LAIFINA NE 29

87 11 3
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*PAGE 2️⃣9️⃣*

Bobo Kuwa playing Audio yayi yana sauraran zazzakar muryan Fauxeey, Inama yasan gidansu ya furta ahankali, Murmushi yayi yaci gaba da sauraron Muryanta

   Wayarshine tai ringing dan karamin tsaki yaja wai waye zai katsemai sautin muryan da yakeji me dadi wanda idan yanaji har gyangyadi yakeyi, Har zai danna Rejecting yaga *Beloved Mum* dinshi, Cikin jin dadi yai picking yace hello mum, yanda yai magana kamar me bacci tace" My son baka tashi baccin ba kenan ?

"Yace Aa na tashi first luv, Tace" kaci abinci kuwa? Ya marairaice kamar karamin yaro yace mum naci sosai

Tace" Alright, kajini shuru bamu dawoba jiya ko?

"Yace Eh hope lafiya

"Tace Munanan Abuja tare da dad dinka, wani Aikine ya rikeshi a chan kuma se nan da one month zamu dawo, Shine nace lemme call you zaka biyomu ne ko kawai zaka zauna a gida?

   AI kamar An tsikareshi dan dadi a kwance yake amma wurgi yai da bargon dan dadi, ya lankwasa murya yace" mum zan zauna anan kawai ko dan Saboda gida ba kowa, Mum dinshi tace Alright, take good care of ur self, Kaga alert kuwa?

Yace No banganiba, Tace" Ok ka duba account dad dinka ya turoma da 500K yace idan be ishekaba zai sake turoma

Wani dadi yaji yace Ok thank you Ma, Sallama sukai sannan ya kashe wayar, suna gamawa wani tsalle yayi yace yau akwai chilling kuwa

Abokanshi ya fara kira yace su hadu a joint inda suka saba shakawata, yau akwai ciye ciye da shaye shaye...suma dadi sukaji sosai dan kwana biyu dama basu shakataba, Wata zuciyar tace inama tare da Fauxeey zanje, Tinowa yai fa Befi 2weeks birthday dinshi ba, wata murmushi ya sakar da ni kaina bansan dalilin hakan ba

***
  Bangaren Muhseen kuwa, Tun lokacin da ya shiga Gida Daki direct ya wuce da yan magungunanshi a hannu, Wacce Take Kula da sasanshi yace mata karta yarda wani ma yasan yadawo, duk wanda zai shugo tacemai yana bacci kawai, Ta amsa ta to ta dakko kujera tana gadin Wajen da zai sada ka da dakinshi

Mahaifiyarshi ma sam batasan Ya dawo ba, Motarshi tagani, dan haka tazo Sashenshi. Da yake Mahaifiyarshi ce Mai kula da wajen batace mata komai ba ta barta ta shiga

   Ahankali ta bude kofar, Ga mamakinta tana aza zataganshi a kwance ne taganshi a zaune yayi tagumi, Da sauri ta karasa wajenshi, ta rike hannunshi tana meya farune? meya sameka my son? Da yake Muhseen duk halin da yake ciki yana boye damuwarshi ga mahaifiyarshi beson tasan matsalarshi, baccin hakama wannan matsalar bata kowa bace tashi ce, shi da kanshi zaiyi maganin abun

Dan haka ya kirkiro murmushin da seda mahaifiyarshi taji sanyi a ranta yace" Yunwa nakeji na rasa me zancine kirjina na mun kona sosai gashi na amso magunguna, yana magana yana dakko ledar maganin dan kawai ya gusar da tinaninta, dan a duniyar nan Ita kadaine beso yaga tana damuwa

Shafar fuskarshi tai tace har ka rame, ko Inmaka kunun gyada ne dan Shine daidai dakai yanzu? Kama hannunta yai yace Akwai masu aiki ai ki huta Mun

Tace" barni Kai kadaine namiji a yayana dole inji dakai, bari na tashi na hadoma, Yace Jazakillahu khairan Ummiey,

tai Murmushi ta fita Shiga kitchen tai da kanta ta fara hadamai lafiyayyen kunun gyada

Shi kuma yana kwance Gabanshi se faduwa yakeyi, Yanzu kenan yar da yagani yana sha'awar aura dukda yasan hakan mai wahala ne

Ranshine ya baci yace  Qilama wani ya gama lalatata, Meyasa wasu yan matan basu da tinani ne, Wai shin waye ma mahaifinta, inane gidansu, me tazo yi garin ko kawai iskacinta tazoyi dan Dama ance baason gidansu ba, Jiyai ya tsaneta tabashi haushi

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now