanu tace Jiddah motsa jiki dai" naga ko agida ke bame son fita ko tsakar gida bace and yau kuma........
"Momma please"
Okay toh kije amma kada ki dade iyakarki area dinnan kada ki wuce wajan kina jina.
"Eh Momma ta amsa tayi waje da sauri abinta,
Momma ta girgiza kai tana cewa Jiddah hmmm tana tuno yanda akayi drama kafin iyayenta suka yadda ta amso Jiddah, dukdama Jiddah na tsananin son Momma hakan yasa ta yadda ta biyo ta kd.....tashi tayi tana gyara ward din.

Jiddah na fita tayi hanyar wani corridor har tayi nisa ta fita waje kaman ance ta waiga hannunta na hagu, tsaye ta hango su, ahankali tace wancen kaman Yaya Faisal.....ta kuma kai dubanta gareshi, Sanye yake da uniform na police black trouser sai shirt din royal blue ayayinda shoulder dinsa ke manne da star har uku, Dogo ne sosai kuma black in completions sai dai kallo daya zakai mashi kasan fulani ne yanayin gashin kanshi mai laushi Kuma ya kwanta hade da saje Mai kyan gaske wanda yasha gyara kuma ya kara fito da asalin kyan nashi dukda force ba'a cika son suna barin gashi any how ba Amma shi babu ruwanshi....  Jiddah tasaki ihu da karfi tace Yaya Faisal cike da murnar ganinsa" shima damamaki ya kalli wajan da aka kira shi nan ya ga Jiddah ce dukda yana mamakin ganinta awaje haka how comes tabar ward din ta fito waje kuma, Amma hakan bai hana shi yin murnar ganinta ba, murmushi ya sakarmata yace Jiddah
Tunda ta karaso wajan tafara zuba kaman an sa mata  battery,tace" Yaya Faisal tun day b4 yesterday ban sake ganin ka ba, yauwa dama akwai aikin danakeso kamin Yaya "Faisal dake sauraronta yayi murmushi yace wani irin aiki Jiddah? Jiddah ta numfasa sannan tace wai daman wannan sojan daya jimin ciwo nake nema, so nake idan na kamashi ka tafi dashi police station  ka kulle minshi har sai na warke sannan ka bude shi, Yaya Faisal ji hannuna fah tun jiya yake min ciwo bana iya motsi dashi sai kuma ta saki kuka wanda idan kaga yanda tayi reacting dole tabaka tausayi tana cewa Allah sarki hannuna, shikenan na koma mai hannu daya....taja majina ta goge hawayen fuskarta sannan ta cigaba dacewa Yaya Faisal zaka tayani neman shi don Allah muje mu kulle shi saboda yaji min ciwo, Ni bazan raga mishi ba kuma sai na koya mai hankali tunda yasan halin danake ciki kuma ya tafi ya barni maimakon ya tsaya awajan har sai na warke.....uhmmm ai ya kara ma kanshi laifi,yanzu laifinshi 2✌️ tayi nuni da dayan hannun tana gwadawa wanda yake tare da Faisal ayayinda takai dubanta ga fuskarshi ita ala dole tana basu labarin abinda wancen guy din yayi Mata, Amma me zai faru......kallon shi tayi at thesame time hannunta na nuna alamar ✌️, zare idanu tayi lokaci daya sannan tace da karfi Yaya Faisal wannan ne, wlhy shine wanda yaji min ciwo ka kamashi kada ya gudu Allah shine yaji min ciwo jiya......kana ta kalli sojan tace kaine Allah, sai kuma ta murguda masa baki hade da harara sannan tace zaka sani yau, bakai ka iya guduwa ba, baka iya tsayawa ka wanke laifin ka ba,yau zaka gane ai....dama nace bakasan wacece Jiddah Junaid ba, Amma still ka tafiyar ka ko ajikinka Koh to sai nasa Yaya na ya kulle mun kai, inga ta inda zaka kara guduwa, ta tura baki gaba tana kallonshi daga sama har kasa, sai kuma tace kana ji koh ni babu ruwana da wai ka sanya kayan soja wama yasani ko aro aka baka kayan, ko kyau ma basuyi maka ba ai gwanda ka cire........ta kalli Yaya Faisal da hankalinshi ya gama tashi tace Yaya Faisal kabashi shawara idan ka kulle shi kace mishi uniform dinnan baya mai kyau ta fada cike da nuna seriousness a fuskarta.
Sosai abin da Jiddah take Fadi wa bawan Allahn nan ya tsorata Faisal duk da yasan halinta Amma hakan bai hanashi kara mamaki ba, don wannan sojan ma ko da police officers ne to ya fishi rank taya ma zai iya kama shi har ya kulle shi, ita Jiddah bata ganin rank dinshi ne shine fah commander na hospital din, dayan zuciyanshi tace dashi to ai bata sani ba shiyasa, karkayi blaming dinta.....lokaci daya yaji ba laifin Jiddah bane Amma yasan yaddah zai yi handling dinta.
Ya kalli Jiddah wacce sai faman hararar sojan take yi tana murguda masa baki, ya dafe kanshi yace ya Ilahi! Sannan ya kalli Hafiz da tun da Jiddah ke magana yake ta kallan ta yana mamkinta....hannayensa sanye cikin aljihun wandonsa Faisal shikanshi sai da ya yaba da irin kyan da uniform din sukai ma Hafiz donshi tunda yake bai taba ganin wanda kakin soja ya amshi jikin shi sosai ba sama da Hafiz.....Amma lokaci Daya Jiddah ta kushe shi.....Ajiyar zuciya yayi hade da dafa shouldern Hafiz yace am sorry sir she is my sister and on behalf of her Ina bada hakuri batasan ko kai waye bane shiyasa take fadan haka,Am so sorry sir.

Hafiz ya girgiza kai Yana murmushi lokaci daya Kuma kyan fuskarshi ta bayyana karan hancinshi ya fito sosai ya dubi Faisal yace don't worry i understand.... anyway ni zan koma office yanzu idan kana bukatar wani abu ka sameni a office dina....abinda yace kenan kawai ya wuce yana kallon Jiddah wacce take kallon shi cike da tsana a fuskarta....har sai da ya bacewa ganinta ta dubi Faisal tace Yaya Faisal why?

******************
Vote
Comment

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now