LAIFINA NE 11

89 9 0
                                    

(☆^O^☆ ☆^O^☆)
       ❤️ *LAIFINA NE*❤️
(☆^O^☆ ☆^O^☆)

NA
   *FRESH UⓂ️MIEY XEEY*

_Wattpad....Freshummieyxeey_

*Dedicated to My Dear Frnd Ibrahim (Sir Ibress) HBD to you...More life🥰More Wins😘 More money😀 More Health💪🏼 Less Rashin Ji😜 And Mata tagari 👏🏼 Break the rule It's your dayyyyyy💃🏻💃🏻*

*PAGE 1️⃣1️⃣*

Hajiyar su haidar ne zaune a kujera kafanta daya kan daya, ranta yai matukar Baci, har haki takeyi dan bacin rai, kollon yaranta tayi tace" kui maza ku kiramun Haidar mu Za'ai wa iskanci
     Yasmin da Safiyya ne suka fara kallon kallo dan tsoron Kiran Ya Haidar suke, cikin tsawa hajiyarsu ta fara magana kamar haka" badaku nakeyiba? Sannan ta kalle Safiyya tace kiramun shi, Jikinta a sanyaye ta soma dialing Number ya Haidar, yanata ringing be daukaba
     sanar da Mum dinsu tayi, A fusace tace" cigaba da kira harse ya dauka

  Dan haka taci gaba da Kira Ana bakwai dinne ya dauka, Dan shi sam yasama wayarshi a aljihu kuma tana silent, Yanzun ma duba time zaiyi yaga screen din wayarshi na haske yana dubawa yaga sister Sofy
   
Dasauri yai picking yana karawa a kunnanshi tare da fadin Hello, sister ya akaine? "Safiyya cikin sanyin murya tace" Kazo mama na kiranka, Ina wajen aiki yace"

"Meyace? Maza sa handsfree inji hajiyarsu"

Safiyya tai yanda aka umurceta

Safiyya tace mamane tace kadawo Gida! OMG yace ina wajen aiki, Maman ne ta amsa waya tace ba aiki ba komeye ne kazo yanzu yanzun nan, Nan yaji hanjin cikinshi ya kada dan mum dinshi nada Zafi kamar hajiya tubulas Maman Mahmoud Na labarina...

Cikin hanzari ya mik'e yana kallon Ahmad yace" katayani Addua Hajiya ke kirana Allah dai yasa bataji labarin Aikin nan ba
Ahmad yai shuru yace" Ameen Zanzo anjuma inshaa Allah
     Cikin Hanzari Haidar ya fita ya bude motarshi ya tada Ya nufa Gida

In 20mins ya isa cike da fargaba, Yana shiga Gidan yaji kirjinshi na bugun takwas takwas, cikin sanyin Jiki ya shiga falo da sallama

   Amsawa tayi a daidai lokacin tanamai wani Kallon Zaka gane kuranka

Samun Waje yayi ya zauna duk zuciya na Aliyou haidar yana bala'in tsoron mahaifiyarshi, Jikinshi Se tsuma yakeyi dan in akwai abunda ya tsana a rayuwarshi be wuce Fada

    Kallonshi mahaifiyarshi tayi ya kuma tsurewa, Addua kawai yakeyi Allah ya sausauta abun

Fara magana tai kamar haka, Ashe dama Kai mugune? Mayaudari? Tunda ta fara maganar Yagane inda ta dosa, "taci gaba da cewa gidan uban wa kakai musu takardu, Gashinan Sai Watsawa a radio da social media akeyi, Kaga ka janyo mana abun fada KO? Zaiyi magana ta tashi ta wanka Mai mari tace yimun shuru, dan haka yai shuru

   Tino fauxeey yayi duk ita ta jamai Wannan abun, Jiyai ya tsaneta kwata kwata, Aranshi yace da Zai ganta wallahi seya rama saboda da wuya mahaifiyatshi tamai irin haka, Amma wata banza naso ta hadashi da maman shi

Tace badakai nake magana ba!

Karar wayar Hajiya lubabatu ya katse ta daga maganar da takeyi sunan Mahaifin Haidar kenan (Lubatatu)

Tana dubawa taga Abban Haidar, Hararar Haidar din tayi sannan ta dauka wayar hade da Sallama, Yace Kinga abunda nagani kuwa? Wani number ne ya turomun Pic din haidar wai ya sace wasu takardu, Hankalina yai matukar tashi, Shin da gaskene?

