LAIFINA NE 48

86 12 0
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       *❤️ LAIFINA NE❤️*
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

_One of the most amazing feelings in the world is having someone fall in love with you who you thought you never had a chance with❣️._

*PAGE 4️⃣8️⃣*

Bangaren Gidan su Haidar kuwa, Tunda Cousin din Haidar Halima taji labarin ba garin su haidar zasu zauna ba Yanzu hakama sun tafi, wani Kululun bakin ciki taji duk ya mamaye mata zuciya Ita bataga ta zama ba

     Ba'a gama watsewa ba ta tashi ta tafi ba tare da ta wa kowa sallama ba, kirar Kawarta tai ta rakata gun wani malami akan Ahanasu Zaman lafiya, Malamin yace angama Nan ya gama surkullenshi ya bata wani jini a leda Da kwarya yace ta je ta daure a wani bishiya sai ta saka kwaryan a kasa ta sama tsinke ta huda ledan jinin ya dinga diga a kwaryan to intai haka zata gujeshi ba abun da Zai shiga tsakaninsu na auratayya

  "Tace To shikkenan tai godiya

Suna fitowa daga dajin Ta sama Wani bishiya ta kulle ledan jinin ta sa kwarya a kasa kamar yanda ya umurceta,

Tace Ayi mugani Sannan suka fito daga dajin Sannan suka bar dajin da gudu dan tsorace tsuke dan dare yayi

    Bangaren Su Haidar kuwa tsuna cikin jirgi suna hira sosai, Ganin sun kusan saukane, Lokaci daya Fauxeey ta chanza fuska kamar ba ita ba, daga fa'arar da takeyi zuwa rashin fara'a, wani kunci kawai takeji, tundaga lokacin Haidar be sake ganin hakurantaba

A tinaninshi ko duk tinanin Muhseen ne yaga har suka sauka batace mai komai ba

   Ko yayi kokarin mata magana sai yaga sam bata da fara'a sai yasa ya barta

Wajen karfe 8 na dare suka isa, shine 10 na dare a Nigeria

    Daga Campanyn da zaiyi aiki suka turomusu da moto, haka suka shiga, har suka isa masaukinsu Fauxeeya batace mai uffan ba,

Wani babban Gidane Haduwarshi basai na fada muku ba kunsan dai irin gidajen Outside Lol

Masha Allah, Haidar yace dama tinanina Allah yasa su bamu gida me kyau, Ko baiyi maki ba Baby?

Tace Yayi dagaban bata sake cewa komai ba

   Wasu Maza su biyu suka kawo masu lemo da sim card da duk wani abun da zasu bukata, "Yace Ok thank you amma karku sake shugowa cikin dakin nan iyakarku waje sukace Ok da harshen turanci

Kamo hannunta yai suka Shiga bedroom ta zauna gefen gado

Daukar wayarta yai yasa mata new sim din da aka kawo yai mata copying all her contacts Sannan ya mika mata, shima yaiwa nashi haka

   Kallonta yai yace are you Ok kuwa? Ko bakya murna ne my baby ko wani abun ne? Kallonshi ta tsaya yi sai taji duk ya bata haushi Aranta tana meyasa ma na aureshi

Da yake tun kafin ya aureta yasan halinta, macece yar ra'ayi kuma idan batai niyyar abu ba ba wanda ya isa ya sata balle yasan cikin abu daya kila muhseen ko mamanta take tinawa sai yas abe damu sosai ba

Murmushi yai Ya dakko wayarshi ya kunna suratul Baqara, ya shiga wanka

Har ya fito ya shirya yai kwanciyarshi dan ya gaji

  Ita kuma tananan zaune inda ya barta, gabanta se fadi yakeyi Kamar ta kwalla ihu

   Yayi bacci Kusan 40mins Fauxeey ta waigo ta kalleshi, yanda yake baccinsa hankalinshi kwance Sai taji ya fara bata haushi

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now