LAIFINA NE 31

93 11 2
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

_Where are you my daughter hannah❣️ Your page is here, Kiyi yanda kikeso dear, love you With All my heart❤️_

*PAGE 3️⃣1️⃣*

Muhseen Tsayawa sororo yai a wajen, aranshi yace meyasa wasu matan sa basuda kamun kaine, yanzu be wuce akan wani abu kadan ta jefa kanta a wannar harkan, Wasu sa basa tinanin mutuwa, ji yai inama bai fitoba dan wannan mummunar abunda ya gani, jiyai ya kara tsanarta shi sam bega ma abun burgewa a tare da ita, kenan abunda yake zargi da gaske ne tunda gatanan bata da lafiya kuma duk alamu sun nuna Asibiti zasu, yar kamar tsaki yaja yai shigewarshi moto, ba gida ya wuce ba, wani Shagon wayoyi ya nufa yasai yar karamar waya da New sim yasaka, Sannan ya dawo gida

Koda ya dawo gida babban amininshi ya gani Lukman, Wanda ranar da suka fara ganin fauxeey yacemai kawai ya kyaleta dan bata da kunya

   Yana ganinshi ya tino da maganar abokinshi, yadan bata rai, Lukman ne yace yadai? Dagamai hannu yai alamun besan magana yanzu, Lukman da yake ya gama sanin halin abokinshi yaja bakinshi yai shuru, yace to how's your health Umma tace bakada lafiya,

Da sauqi kawai yace, Ya sama waje ya zauna yai shuru, tino yanda yaga Fauxeey a motar bobo yakeyi, Se kawai yai tsaki,  Lukman kuma Yace Allah ya kyauta...

****
    Su bobo Kuwa sun isa asibiti, anan aka gwada Fauxeey akace cronic
Ulcer ke damunta, Allurai akai mata sannan aka basu wasu magunguna, kuma dr yace tadena cin yaji da mangyada ta kiyaye kuma lukutan cin abincinta,

Fauxeey tace Ok Nagode

Bobo nan take ya biya kudin, Fauxeey tamai godiya yace ba godiya tsakaninmu

Ahanyane yace me kike bukata? Tace ita bakomai, Murmushi yai yace abincifa? Tace ita A'a ta koshi,

Yace yaushe kikaci abinci? Daga asibiti muke ai, kinajin abunda Dr yace ai, ita dai tace ta koshi

Kallonta yai yace kee, ta kalleshi yace ba'amun musu, duk abunda nace kawai ki bini toh

Nan take ta tina da halayen Bobo Tuni ta shiga hankalinta, 

Wani babban wajen cin abinci ya samu yai Parking, Ya fito yai musu ordering dan yasan kosun koma gida ba wani aikin zata iyaba,

Yagama ya fito

Sannan ya biya wani babban plaza yai mata siyayyan kayan kwadayi ya zo ya ajiye a bot,

Ahankali yake tafiya, bini bini yake tambayar yakafiyarta, sedai tace dasauqi

Driving yakeyi ahankali har Suka dawo gida

Me gadi yasa ya shugo  da kayyakin dakinshi, Ita kuma Fauxeey ta wuce part din hajiya, Bobo ne ya shugo yace Sorry na manta hajiya basu dawo ba, Wani aiki ya kiresu a chan senan da One month zasu dawo

Gaban Fauxeey yace Rass, amma bata nunamai ba tace Ok Allah yakaimu, Yace Ameen kizo muje

Ba yanda ta iya dashi, haka ta bishi gabanta na fadi zuciyarta kuma addua kawai takeyi, tace lalle Ina cikin hatsari, Wata zuciyar tace langwabewa zaki har ki cimma burinki, Tace aiko haka za'ai

   Tana shiga dakin Already ya baje mata abinci a plate, yace Oya zo kici, Na koshi ta cemai

   Sauya fuska yayi yace bana ce maki banason musu ba? Jikinta na rawa tazo ta zauna taci a binci har turawa takeyi dan ta koshi, seda yaga ta kusan yin amai sannan yace ta dakata

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now