Wani ajiyar zuciya tai tace nima haka naji ai ga haidar dinnan a gabana, Bashi wayar yace, Ta mikamai

Fada masu Zafi Dad dinshi yamai, Da seda yaji ya tsana kanshi,

Babanshi yace"  ba yanda banyi dakai ba akan aiki a company dinnan ka Kafe yanzu kaga Result din qin jin maganar iyaye KO?
Wasu Hawaye masu Zafi suka zubomai a ido, Yace Dan Allah dad kayi hakuri

Babanshi yace" da girmana kowa ya sanni ka zubar mun da mutunci? Meka nema ka rasa? Mezakai da takardu

Yace" Dad Wallahi Bani na dauka ba, bansan ya akai ba, Dad din yace wannan maganar banza ce ay, Duk wanda zaka fadawa wa dole kai za'a tuhuma tunda everything a wajenka yake

Yace" Hakane, Dan Allah Dad kayi hakuri, ka yafemun bata suna danai maka, Yace" to Bakomai Allah yai mana jagora, Yace Ameen, Da yake Uban me sauqin kaine nan sukai Sallama

Dukda Abun na damun Mahaifinshi, Amma yayi imani bazai taba aikata hakaba saboda yasan training din da yaiwa danshii,

Yana Zaune Mum dinshi tace" senayi binciken ya akai suka bata, Tunda kudi ba abun da basayi.....nan Haidar ya Kara tsurewa shi tsoranshi daya Kar ta gane Fauxeey tamai Wannan Abun Dan tasha Warning dinshi akan yarinyar, Aranshi yace" yace Ya Allah see me through

Ji yai ya Kara tsanarta aranshi yace" gaskiya fauxeey baki kyautamun ba....

   *****
Bangaren Fauxeey kuwa sunje kasuwa sun siyo kayayyaki da yawa, Dan kudin da suka kashe kamar basu taba komai ba, wayarta ta dakko ta shiga WhatsApp Taga A Wani group ansa breaking news, Dan akwaita akwai son jin labarai

    Hoto tagani daya firgitata, Hoton Haidar hade da rubutu a kasa, Dan tsohon ministan man fetur yayi sama da fadi da wasu document, Nan take Kwalla ya cika mata ido Dasauri ta shige toilet tai kuka ma ishinta akan bata Mai suna datai, ita batai tinanin Haka zai kasance ba, Meyasa tabi wannan hanyar dan hukuntashi, Dukda tasan Koranshi aiki ba wani abu babba bane tunda sunada Arziki me tarin yawa, Amma matsalar Bata mai suna datai gashi ya kaurade ko ina

, Kuka taci sosai
Da har seda zazzabi ya kamata, Jitai gaba daya ya bata tausayi, Harta ciro wayarta zata kirashi wata zuciya tace karma kiba kanki wahala bazai taba kulakiba tunda shi ba Wawa bane kimai wannan rashin mutuncin sannan ya kulaki?

Ajiye wayar tai, Taji Sonshi ya mugun kamata, Aranta tace duk LAIFINA NE, rintse idonta tai tafara Kiran sunanshi da Haidar Ina sonka, Haidar karka barni, I love you

Ummie ne ta shugo dakinta tace" Wai lafiyanki kuwa? Are you normal?

Fauxeey rawan sanyi ta fara tace banda Lafiya ne, Dan Allah kidauka kudi kije shagon wajen nan kice ya nuna maki chemist kije ki siyomun magana

Ayya Sannu tace" Sannan ta bude jakar fauxeey ta ciro 1500 sannan ta sanar wa mamansu ta fita
Fauxeey na kwance ga zafin ciwo ga Son haidar daya addabeta, Jitai tanason ganin fuskarshi amma Sam ba hali....

*** bangaren haidar kuwa Tunda yaji mahaifiyarshi tace zatai bincike shima ya shiga tinani, Dan kwakwalwar shine ta dau chaji, Dakko Wayarshi yayi, kallon pic din Fauxeey yayi yace kin cutar Dani I hate youuuuu

Ita kuma fauxeey na kwance tana tinanin anya Alhaki ze barta kuwa, Wasu zafafan hawaye sukq Kara zubo Mata.......

MUJE ZUWA, shin idan mahaifiyarshi tai finding out wani mataki zata dauka?

Urs Ummiey Xeey

VOTE
FOLLOW
COMMENT

LAIFINA NEWhere stories live. Discover now