LAIFINA NE 32

101 9 0
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*Dedicated this page To you Meelat...thank for ur cares Dear..ILYSM❣️*

*PAGE 3️⃣2️⃣*

Washe gari
  Zainab ce Zaune Gaban dressing mirrow ta fito wanka, kitso ne akanta har gadon baya, Towel ta dakko ta goge jikinta ko ina, Karar wayarta taji ta tashi ahankali ta dakko, Muhseen luv tagani ta tabe baki kadan, tai picking, Ganinan a kofar gidanku yace mata

tace Ok

Dukda Tasan ita miskila ce tasa Muhseen ya fita, ko ita kadai yakewa haka oho, Doguwar riga moroon ta dakko ta saka, wani tutare me kamshi ta fesa, ta dakko gyalen kayan ta yafa, Kanta ta kamashi da ribon, Tayi kyau sosai, Zainab yar duma duma ce sosai, Ba ramammiyaba kuma batai kibar nan sosaiba

Ba fara sosai bace chocolate colour ce

Tana fitowa falo, mum dinta tagani da kannanta suna kallon TV, kallon mum dinta tai tace ina zuwa! Mum dinta tace Ok, Tasan basai ta tambaya wayeba ko ina zata tasan Muhseen ne ma kawai

Dan tun tuni bata tsayawa da kowa, dan shine abokin fadanta, ko sun hadu ba abun da suke inba musu da chachan baki ba dan a family kowa yasansu, sai iyayensu suka yanke Hukuncin hadasu aure tare dan ganin da suke soyayya suke, Tunda Akace zaa hadasu Kuma suka dena magana sedai ba yanda zasui indai iyayansu sukace abu Bamai musu yace ba haka ba

     Bawai son Junansu suke sosai ba kawai yan uwantaka ne ba wata alakar soyayya tsakaninsu

Abunda yasa ma take dan Kula Muhseen din takanji ana yawan maganarshi, wai duk wanda ya aureshi ya more

Sai yasa ma bata damuba, Tunda tasan wani abun ne suka gani a tare dashi suka fada haka, ita kam A wajenta kifi ya fadi kasa gashesshe ba ruwanta

   Fitowa tai cikin yanga, taga motarshi yai parking  ta dayan bangaren Kama Class din ta tai tana tafiya kamar bazata taka kasa ba, Waigowa yai ya kalleta yaga tamai kyau,

Lukman kuwa yana bayan mota yai zamanshi abunshi,

Bude motar tai ta zauna, tamai sallama ya amsa, Suka gaisa, Lukman ma suka gaisa dan tasan baya zuwa shi kadai tare suke zuwa, Ba wanda yacewa kowa komai

Lukman kuma yana mamakin irin soyayyar nan tasu, Kowa ji da kanshi yakeyi

shuru sukai in banda kamshin turenta daya garmaye motar, Aran Muhseen kuwa tace turaren nan yamun dadi

Game take yayi a yar karamar wayarta batacemai komai ba shima haka sedai ya baya da kyanta Kuma tasa abun da yake matukar So turare

Jan Lukman tai da hiran Ball dan ita mayyan kwallo ne dukda mace ne amma tanason kwallo
Hira sukai sosai sai jefi jefi muhseen ke sa musu baki,

Sun gama hirar ne, Musheen yace nazo gaishekine

Zeee tace uhmm yazo dai gaisheni tunda ba dakai mukai hiran ba, Lukman yace aikuwa

Muhseen Yace Eh hakane amma na ganki kuma kinyi kyau Yana magana cikin gadara da isa,

Zainab tace to Nagode, Yau Wace rana yai magana ne tsaho Lol

Cewa tai ku gaida gaida, Amma  *ADAI GYARA HALI* Ta bude motar ta fita

Muhseen yaji wani baki ciki ya kamashi, duk text da Kira ko idan yazo se tacemai adai gyara hali, halin me zai gyara kuma

Binta da ido yai Yanaso ya furta wani abun, amma Beson tagane ma Yaji haushi dan sunsaba indai suka hado sai sun tusawa junansu Hashi...Lol nace duk kuyi kugana So ne da kishi duk bakusani ba

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now