Da sauri yaran suka hau girgiza kai dayan karamin har da cewa Noooooo granny bana son allura Ni.

Yauwa good boy to ku shiga mota kuyi wasa kafin mutafi gida Koh

Suka Shiga mota abinsu, daka gansu sekaga Basu da wani damuwa tunda basusan halin da Ummin tasu take ciki ba, su kawai dai ance musu Ummi zata haifa musu baby ...... Babban ne Mai shekara tara ya ke dan fahimtar abubuwa ba kaman karamin ba.

Mama tace toh.sannan suka koma cikin dakin haihuwan.
Allah cikin ikon sa kuwa tana shan rubutun after an hour tafara jin azabar ciwon mara, ji takeyi kaman marar zata fashe.....ciwo ahankali ya farayin yawa, Addu'o'i kuwa babu wanda baya zuwa bakinta......tana farawa Mama zata karashe, Mama na farayi mata ita kuma zata karashe.....Ammi kam tasha Addu'a dukda tana waje basusan abinda ke faruwa ba,fadi take Ammi nah Allah yai maki Albarka, Allah yabaki gidan aljanna, Ammi ki yafe min duk wani laifin danai maki da wanda na sani da kuma wanda ban sani ba Mama ki kiramin Ammi don Allah......sai kuma nishi haka dai take ta fama,
Mama na fada Halima addu'a akeyi please, kiyi addu'a and stop shouting kinji Yar mama....to daga nanne ta somayin shuru din hade da cigaba da Addu'o'i
har tsahon awa uku kafin nurses din suka tura Mama waje sannan suka fara duba matar.

Nurses basu jima da shigowa ba, Halimatu tai yunkurin nishi mai karfi at thesame time kan jariri yafito, daganan suka taimaka mata suka fito da babyn..,.sai faman kuka babyn keyi anguwar zoma wacce keta faman goge babyn da olive oil tace MashaAllah 'ya mace kyautar Allah.

Koda suka gama da matar da babyn sai suka kira Yan uwan nata, batareda bata lokaci ba suka shigo suna duba Yar tasu hade dayin murnar ta sauka lafiya,sai faman daukan baby akeyi hardai tazo hannun Ammi

Mama ta ansa jaririyar ta tsura Mata idanu Adoringly" tace MashaAllah Ammi duba kiga kaman lokacin dakika haifi Halima"

Ammi tai murmushi cikin wasa tana kallon Yar tata tace wannan Kam ai tafi Halima kyau Mama  duba kigani dai, sannan ta kalli Halimatu tace shine wannan karan akayimin kishiya koh, bakomai ai kyautar ubangiji ce....Ina godiya sosai🙏
Dukkansu saida suka dara kafin
Halima dake kwance ta lumshe idanu tana jin son mahaifiyar tata na kara shiga cikin zuciyarta, sannan tace Ammi kin manta kin taba cemun kina son kishiya lokacin kafin na haifi Saif...........tayi shuru tana kallon Ammi.
Ammi ta zare idanu ta kalli Mama kafin tace Mama kinajin mara kunyan yarki ko wai fah..............

Ahhhhhhh Ammi kibar min ya'ta ba ruwanta, nikam ma naji dadi da akai maki kishiyar Kinga kin samu mai takura maki.

Ammi ta tabe baki dama ai dole kibi bayanta,  don bakinku daya kukam.... ta dubi yara maza guda biyu tana cewa look she is your sister, ku dauke ta, kubata blessings dinku .

Karamin yayi murmushi mai hade da dariya ya mika hannu zai amsheta Amma Ina babban ya rigashi, zasu fara fada kenan, Ammi tace shihhhiiiiiii ku dauke ta one by one.

