LAIFINA NE 22

75 8 0
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*PAGE 2️⃣2️⃣*

Fauxeey ne kwance a kan gadonta, Maganar Mahaifiyarta ya fado mata na kan yakamata ta ajiye aikinta Saboda tana kaiwa dare, Ga wani bangaren na zuciyarta Tana da bukatar Ganin Haidar, she found her self smiling, tana tino da Soyayyan Da Haidar ke nuna mata, Wani bangare na zuciyarta kuma tanamai nadamar abun da tai mai, yanzu kenan shikkenan ta batamai suna? Wano numfashi taja, A daidai lokacin Wayarta yai ringing, Tana dubuawa taga Number da akai mata text dazu ne, Gaba daya tai switch off din wayar ya kwanta....

WASHE GARI
    Tun Asuba Hajiya ta tafi kauyensu dan dakko wa Haidar matar da zai aura, Zuwa kauyensu tai, da yake akwai yan uwansu sosai, Direct gidan kanwarta ta nufa saboda Su a chan suke, ita kuma sun shugo birni saboda Mahaifiyar Haidar wani dan uwansu ya riketa a birni tai karatu Harta sama Alhaji Abdallah Dabai ya aureta inbaka saniba zakace A chan aka haifeta, dan tayi karatu ta waye sosai, gashi fatar ta ta goge bazaka ce a cibiyarta na kauye ba

****
   Bangaren Aliyou kuma tunda yaji labarin mamanshi ta tafi kauye dan Da safe kwata kwata basu haduba, shiga toilet yayi yai Alwala yayi yazo yana Sallah ya roka Allah, Allah yasa ba Acikin kannan mamanshi bane zaa hadasu dashi dan he will not reject any one a cikinsu, ko bayasonsu dole ya zauna dasu a matsayin matanshi saboda jininshi ne kuma yana sonsu dan tausayi suke bashi, Hawaye suka zobomai ya daga Hannu yace" Ya Allah See me through, Ya Allah idan Alherine hada auran nan kasa ayi, idan ba alheri bane Allah kawo mun mafita.

   Hajiya lubabatu bayan ta isa gidan kanwarta, sun gaisa sai a lokacin take sanar da ita duk abunda ya kawota

"Kanwarta tace" kai amma naji Dadi, amma wani hanzari ba gudu ba, shi Aliyun yana santa ne ko kawai Kece Kikeso ki hada?

"Hajiya lubabatu tace" nice nakeso na hada naga ko bakomai za'a kara hada zumunci, Tace amma kinsan ya'yan yanzu basason auren zumunci sunfison Wanda sukeso, Kina ganin abubuwan nan da yake faruwa a gidan maaurata wasu fa kiduba auren soyayya ne amma idan kikaji wani abun sai ma ki sama cewa komai,

Hajiya Lubabatu tace bawai nazo bane dan kifada mun magana, ko kifaramun Nasiha idan bazaki ba d'ana auran yarki bane, shikkenan

Kanwar tace" waneni, bari na kira maki su Sai kizaba wanda kkeso saiki tafi dasu amma niba ruwana a maganar..

Kiransu tai su biyu yan mata, da shekarunsu bazai wuce 15,17 ba tace gasunan kizaba,

Dayar ce yar babba tace" laaa dama yar uwarmuce munganta a moto dazu da mukaje tasha, mema za'a zaba?

Mamansu tace" birni za'a kaiku ai muku aure, Dukansu sukace su basason auren zumunci, Yar babban ne da yake tana da magana tace" dawa wai zama a hadamu?

Mamansu tai musu bayanin Wannan Haidar Dinne da yake zuwa akai akai, sukace laaa dama wannan ne mamanshi? Bamusantaba

Nan take Hajiya lubabatu tasan tabbas Zumunci nada dadi, Da ace har tana zuwa tana ganinsu bazasu taba qin amince mata ba, Kuma Allah yace A dinga zumunci yanzu gashinan abunda take kwadayi tana ganin Samunshi Bazai mata wahala ba yanzu kiri kiri ya gagareta, Ba yanda batai convincing dinsuba akan Su yarda su aura danta amma Sunqi, tace duk abunda kukeso zan maku, kawai inasone a hada auran,

Aiko yaran nan suka qi

Haushi taji aranta tace Kamar ana neman Kai da Aliyou tazo duk ta zubar mai da Class, Yaro me hankali ga tarbiya ga natsuwa, Hot cake dashi koni na sameshi aureshi zanyi lol, amma Gashinan sunqi yarda Saboda kawai bata zumunci, ta hadasu da Allah sukaqi, gashi batason tace tana so yai aurene har su gane ko wani abun yake aikawata dukda ita kanta bata da tabbas a maganar da Aisha Igala ta fada mata

Tashi tai tace Zata tafi,

Kanwarta tace" Ba kwana zaki ba?

Daga kai tai Alamun Eh fuskar nan ba annuri

Da kanwarta ta lura da hakan tirsasa Yaranta tai akan dole su amince amma suka qi amincewa

Kowa yace yayi alkawari da Saurayinshi

Abun ya batawa Hajiya lubabatu Rai sosai

Tashi tai tace akaita gidan wata kawarta Maimuna da tun suna yara suke tare, dan kawai ma hajiya lubabatu ta shiga birni ne kunsan bakowani kawance zai yiyuwa da dan boko da wanda beyi boko ba
  
Yaran nan suka rakata gidan
  Sannan suka dawo gidansu. 

Sukace mama ji mana ikon Allah, wai me masu kudin nan suka maida mune, ba yar uwarki bace uwa daya uba daya? Mamansu tace kudai kubar maganar nan nan...Allah yasa mudace sukace Ameen
   Amma yau da ace Shi Aliyun ne yazo da kanshi dole zamu amince ko ba Komai yanada zumunci ga kirki dan idan yazo abinci Niki niki da kayan sawa da sauranshi yake kawo mana
    Mamansu tace kudai nace kubar maganar nan ko?

   Shuru sukai a gabanta suka fice waje sukaci gaba da maganarsu....

***
     Bangaren Fauxeey kuwa yauma da zata fita taga Mahafiyarta tadan damu, ita so take a ajiye aikin gaba daya, Fauxeey tace" mama Naji ma ance Ankusan mun transfer na koma chan Gida kawai dama So suke kazo kazauna nadan wani lokaci zan koma chan gaba daya

Mamansu tace" to shikkenan Allah ya te maka, Fauxeey tace Ameen

   Wannan shige da ficen da takeyi duk mahaifiyarta bata sani ba, Dukansu suna aza Aikin company ne akai mata transfer xuwa nan......hmmmm Muje zuwa

Urs Ummiey Xeey

FOLLOW
VOTE
COMMENT

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now