LAIFINA NE 18

74 13 2
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

    _Dedicated to all Masoyan novel dinnan...Ina ganin ruwan comment Thank you all😍🤩😍_

*PAGE 1️⃣8️⃣*

  Fauxeey Sallama taiwa maman zeenatu tai mata fatan alheri sannan ta suri dan karamin jakarta ta makaleshi a hammata, Da zasu tafi Gidan kashe wayarta tai tasa a jakarta

Suna tafe Fauxeey na adduan Allah yasa ta sama karbuwa, Sunyi tafiya medan Nisa a kafa, ga chabalbali ya bata musu kafa kasancewar anyi ruwa, Wani Katafaren Gidan Sama suka Tsaya a kofar gidan Fauxeey dai cike take da fargaba

Knocking sukai, megadi yazo ya bude musu gida, da yake sunsaba da baba lami, yana ganinta washe bakinshi yayi Yace" sannunku anyi Sabon zubi kenan? Fauxeey kallonshi tai batace uffan ba tana kokarin gano wani abu daga gareshi duk yanda akwai yana temakawa yaron gidan Wajen yin abunda yakeso in ba hakaba ina ruwanta da ita ko wacece
  "Baba Lami tace Eh daga kauye Muka dakkota ta dan zauna Anan shine kaga tadan waye, saboda kasan Hajiya Batason mara gane abu, Yace hakane dakyau, bakuwa sannu da zuwa

"Fauxeey tace Sannu dai

"Hajiya nanan cewar baba lami?
   "Me gadi da sauri ya amsa tananan tace" OK
bude masu gate din yayi suka shugo Gidan, Tunda fauxeey ta shugo bin gidan da kallo tai dan gidan babban gidane,

Direct Kofar falon Hajiya suka wuce ita da kanta tazo ta bude masu kofa, kallonsu tai daga sama har kasa tace woo baba lami yaushe zaku shugomun daki haka kalle kafarkufa, kuje chan bayan gida ku wanke kafafunku, gaban zeenatu yace rass anya zata sama shiga kuwa? Da taga matar daga gani zatai masifa da isa
    Baba lami ta kalle fauxeey tace muje, baya sukaje suka Wanke kafarsu, Baba lami tace" Zo kiji tai mata magana ahankali tace indai kinason cimma burinki sai kinzama me hakuri, dan Hajiya yar ra'ayice kuma akwaita da zafi da sa aikin tsiya so Kiyi hakuri, Fauxeey tace duk abunta zan jure inshaa Allah,
   Dawoa falon sukai, suka iske an shinfida musu tabarma daga gefe zama sukai sannan suka gaisar da hajiyar

Baba lami tace" Hajiya gatanan na kawo maki ita, sunanta Fauxeeya, Hajiya kare mata kallo tai aranta tace Balaifi Tanada kyau

Kirjin faauxeey se dukan uku uku yake Allah yasa kartai rejecting dinta dan kallonta takeyi sosai

"Hajiya tace tayi amma sedai tayi babba naso yar karama kinsan yan mata ba kowanne zai jure aikin gidan nan ba saboda Akwai wahala,
"Baba lami tace" karki damu bazaki sama matsala da wannan ba

   Suna zaune suna tataunawa akan aikin, da abubuwan da fauxeey zata dingayi a gidan, Usman Bobo ne dan hajiya daya tilo tak ya shugo falon, hannunshi rike da Iphone Da headphone a kunnanshi, dagashi se gajeran wando da wata yar rigar kwallo a jikinshi, ganin akwai baki, Dago kan da zaiyi ya sauke idon shi akan Fauxeeya itama adaidai lokacin takai idonta kanshi, Rikicewa tai kamar zata mik'e tsaye Hajiya tace yadai? Dan ganin Fuskar Guy din ya matukar Firgitata Aranta tace" subhanallah badai gidansu usman bane, shima kafeta da ido yayi kamar yasan fuskar nan, rintse idonshi yai kamar yanason tino wani abu, Sannan ya bude idon ya sake kallonta
   Yana kai idonshi kanta itama a lokacin taje satar  kallonshi, sukai ido 4, Kallo cikin ido sukai ta tabbatar da lalle Wannan Usman Bobo ne ba kama bane, Bata kara tsorataba seda taji mahaifiyarshi tace" Usman ka tashi kenan? Taji zuciyarta ya karaya anya zata iya?

Mum dinshine tace Ga break fast dinka chan kan dining, yaudai na maka favorite dinka, soyayyan Irish da kwai, sai ka hada tea kasha "Wow yace" mum you're a darling tai murmushi, Tace nima na huta daga yau ga house help nan an kawo seta dinga maka kullun kullun

  Aranshi yace" badai wannan tsohowarba, Fauxeey kuwa tinani ta tsunduma anya bata kawo kantaba, dan tasanshi a school Rugged guy ne beji sosai dan Shine ma Ogansu, Ya Allah see me through tace a zuciyarta, dan dole se tayi taka tsantsa dashi

Tashi sukai hajiya ta shiga da ita ko ina ta nunnuna mata komai da yanda zata dinga amfani dashi, Sannan tace bata batason kazanta dan hatta kayan jikinta be mata ba, dole ta bude kayanta wanda sukai mata kadan da Wanda suka tsufa ta bata su, tace sam batason kazanta, Fauxeey tace" to Inshaa Allah,

Falo suka dawo tace kinyi shirin aiki ko zakije gida ki dawo ne? Fauxeey tace" nayi shirin aiki, hajiya tace" very good daga gani zamuje dake
Aran Fauxeey kuma tace" hmmm,

Hajiya tace wannan ne part dina, Akwai part din Yarona zaki iya ko a nemo wata? Shuru tai tana nazari

Bobo kuwa kallonta yake tayi yana kokarin tino inda yasan fuskar nan amma ya kasa

"Hajiya tace Yar nan lafiyarta kuwa? Baba Lami tace Dasauqi Kanta amma tanada aiki, hajiya tace to shikkenan

  Usman bobo ne yace" Lami inasu Zeenatu, Fauxeey satan kallonshi tai tace" mugu kasan abunda kai dole ka tambaya inshaa Allah wa'adinka yakusan zuwa karshe, Ita sam hajiya batasan ma me yafaru ba. tace" aikuwa zeenatu ta guje mu,
   Usman bobo kuwa shi yasan me ya aikata Kurbar Ruwan faro yayi ya lashe baki, Fauxeey tace zaka gane kurankane Dan air kawai

    Sungama komai an yankewa fauxeey kudin aikinta 20k tace Allah ya amfana dan komai ita zata dingayi kuma basu da yawa daga Danta usman se se me gadi se Alhaji in yananan..........

Baba lami ne tai sallama da Hajiya ta tafi gida..Usman Bobo yace Keee jikinta na rawa ta waigo yace zo ki kwashe kayan nan kikai kitchen

Tace Tom....
   Dirty girl ba tom ake cewa ba Toh akecewa inji bobo

Kanta na kasa da godon hijib dinta ta kwashe kaya takai kitchen, bin bayanta yai da kallo, yace yau a yan aikin ma wannan malama ce🤣

Hope kuna jin dadi.....idan kunji dadi kui comment

Muje ZUWA

Urs Ummiey Xeey
    Follow, vote And comment

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now