Daganan dai gida suka koma don Basu ma kwana a asibitin ba wuraren sha biyu suka nufi anguwan su, babban gida ne gidan inda suka shiga sashin da aka sauke su gidan yayan Halima ne (babban 'Da ga Ammi )

Asalinsu
********

Ammi da Mama kishiyoyi ne Kuma matan Alhaji Ibrahim Muhammad.
Ibrahim Muhammad mazaunin garin Jibiya nee tun asali kafin yasamu budi yayi arziki lokaci Daya kuma ya koma katsina anan ya hada kan iyalanshi yakuma ba ma yayansa tarbiya, hade da sauke dukkan hakkokin dasuka rataya akansa dakdama Dan shi Daya namiji.amma matanshi hudu kuma ya aurar dasu duka ayanzu.

Ammi tana da yara uku
Muktar shine babba Kuma shi kadai ne namiji awajan Ibrahim Muhammad...Muktar kasuwanci yakeyi a nijar (maradi), to which  sanadin zaman shi a Jibiya kenan sannan sai Maryama tana kaduna tana aure da yara biyar. sai autan Ammi  Halimatu shekaranta 9 da aure tun 1988 ayanzu ita a Nijar tayi aure an kawota Jibiya ne saboda tasamu kulawa daga wajan danginta dukda ba haihuwanta na fari bane, ya kasance duk haihuwan ta sai tazo gida saboda irin wahalan da takesha lokacin nakuda. Ammi na matukar ji da Autan nata.
Diyan Halimatu uku, Babban sunanshi Muhammad Junaid shekaran shi 9yrs
Na biyu sunanshi Saifullah Junaid mai 6yrs sannan jaririyar da aka haifa yanzu.

Bangaren mama abokiyar zaman  Ammi yaranta biyu Duka mata suma duk sunyi aure suna cikin garin Katsina.

Ammi taso a tafi da Halima katsina Amma mijin sam ya hana, wai sai dai su taho, ai mata komai a jibiya.....ya suka iya dole suka taho aranar datafara nakudar , ayanzu Ammi zata koma katsina da yara Mama Kuma zata tsaya ta kula da Halima.(Ummi)

Ana gobe suna mahaifin jaririya
Mai suna Junaid Muhammad (Abba) ya zo ganin baby, babu irin siyayyar da baiyi ba kasancewar akwai kudin, kuma yana ji da wannan haihuwan saboda burinshi ayima mahaifiyar shi takwara wacce ta rasu tsahon shekaru bakwai kenan.
Gaba daya yan'uwan halima sun iso aranar gobe suna, sai faman hidima akeyi.....Ranar suna kuma yarinya taci sunan kakarta Hauwa'u Jiddah Junaid
(Sunan maihaifiyar Abbanta).
***********
Halima(Ummi) na zaune a falo, Abba) na gefenta yana wasa da Yara yace Ummin Saif dama Ina son muyi wata magana mai muhimmanci.

Ta dube shi cike da tattara dukkanin hankalinta akan mijin nata tace Abban Saif Ina sauraronka"

Ya numfasa sannan yace Idan kika gama wanka zamu koma katsina da zama inshallah , ya karashe maganar yana dubanta cikin zuciyarshi yasan bakaramin farin ciki zatai ba saboda yasan burinta kenan, dama bata son zaman Nijar tafiso tajita kusa da Ammi da Mama.

Cike da murna, tace Katsina Alhamdulillah Allah ya amsa min addu'a ta Abban Saif,Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya.

Ameen Summa Ameen, ya fada sannan suka cigaba da hiransu.
Muhammad da Saif kuwa sai wasa sukeyi ajikin Abban nasu sunayi suna taba fuskan Baby Hauwa'u, Ummi na kwabar hannunsu saboda dasun taba saita yamutsa fuska, sukuma suyita dariya, Abba Kuma nacewa ki rabu dasu ba kanwar su bace.

Abba ya dubi matar tashi yace Nikam a canja ma mamana suna, In ba haka ba kuma ni nayi mata abina.

Ummi tai murmushi murya kasa kasa tace JIDDAH

MashaAllah Abba ya furta lallai kaman kinsan abinda ke cikin raina kenan....Allah ya raya mana JIDDAH Allah yayi wa rayuwarta Albarka.
Ameen ya rabbal alamin Ummi ta amsa.

Happy Reading 🤗

*************
Vote
Comment
Share please

RAYUWAR JIDDAH ✔Where stories live. Discover now